Babaji

5704 Posts

Legas: NEMA ta tabbatar da mutuwar mutum biyu da rauni ga 15 yayin ruftawar gini

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa, NEMA, ta tabbatar mutuwar mutane biyu yayin da wasu 15 suka samu raunuka a lokacin da wani gini mai hawa uku ya rufta masu a layin 3 Oremeta dake yankin Ojodu a Jihar Legas. Kodinetan NEMA na shiyyar Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinloye ya ce lamarin ya auku ne a ranar Asabar, inda Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar, LASEMA, ta samu kiraye-kiyaren kai ɗauki. Ya ce, kawo yanzu jami'ansu suna ƙoƙarin ceto rayuka da dukiyoyin da abin ya shafa. Tuni aka garzaya da waɗanda suka samu raunukan asibiti, yayin…
Read More

Bayanai sun fito game da rahoton ba wa hammata iska tsakanin Ministan Harkokin Waje da Mataimakin Gwamnan Bauchi

Daga BELLO A. BABAJI Wasu magoya bayan Mataimakin gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Jatau, sun fitar da wasu bayanai da ke da alaƙa da bai wa hammata iska tsakanin sa da Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar. Wani shaida daga zaman da suka gudanar da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce batun cewa an casa Ministan ba gaskiya bane. Ya ce, ministan mai motsa jiki ne wanda ya fi mataimakin gwamnan karsashi, ya na mai cewa ko faɗa aka yi da shi zai yi wahala a yi galaba akansa. Don haka ya ce, batun an masa duka ba gaskiya bane, lamari…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: JAMB ta sauya lokacin rubuta jarrabawa

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar haɗaka ta bada gurbin karatu ga ɗaliban da ke kammala sakandare (JAMB) ta ce za a fara rubuta jarrabawar UTME na shekarar 2025 a ranar 24 ga Afrilu a madadin ranar 25 ga watan da ta sanar da baya. A wata sanarwa da Kakakinta Fabian Benjamin ya fitar a ranar Asabar, hukumar ta ce ta yi hakan ne don maslahar ɓangarorin da ta ke aiki tare da su. Ya ce, akwai buƙatar ɗaliban su sake fitar da takardar jarrabawar a komfuta don sanin haƙiƙanin yadda sabon jawabin ya ke. Takardar ta ƙunshi wuri, lokaci da…
Read More

‘Yan bijilante 15 sun rasu a yayin harin sabuwar ƙungiyar ta’addanci ta ‘Mahmuda’ a Arewa ta Tsakiya

Daga BELLO A. BABAJI Kimanin ƴan bijilante 15 ne suka rasa rayukansu a yayin harin wasu ƴan ta'adda a wasu yankunan Arewa ta Tsakiyan Nijeriya. Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun bayyana ne daga wata sabuwar ƙungiya da aka yi wa laƙabi da 'Mahmuda', wadda ke kai farmaki a garuruwan da ke kusa da tafkin Kainji, wato Kainji Lake National Park. Yankin, waje ne da ke kan iyakar Jihohin Neja da kwara wanda ya haɗa ƙauyuka da dama na ƙananan hukumomin jihohin. Wasu daga cikin yankunan a Ƙaramar Hukumar Kaiama sun haɗa da Kemaanji, Tenebo, Baabete, Nuku da Nanu; sai…
Read More

Yadda ake yaɗa rahotanni masu ruɗarwa game da Shettima – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI A ƴan kwanakin nan ne aka kitsa makirci da batutuwan ƙarairayi akan Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da ofishinsa. An tsirar da rahotonnin ƙarya ne akansa da nufin haddasa ruɗani gami da rashin jituwa a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja. A wata takarda da babban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai na ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ya fitar, ya yi bayani akan wani batu da ke nuna cewa an hana Shettima shiga Fadar, wanda a zahiri batu ne na ƙarya. Ya ce, wasu rahotonni daga kafafen sadarwa sun yaɗa cewa jami'an…
Read More

