14
Apr
Dafa BELLO A. BABAJI Jami'yyar APC a Jihar Borno ta jaddada goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takara a zaɓen 2027 tare da kira a gare shi da ya riƙe mataimakinsa, Kashim Shettima a matsayin abokin tafiyarsa a wani karon. Ta sanar da hakan ne a wata takarda jim-kaɗan bayan kammala zama a Gidan Gwamnatin jihar na masu-ruwa-da-tsaki, ranar Lahadi. Mai bai wa Gwamnan Babagana Zulum shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dogo Shettima ya, fitar da sanarwar inda ya ce zaman ya ƙunshi sanatoci da ƴan majalisar wakilai daga jihar, ƴan majalisar dokokin jihar, kwamishinoni, ciyamomi da…
