Babaji

5704 Posts

Muhimmancin Abuja ya wuce a bar ta hannun ƴan adawa, inji Ganduje

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce muhimmanci Birnin Tarayya Abuja ya wuce a bar ta a hannun jam'iyyun ɓangaren adawa. Ganduje ya faɗi haka ne ranar Alhamis a Abuja a yayin karɓar wasu sababbin mambobin APC da suka sauya sheƙa daga jam'iyyun PDP, LP da wasu. Shugaban ƙaramar hukumar birni (AMAC), Chris Maikalangu ya jagoranci tawagar a tsohon filin fareti dake Abuja. Ya ce, hakan ya nuna yadda masu zaɓe suka gamsu da APC a birnin kuma yana fatan za su yi ruwan kuri'u ga jam'iyyar don sake zaɓar Shugaba Bola…
Read More

2027: Ba zai yiwu ku yi magana a madadin tawagar CPC ba – Malami ga ƴan Al-Makura

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon ministan shari'a kuma Antoni-Janar na ƙasa, Dakta Abubakar Malami (SAN), ya yi watsi da ikirarin da ƴan ƙungiyar Sanata Umaru Tanko Al-Makura suka yi na cewa mambobin tsohuwar jam'iyyar CPC dake APC sun fasa ficewa daga jam'iyyar tare da amince wa mara wa Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. Malami ya faɗi hakan ne ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Muhammad Bello Doka, inda ya ce tawagar CPC wanda ɓangare ne na tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ita ke da alhakin bayyana ra'ayinta ba ɓangaren Al-Makura ba. Ya ce, kalaman nasu bai shafin…
Read More

NAHCON ta ƙaddamar da riga-kafi ga mahajjatan 2025

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), ƙarƙarshin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh ta ƙaddamar da taron riga-kafi ga maniyyata aikin hajjin bana a Abuja, ranar Laraba. Hakan na ɗaya daga cikin ayyukan da take yi a yayin shirye-shiryen Hajjin shekarar 2025. Farfesa Saleh ya bayyana ƙoƙarin hukumar wajen ganin ta tabbatar da kula da lafiya da bada kariya ga mahajjatan a yayin da suka yi azamar tafiya ƙasa mai tsarki. Ya ce, a shirye suke su tabbatar da kula da ka'idodin kiwon lafiya na baki ɗaya mahajjatan, ya na mai kira a gare su da su bada haɗin…
Read More

Filato: Gwamna Mutfwang ya bada umarnin bincikar zargin saka wa shanu guba a Bassa

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Jihar Filato, ta bada umarnin gudanar da bincike mai zurfi bisa zargin sanya wa shanu 78 guba a yankin Tafi Gana na Ƙaramar Hukumar Bassa dake jihar. Kwamishinar Labarai, Hon. Joyce Lohya Ramnap ta ce gwamnatin ta samu rahoton sanya guba ga shanu 36 na wani Mallam Sama'ila Nuhu a ranar 16 ga watan Afrilu a yankin dake Gundumar Zanwar. Shugaban Miyetti-Allah na yankin, Idris Ya'u ya shaida wa Blueprint a ranar Laraba cewa an sanya guba ga wasu shanu 78 na wani mambansu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar 36 daga cikin su nan…
Read More

Majalisar Wakilai ta dakatar da ganawa da kantoman Ribas

Daga BELLO A. BABAJI Kwamitin kula da lamuran shugaban Jihar Ribas na Majalisar Wakilai ya dakatar da yin zama da Jagoran jihar, VM Ibok-Ete Ibas (mai ritaya). A ƴan kwanakin nan ne majalisar ta gayyaci Ibas bisa jagorancin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗora masa a jihar bayan sanya dokar ta-ɓaci. Mai magana da yawun majalisar, Sakin Rotimi ya bayyana hakan a wata takarda. Ya ce, sun yi haka ne da nufin zaɓar wata ranar don kammala wasu shirye-shirye da ke da alaƙa da zaman tattaunawar. Majalisar ta ƙafa kwamitin mutane 21 da za su sanya ido kan harkokin shugabancin…
Read More

