Babaji

5704 Posts

Wani mutum ya kashe shaidun da za su bada shaida akan sa a kotu

Daga BELLO A. BABAJI A ranar 1 ga Afrilu ne aka samu rahoton wani mutum da ya kashe wasu mutane uku da suka yi yunƙurin bada shaida akan sa a kotu. Lamarin ya auku ne a yankin Yovoyan - Gberefu a yankin Badagry, inda aka samu wani mai suna Charles Atideka ya buɗe wa wasu mutane uku wuta, wato Muji Onilude mai shekaru 75 da Richard Atideka mai shekaru 70 da kuma Charity Atideka mai shekaru 59. Tuni aka garzaya da su babban Asibitin Badagry, inda aka tabbatar da mutuwarsu, kamar yadda ƴan sanda suka bayyana. Baya ga haka ne…
Read More

Kotu ta tasa ƙeyar mutane biyu zuwa gidan yari kan satar kaji

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Litinin ne wata Kotun Shari'a dake Jihar Ogun ta yanke wa wani mai suna Shibu Abdullahi ɗan shakara 21 da Yakubu Usman mai shekaru 25 hukuncin zama a kurkuku na wata guda bisa sace kaji biyu da adadin kuɗinsu ya kai Naira 70,000. Alƙali O.O. Fadairo ya yanke wa kowane ɗayan su zaman watan ne ba tare da zaɓin tara ba, bayan amsa laifukan da ake tuhumar su a kai. Lamarin ya auku ne a ranar 30 ga watan Maris, inda matasan tare da wasu suka aikata satar da misalin ƙarfe 2 na dare…
Read More

Har yanzu Farfesa Mahmood ne shugaban INEC, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata jita-jitar cewa an maye gurbin Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu. Ta bayyana batun a matsayin labarin bogi, inda ta ce labarin ya na yawo a Soshiyal Mediya kan cewa Shugaba Bola Tinubu ya maye gurbin Farfesan. Saidai, Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkar yaɗa labarai ta kafar zamani, O'tega Ogra, ya bayyana cewa, babu ƙamshin gaskiya a cikin hakan ya na mai kira ga al'umma da su ƙaurace wa batun, a wani jageren saƙo da ya fitar. Ya kuma ce, matuƙar hakan ya faru, za a…
Read More

Rahoton dakatar da biza ga ƴan Nijeriya daga hukumomin Sa’udiyya ba gaskiya ba ne – Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Ma'aikatar Harkokin Waje ta ƙaryata rahoton da ke cewa ƙasar Saudiyya ta haramta bada bisa ga Nijeriya da wasu ƙasashe 13. A wata sanarwa da mai taimaka wa ministan ma'aikatar kan harkar yaɗa labarai, Alƙasim Abdulƙadir ya fitar, ya ce hukumomin Saudiyya sun ƙaryata batun da ake cigaba da yaɗawa acikin al'umma. Ya ce, batun cewa Nijeriya ta shiga sahun ƙasashen da aka haramta ba su bisar shiga ƙasar, wanda zai fara aiki daga ranar 14 ga watan Afrilu, ba gaskiya ba ne. Cibiyar Walwalar al'umma ta Saudiyya ta ce babu wata magana mai kama da…
Read More

Shettima ya karɓi baƙoncin Gimbiya Victoria yayin da Nijeriya ta ƙarfafa alaƙar tattali da Sweden

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Litinin ne Nijeriya da Sweden suka sanar da ƙarfafa alaƙa kan harkokin da suka shafi tattali musamman wajen amfani da fasahar zamani don inganta rayukan al'ummominsu. Lamarin ya biyo bayan ziyarar da Gimbiyar ƙasar, wato 'Victoria of Sweden' zuwa Fadar Shugaban ƙasa dake Abuja, a wani ziyarar kwanaki uku don haɓaka harkokin siyasa da tattalin arziƙin ƙasashen biyu. Ya ce, ziyarar ta kuma ƙunshi haɗa hannu a tsakanin su wajen inganta cibiyoyin kasuwanci da ƙarfafa alaƙar al'adu da ke tsakaninsu. Mai Martaba, Gimbiya Victoria ta ce, Nijeriya da Sweden sun yi tarayya a ɓangarori…
Read More

