05
Apr
Daga BELLO A. BABAJI Babban Kamfanin Raba Wutar lantarki na Ƙasa, TCN ya ce ayyukan lalata kayayyakin lantarki daga masu ayyukan haramtattun haƙar ma'adanai da wasu ɓata-gari a Nijeriya na barazana ga ɗorewar lantarki ga al'ummar ƙasar. Ya ce, lallai sai an kawo ƙarshen ayyukan nasu kafin za a daina fuskantar ɗaukewar wuta akai-akai ganin yadda tashoshi da layukansa ke samun tsaiko. Manaja Janar na Shiyyar Enugu, Dakta Thomas Inugonum ya garzaya wata tasha da manema labarai, inda ya nuna masu wajen da aka haƙa wani sashi na layukan, waɗanda tsawa da iska ka iya ɗaiɗaita su. Ya ce, har…
