11
Apr
Daga BELLO A. BABAJI 'Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani faston cocin ɗariƙar EKWA, Samson Nda Ali, a yankin Mararraban Aboro na Ƙaramar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna, sun sako shi. Saidai, sun riƙe wani mai suna Yusuf Shehu Ambi, wanda shi ne wanda ya kai musu kuɗin fansar faston, inda suka nemi a ƙara masu wasu adadi na kuɗaɗe kafin su sako shi. A ranar 8 ga watan Afrilu, 2025 ne aka yi garkuwa da Fasto Ali a gidansa, makonni biyu bayan an naɗa shi a matsayin babban jagoran wani coci a yankin. Da fari dai waɗanda…