Gwamnatin Tinubu ta zaɓi 7 ga Afrilu a matsayin ranar tunawa da ƴan sanda

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yayin da ya ke wakiltar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen bikin ranar ƴan sanda karo na farko a dandalin Eagle Square. Bikin shine irinsa na farko tun bayan da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ayyana ranar 7 ga Watan Afrilun kowace shekara a matsayin ranar tunawa da irin gudunmawar da jami’an ƴan sanda ke bayarwa wajen wanzar da tsaron ƙasa. Da ya ke jawabi yayin gudanar da taron Sanata Kashim Shatima ya jaddada kudurin Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinibu na horar da…
Read More

Lakurawa sun kashe ƴan bijilante 13 a Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI Kimanin ƴan bijilante 13 ne mayaƙan Lakurawa suka kashe a wani hari da suka kai a ƙauyen Morai dake Ƙaramar Hukumar Augie a Jihar Kebbi. Wani shaida mai suna Alhaji Augie, ya bayyana cewa, lamarin ya auku ne a lokacin da ƴan bijilanten suka yi ƙawanya wa yankin bayan samun wani rahoton sirri game farmakin ƴan ta'addar. Ya ce, a lokacin da mayaƙan suka hallara, sun yi yunƙurin satar dabbobi ne, inda ƴan bijilanten suka mayar da martani da nufin ƙwato dabbobin. Saidai mayaƙan sun kewaye su sakamakon kere su a adadi da makamai. Ya kuma…
Read More

Masu zanga-zanga sun yi watsi da gargaɗin ƴan sanda a Legas, Abuja, Ribas da wasu jihohi

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Litinin ne wasu masu zanga-zangar tafiyar 'Take-it-back' suka yi buris da gargaɗin rundunar ƴan sanda na hana su fitowa, inda suka yi dandazo a wasu titinan jihohin Abuja, Legas, Ribas, Oyo da sauran su. Da fari dai rundunar ta yi kira ga ƴan tawagar tafiyar ne da su soke batun yin zanga-zangar, inda ta ce lokacin da suka zaba bai dace da halin da ake ciki ba. Saidai, duk da haka tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma ɗan kishin al'umma, Omoyele Sowore ya yi watsi da gargaɗin ƴan sandan, inda ya ce an shirya…
Read More

An yaba wa Shettima bisa rawar da ya ke takawa wajen yaƙi da ƙarancin abinci a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shatima ya karɓi baƙoncin tawagar gidauniyar tallafi ta Big Win bisa jagorancin Shugabarta, Jamie Cooper, yayin wata ziyarar ban girma da suka kawo Fadar Shugaban Ƙasa. Hakan ya biyo bayan rawar da mataimakin shugaban ƙasar ya ke takawa ne wajen yaƙi da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki da Kuma buƙatar haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya. Da ya ke jawabi, Shatima ya bayyana cewa, hangen nesa da jagoranci na gari na Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, nan ba da jimawa ba zai sauya Nijeriya zuwa mataki mai inganci da zai taimaki al'umma.…
Read More

Kisan Filato: ACF ta buƙaci a sanya dokar ta-ɓaci a yankunan da iftila’in ya shafa

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Lahadi ne Ƙungiyar Mashawartan Arewa (ACF), ta bayyana takaicinta game da kashe-kashen al'umma da ake yi a wasu yankunan Jihar Filato, inda ta yi kira da a sanya dokar ta-ɓaci a dukkanin sassan da ƴan ta'adda suka addaba a Arewacin Nijeriya. Haka kuma ACF da Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen yaƙar ayyukan ta'addanci a shiyyar. Hakan ya biyo bayan ikirarin Gwamnatin Tarayyar ne na cewa an sami nasara a yaƙi da ta'addanci da samar da tsaro da kaso 90. Gwamantin ta kuma tabbatar da…
Read More