10
Apr
Daga BELLO A. BABAJI Ɗan majalisar dokoki da ke wakiltar mazaɓar Kaiama/Kamanji/Wajibe a Jihar Kwara, Hon. Abdullahi Halidu Ɗanbaba, ya taya Kwamared Salihu Ɗantata Mahmud bisa samun muƙamin mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Ƙaramin Ministan Ayyuka, Muhammad Bello Goronyo. Ya ce, Kwamared Salihu Ɗantata aboki ne na ƙwarai kuma ɗan yankin Kaiama, wanda ya bada gudunmawa sosai wajen ci-gaban al'umma a yankinsa. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa, Hon. Ɗanbaba ya bayyana cewa, naɗin Ɗantata ya biyo bayan ƙwarewarsa ne da ƙoƙarin bada gudunmawa ga ci-gaban ƙasa. Ya kuma bayyana farin cikinsa game da…
