13
Apr
Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinsa na fitar da ɗalibai da suka yi karatu a ƙasashen waje daga ƙunci, Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, ya warware matsalolin da suka sanya aka riƙe musu takardun shaidar kammalawa. Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar. Ya ce, tun a watan Disambar 2024 ne gwamnan ya je Cyprus da nufin samar da mafita ga matsalar, wadda gwamantin baya ta gaza saukewa. A yayin ganawa da wakilan Jami'ar 'Near East University', Gwamna Abba ya mayar da hankali ne akan sake wa…
