16
Apr
Daga BELLO A. BABAJI Biyo bayan ƙaddamar da ragin N15 ga kowacce litar man fetur a ƴan kwanakin nan, Matatar Ɗangote ta sake sanar da rage farashi, inda yanzu za a riƙa dakon kowacce lita akan N835 daga wajenta. Hakan ya nuna an samu ragin N30 ga kowace lita daga N865 da ake sayar da ita a tsawon kwanaki shida da suka gabata. Haka kuma ya nuna an samu jimillar ragin N45 daga yadda aka sayar da shi a ranar Laraba da ta gabata, wato ragin kaso 3.5. Wannan shi ne karo na uku da Ɗangote ke rage farashi acikin…
