Babaji

5704 Posts

Yadda aka ajiye mu tare da kuraye da macizai – Janar Tsiga a hannun ƴan bindiga

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Darakta-Janar na Hukumar Kula da ɗalibai masu yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga, wanda ya shafe sama da watanni biyu a tsare, ya bayyana halin matsin da suka tsinci kawunansu a hannun ƴan bindiga. Ya ce, da shi da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su, an tsare su ne a wani jeji da ke kewaye da duwatsu da dabbobi masu haɗari. Janar Tsiga, mai shekaru 72 ya bayyana cewa, daga cikin dabbobin da aka ajiye su de tare akwai kuraye da macizai da kunamu, inda har a wasu lokutan kurayen ke…
Read More

Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI A daren ranar Juma'a ne babban limamin Masallacin Dutsen Tanshi, Dakta Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi ya rasu. Ɗaya daga cikin jami'an masallacin ya tabbatar hakan ta kafar Facebook. Za a gudanar da jana'izarsa da misalin ƙarfe 10 na safiyar Juma'a. A baya dai Malamin ya yi fama da wani rashin lafiya da ba a bayyana wa al'umma ba, musamman a cikin watan Ramadana, kana daga bisani ya rasu. A makon da ya gabata ne ya dawo daga ƙasar Indiya bayan wata jinya. Haka kuma bai samu damar gudanar da tafsirin azumin watan Ramadan ba kamar yadda…
Read More

Filato: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 10 a Ɓokkos

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba ne wasu ƴan bindiga suka farmaki mutane a ƙauyuka biyar na Ƙaramar Hukumar Ɓokkos dake Jihar Filato, inda suka kashe kimanin mutane 10. Shugaban Majalisar Ci-gaban Al'adun Ɓokkos (BCDC), Farmasun Fuddang da Sakatarenta, Ambasada Duwam Bosco suka bayyana hakan a wata sanarwar haɗaka, ranar Alhamis. Sun ce, a cikin sati guda sun rasa mutane aƙalla 20 daga masu faɗan addini da ƙabilanci a ƙauyuka biyar dake ƙaramar hukumar, inda a ranar 2 ga watan Afrilu kaɗai mutane 10 aka kashe. Majalisar ta kuma ce, maharan sun fara ne da kai farmaki da tsakar…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Yadda Ribaɗu ya miƙa Janar Tsiga da wasu 18 da aka yi garkuwa da su ga iyalansu

Daga BELLO A. BABAJI Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ya damƙa mutane 19 da aka yi garkuwa da su ga Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa don ya miƙa su ga iyalansu. Jami'an sojoji da na wasu hukumomin ne suka ceto su daga sassa daban-daban na ƙasar bayan gudanar atisaye a yayin ayyukansu. Daga cikin waɗanda aka damƙa wa CDS ɗin akwai tsohon Darakta-Janar na Hukumar NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) da Ambasada Gideon Yohanna. A ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka yi garkuwa da Tsiga…
Read More

Shettima ya tafi wakiltar Tinubu a bikin cikar shekaru 65 na samun ƴancin kan Senegal

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya tafi Dakar, Babban Birnin Senegal domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron cikar shekaru 65 da samun ƴancin kai a ƙasar. A ranar 4 ga watan Afrilun kowace shekara ne ake gudanar da bikin samun ƴancin kan, wanda ya kawo ƙarshen mulki jagororin Faransa a shekarar 1960, inda ake gudanar da harkokin da suka shafi fareti da wasu taruka na gargajiya. Hakan ya biyo bayan gayyata ta musamman da Shugaban ƙasar, Bassirou Diomaye Faye ya yi wa Shugaba Tinubu sakamakon alaƙa mai ƙarfi da ke tsakanin ƙasashen biyu. Za a…
Read More

‘Yan sanda sun kama mai safarar yara mata zuwa ƙasar Mauritania

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda da ke aiki a rukuni na 2 na yankin Onikan a Jihar Legas, sun yi nasarar kama wata ƴar safarar ƴan mata daga Nijeriya zuwa ƙasar Mauritania domin yin ayyukan da suka shafi karuwanci. Kakakin rundunar, CSP Umma Ayuba ta bayyana hakan a wata sanarwa, ranar Laraba, inda ta ce a ranar 22 ga watan Maris ne aka kama mai laifin a jihar. Ta ce, jami'an Leƙen Asiri na ZIRS ne suka gudanar da atisayen kamen, inda suka cafko mutane biyu da ake zargi da hannu a laifin, waɗanda tuni suka amsa aikata…
Read More

Tinubu ya yi jimamin rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar Galadiman Kano kuma ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki, Alhaji Abbas Sanusi. Marigayin ya rasu ya na da shekaru 92 a duniya bayan fama da wani dogon rashin lafiya. Ya rasu ya bar ƴaƴa da dama da jikoki, kamar yadda Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya bayyana, ranar Laraba. Daga cikin ƴaƴan nasa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, wanda shi ne shugaban Jam'iyyar APC a Jihar Kano. Shugaba Tinubu ya bayyana Galadiman a matsayin ginshiƙi daga cikin ginshiƙan al'adun gargajiya, wanda ya bada gagarumar gudummawa ga masarautar Kano da…
Read More

Kwastom ta musanta rahoton ƙara wa’adin Kwantirola-Janar

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kwastom (NCS), ta bayyana rahoton ƙara wa'adin Kwantirola-Janar, Bashir Adewale Adeniyi a matsayin ƙarya da kuma abinda ake yaɗawa don ƙoƙarin ruɗar da al'umma. A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, ta hannun jami'inta na hulɗa da jama'a, Abdullahi Maiwada, NCS ta ce, naɗe-naɗe ko ƙara wa'adin Kwantirola-Janar na Kwastom, iko ne na Shugaban ƙasa kaɗai ba ga wani ko wata hukuma ba. Ya kuma ce, za a yi hakan ne a ƙarƙashin dokar NCS ta 2023 da wasu dokoki da ke gudanar da tsare-tsaren naɗa muƙamai, ya na mai cewa babu…
Read More

Kisan Uromi: Gwamnan Kano ya jinjina wa Tinubu da Gwamnan Edo

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yaba wa ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Monday Okpebholo na Edo bisa nuna kaɗuwarsu game da iftila'in da ya yi sanadin kisan mafarauta 16 a garin Udene na Ƙaramar Hukumar Uromi a Jihar Edo. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kwamishinan Labarai na Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, Gwamna Abba ya bayyana alhininsa kan lamarin inda ya jaddada kira da a tabbatar da adalci ga iyalan waɗanda aka rasa da waɗanda suka samu raunuka. Ya ce, lallai akwai buƙatar ɗaukar matakin doka da gabatar da masu…
Read More

Natasha ta gudanar da gangami Kogi duk da dokar hana taro

Daga BELLO A. BABAJI Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Kogi ta Tsakiya, ta sauka a mazaɓarta da ke Jihar Kogi a Arewacin Nijeriya. Hakan na zuwa ne duk yunƙurin gwamantin jihar da rundunar ƴan sanda na hana zuwan sanatar. A baya ne dai rundunar ƴan sandan jihar ta fitar da sanarwar barazanar tsaro, inda ta yi kira ga dakatacciyar sanatar da ta janye batun gangamin da aka shirya da sunanta. Yadda ta isa mazaɓarta
Read More