Babaji

5704 Posts

‘Yan sanda sun kama shahararrun ƴan fashi da ƙwato motoci a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an rundunar ƴan sanda a Abuja, sun yi nasarar kama Rabi'u Jibril da Ibrahim Isa, waɗanda sanannun ƴan fashi ne da kuma ƙwato motoci da wasu ababe. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ta ce a ranar 27 ga watan Maris ne jami'ansu da ke aiki a rukunin Mabushi suka kai ɗauki a rukunin gidaje na Royal Court Estate dake Jahi na II. Lamarin ya biyo bayan kiran gaggawa ne da suka samu da misalin ƙarfe 3:20 na asuba, inda da isar su ne aka samu ba-takashi tsakanin…
Read More

‘Yan sanda sun janye gayyatar da suka yi wa Sarki Sanusi

Rundunar ƴan sanda ta ce ta janye gayyatar da ta yi wa Sarki Muhammadu Sanusi na II, bisa wata hatsaniya da ta faru a ranar Idin Ƙaramar Sallah. A kwanakin da suka gabata ne rundunar ta gayyaci sarkin domin bayar da bahasi akan abinda ya faru a ranar Idin a lokacin da sarkin ke komawa gida akan doki bayan kammala sallar Idi, inda wasu matasa suka far wa tawagarsa har suka halaka ɗaya daga cikin masu ba shi kariya.. To sai dai cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ta janye gayyatar bisa shawarar…
Read More

Shugaba Tinubu ya ɗauko hanyar yalwata ƴan Nijeriya, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce, jagoranci na gari da hangen nesa na Shugaba Bola Tinubu zai taimaka wajen sauya Nijeriya ta fuskar samun ci-gaba a nan gaba. Ya ce, hakan zai samu ne la'akari da ƙoƙarin da ya ke yi na zuba jari a ƙarƙarshin tsarinsa na sabonta ƙasa a ɓangarorin kiwon lafiya, Ilimi da wasu manyan ababen harkar tattali. Ya bayyana hakan ne a yayin da ya karɓi baƙoncin tawagar Gidauniyar Big Win Philanthropy kaseta A, ƙarƙashin jagorancin Shugabarta, Jamie Cooper a Fadar Shugaban ƙasa, a Abuja. Ya kuma marabci buƙatar gidauniyar ta…
Read More

Ministan Ilimi ya nemi a mayar da hidimar NYSC zuwa shekara biyu

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Ilimi, Olatunji Alausa ya yi kira da ƙara wa'adin hidimar ɗaliban NYSC daga shekara ɗaya zuwa biyu. Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a lokacin da Darakta-Janar na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja. Ya ce, za a yi hakan ne yayin da aka faɗaɗa ayyukan koyar da sana'o'i a tsarin hidimar ɗaliban, wanda yin hakan zai bada dama a gare su ta dogaro da kawunansu a yayin da suka kammala. Ya kuma yi kira da a kara adadin ƴan NYSC da ake tura wa makarantu a…
Read More

Harin Filato: Shugaba Tinubu ya jajenta wa iyalan waɗanda aka rasa da alwashin hukunta masu laifi

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin kamo maharan da suka kashe mutane a wasu ƙauyuka dake Jihar Filato da kuma hukunta su kamar yadda dokar ta tanadar. Ya kuma jajenta wa iyalan waɗanda aka kashe a yankunan Ruwi, Hurti da Tadai dake Ƙaramar Hukumar Ɓokkos da kuma wasu daga ƙauyukan Manguna da Dafo, inda nan ma mahara sun kashe mutane da ɗaiɗaita dukiyoyin al'umma. Haka kuma ya jajenta wa Gwamantin jihar ƙarƙarshin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang, ya na mai kira ga al'umma da su bai wa jami'an tsaro haɗin kai a ƙoƙarinsu na kamo waɗanda ke…
Read More

Gayyatar Sarki Sanusi zuwa rudunar ƴan sanda a Abuja raini ne ga masarautun Arewa, inji Kwamared Salihu Ɗantata