‘Yan bindiga a Kano sun kashe mutum biyu da garkuwa da ɗan attajiri a kasuwa

Daga BELLO A. BABAJI An harbe wasu mutane biyu tare da yin garkuwa da wani a kasuwar ƙauyen Faruruwa dake Ƙaramar Hukumar Shanono a Jihar Kano. Wani shaida daga ƙauyen ya ce maharan sun farmaki kasuwar ne a lokacin da mutane ke ƙoƙarin rufe shagunansu bayan kammala cin kasuwa. Ya ce, an kai harin ne da nufin samun wani hamshaƙin ɗan kasuwa, wanda an taɓa sace matarsa a baya, kana daga bisani aka sako ta bayan biyan kuɗin fansa. Ya kuma ce, maharan kai-tsaye suka nufi shagon attajirin tare da yin garkuwa da ɗansa kasancewar ba su same shi ba.…
Read More

Kano: Gobara ta ƙone shaguna a kasuwar Kurmi

Daga BELLO A. BABAJI Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa, a tsakar daren ranar Asabar ne gobara ta kama wani sashi na kasuwar Kurmi da ke yankin Jakara ƴan Jagwal a jihar. Ƴan sanda a babban ofishin Jakara sun sanar da Hukumar Kashe Gobara ta jihar batun da misalin ƙarfe 1:35 na dare, inda cikin gaggawa ta tura jami'ai wajen da abin ya faru domin kai ɗauki. A yayin isa wajen ne suka samu shaguna shida sun ƙone ƙurmus, yayin da wasu biyar kuma suka fara ci da wuta. Daga nan ne suka samu nasarar kashe wutar da kuma…
Read More

Ribas: Tsige Fubara na so a yi, ba sanya dokar ta-ɓaci ba, inji Wike

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana rashin jin-daɗinsa game da sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas da Shugaba Bola Tinubu ya yi. A watan da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya sanar da sanya dokar sakamakon rikicin siyasa da ya yi ƙamari gami da barazanar tsaro da suka haɗa da fashewar layukan mai a jihar. Lamarin da suka sabbaba Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa gami da baki ɗaya mambobin majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida. Daga nan ne ya naɗa VA Ibok-Ete Ibas a matsayin kantoman da zai jagoranci harkokin shugabanci…
Read More

Rundunar sojojin Nijeriya ta naɗa mace ta farko a matsayin kakakinta

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar sojojin ƙasa ta naɗa Laftanal Kanal Anele Onyinyechi Appolonia a matsayin Daraktan harkokin yaɗa labarai na riƙon ƙwarya. Ita ce mace ta farko da ta taɓa riƙe muƙamin a tarihin rundunar. Laftanal Kanal Anele, wadda tana ɗaya daga cikin ƴan diɓa na rukunin 15 na kai-tsaye, wato 'Direct Regular Course 15' kuma mamba a Cibiyar Hulɗa da Jama'a ta Ƙasa (NIPR), ta maye gurbin Manjo-Janar Onyema Nwachukwu ne a muƙamin, wanda aka bai wa muƙami a Cibiyar Sojoji da ke kula da al'adu da manufofinsu na nan gaba. Naɗin nata zai fara aiki ne daga…
Read More

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya miƙa gaisuwar ‘Easter’ ga Kiristoci

Daga BELLO A. BABAJI Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Christopher Musa miƙa gaisuwar taya murna ga al'ummar Kirista bisa zagayowar bikin Easter musamman ga mambobin rundunar sojojin Nijeriya. Daraktan yaɗa labarai na Hedikwatar Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau a wata sanarwa da ya fitar, Janar Musa ya jaddada muhimmancin lokacin bikin wajen sadaukarwa gami da nuna godiya ga nasarori acikin al'umma. Ya ce, jami'an sojoji na amfani da damar wajen sadaukarwa a yayin gudanar da ayyukansu da tsare gaskiya ga ƙasa gami da tabbatar zaman lafiya acikin al'umma. Ya kuma yaba wa ƙoƙarin jami'an bisa jajircewa wajen fuskantar haɗari a…
Read More