‘Yan sanda sun yi bayani kan rahoton mutuwar yarinya a jerin gwanon motocin matar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda a Jihar Ondo, ta yi watsi da rahoton bogin da ke cewa wata mota daga cikin jerin gwanon motocin matar Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, ta yi sanadin mutuwar wata ƴar shekara tara a Akure, Babban Birnin jihar, ranar Alhamis. Kakakin rundunar, DSP Olusola Ayanlade ya ce rahoton na ƙarya ne da aka ƙirƙira don ruɗar da al'umma, wanda aka wallafa daga gidan Sahara Reporters a ranar 17 ga watan Afrilu. Remi Tinubu ta je Ondo ne da nufin ƙaddamar da shirin kiwon lafiya na 'Renewed Hope Health Initiative Program' inda aka raba wa…
Read More

Nijeriya ta tsallake yayin da Trump zai rufe ofisoshin jakadancin Amurka a Afrika

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump na yunƙurin rufe ofisoshin jakadancin ƙasar dake Afirka da wasu yankunan duniya, kamar yadda CNN ta ruwaito. Kimanin ofisoshi 30 da wasu cibiyoyinta a sassan duniya za a rufe a ƙoƙarin gwmantin na rage adadin shigarta harkokin difulomasiyya a ƙasashen waje. Ofishin harkokin cikin gida na ƙasar ya ce daga cikin na ƙasashen da za a rufe akwai Jamhuriyar Congo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Lesotho da Kudancin Sudan da cibiyar tuntuɓa ta Afirka ta Kudu. Haka kuma akwai wasu ofisoshin jakadancin a Turai, Asiya da yankin Caribbean da sauran su. Kawo…
Read More

MOPPAN ta yaba wa gwamnan Kano bisa bai wa mambobinta kujerun Hajji

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Ƴan fim ta Ƙasa, MOPPAN, ta jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano bisa bai wa wasu daga cikin mambobinta kujerun aikin Hajjin bana. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kakakinta, Ibrahim Amarawa, ƙungiyar ta ce hakan ya samu me sakamakon ƙoƙarin gwamnan wajen inganta walwala da jin-daɗin masana'antar Kannywood da ƴaƴanta. Ta kuma yaba da yunƙurin gwamnan na tallafa wa harkokinta ganin yadda ta ke taimaka wa ci-gaban al'adun Kano da ma ƙasa baki ɗaya. Kazalika, MOPPAN ta ce tana alfahari da tsarin shugabancin gwamnan na samar da ci-gaba…
Read More

Jagoran Ribas ya musanta gayyatar Fubara da mataimakiyarsa

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Jihar Ribas ta musanta batun gayyatar dakataccen Gwmana, Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Udo zuwa wani zama da aka shirya gudanarwa a Gidan Gwamnatin jihar a ranar 18 ga watan Afrilu, 2025. Ta ce, labarin bai inganta ba kuma ba daga sahihin madogara ya fito ba. A ranar Litinin labarin gayyatar ya karaɗe kafafen sadarwa, inda aka ce Jagoran Gwamantin jihar, VA Ibok-Ete Ibas ya sanar da yin zama da Fubara da mataimakiyar tasa. Saidai, Baban Sakataren Ayyuka na Musamman daga ofishin sakataren Gwamnatin jihar, Dede Sampson Friday, ya yi kira ga al'umma da…
Read More

Arsenal ta yi waje da Madrid a Champions League

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta yi nasarar hayewa zagayen wasan kusa da na ƙarshe a Gasar zakarun Nahiyar Turai, wato Champions League a karo na uku a tarihinta, bayan doke Real Madrid da ci 2 da 1 a filin wasa na Santiago Bernabeu. Hakan ya bata damar yin nasara akan Madrid da jimillar ci 5 da 1 bayan da ta doke ta da ci 3 da 0 a karawar farko, makon da ya gabata. Ɗan wasa Bukayo Saka ne ya zura ƙwallo a minti na 65 wanda hakan ya ƙara wa Arsenal ƙwarin gwiwa, inda…
Read More