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon mataimaki na musamman akan harkokin Arewa ga tsohon gwamnan Jihar Legas (Lateef Jakande), Kwamared Salihu Ɗantata Mahmud ya yi alla-wadai da wasiƙar gayyatar Mai Martaba Sarkin Kano Sanusi Muhammad na biyu da ƴan sanda suka yi masa zuwa Abuja. Salihu ya yi bayyana hakan ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai, inda ya ce Sufeton Janar Egbetokun bai daraja masarautun Arewa ba. Ya ce, shin zai iya gayyatar Alake na Egba a Abeokuta ko Awujale na Ijebu Ode don zuwa yin bincike? "Ina shawarar babban Sufeto Janar akan ya bar kaza a…
Read More

Rikicin hawan sallah: Rundunar ƴan sanda ta gayyaci Sarki Sanusi zuwa Abuja

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinta na bincike game da musabbabin faruwar rikici da ya auku a yayin bukukuwan Sallah a Kano, rundunar ƴan sanda ta gayyaci Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II zuwa Abuja. A ranar 30 ga watan Maris ne aka samu rikicin da ya haɗa da fadawan Sarkin, wanda ya yi sanadin mutuwar ɗan bijilante ɗaya da raunata wasu. Daga bisani, ƴan sanda a Kano sun kama wani matashi mai suna Usman Sagiru ɗan shekara 20 da hannu a rikicin. Hukumomi sun gudanar da bincike akan Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, inda suka masa wasu tambayoyi. A…
Read More

An yi bikin naɗin sarautar Akeem Owoade a matsayin Alaafin na Oyo na 46

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Asabar ne aka naɗa Oba Akeem Owoade a matsayin sabon Alaafin na Masarautar Oyo, wanda kuma shi ne na 46 daga cikin waɗanda suka taɓa riƙe muƙamin. Ya gaji Oba Lamidi Adeyemi ne a kujerar, wanda ya rasu a watan Afrilun 2022 bayan ya rayu da shekaru 83 a duniya. An gudanar da taron naɗa shi ne a makarantar Oliveth Baptist High School a Oyo, inda Gwamna Sayi Makinde ya jagoranci sauran masu alfarma da suka halarci taron. Ga jaddawalin waɗanda suka halarci taron kamar yadda jaridar 'Intelregion' ta ruwaito: "Olubadan of Ibadan, Oba…
Read More

Gwamnan Kebbi ya dakatar da babban sakatare bayan ya ce jihohin Arewa ke da mafi yawan ƴan luwaɗi da ƴan maɗigo

Daga BELLO A. BABAJI Gwmanan Jihar Kebbi, Nasir Idris ya dakatar da babban sakataren ma'aikatansa, Dakta Nasiru Abubakar Kigo, kan cewa Jihohin Kebbi da Sakkwato ne suke da mafi yawan mutanen da ke harkokin luwaɗi da maɗigo. A baya ne sakataren ya gudanar da lakca a wani taron addini, inda ya ce jihar ta na da adadi mai yawa na ƴan luwaɗi (guda 15,979) da ƴan maɗigo (guda 18,567). Ya ce, Sakkwato ta na da ƴan luwaɗi 9,978, yayin da ƴan maɗigo suka kai guda 10,456, lamarin da ya sa ta zama ta uku a Nijeriya a yawan adadin masu…
Read More

NNPCL ya naɗa tawagar manyan jami’an gudanarwa

Daga BELLO A. BABAJI Babban Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL, ya naɗa tawagar manyan ma'aikata da ya ƙunshi jami'ai guda takwas. Lamarin ya biyo bayan naɗa sabon Shugaban Kamfanin (GCEO) ne da kuma tawagar daraktoci (BoD). Jami'in yaɗa labaran kamfanin, Olufemi Soneye ya bayyana hakan a wata sanarwa, ranar Juma'a, inda ya ce tawagar za ta fara aiki ne a nan take. Shugaban Kamfanin, Mista Bashir Bayo Ojulari, shi zai jagoranci tawagar; sai babban jami'in ayyuka, Rowland Ewubare; Adedapo Segun a matsayin babban jami'in kuɗi; da Olalekan Ogunleye a matsayin babban mataimakin shugaba a ɓangaren makamashi. Sauran sun haɗa…
Read More