Babaji

5704 Posts

Umartar al’umma su kare kawunansu ba daidai ba ne – Martanin Gwamnan Jigawa ga TY Ɗanjuma

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi ya yi tsokaci game da kalaman tsohon babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Theophilus Ɗanjuma na kira ga ƴan ƙasa da su ɗauki matakan kare kawunansu ganin yadda rashin tsaro ya tsananta a ƙasar. Gwamnan, a wata hira da gidan talabijin na 'channels', ya ce kalaman za su iya kai al'umma ga taka doka a yayin da suka ɗauke ta a hannayensu. Ya ce, a matsayin TY Ɗanjuma na babban masanin harkar tsaro da ya kamata a girmama, ba daidai bane ya furta irin kalaman, waɗanda ka iya haddasa bijirewa dokokin da…
Read More

Harin Ƙungiyar Mahmuda: Ƙungiyar ɗaliban Kaiama ta nemi agajin gwamnati

Daga BELLO A. BABAJI Ɓullar ƙungiyar mai suna Mahmuda, wadda wani tsagi ne na Boko Haram, ya haifar da barazana ga zaman lafiyar al'ummar da ke rayu a yankunan iyakokin Ƙananan Hukumomin Baruten da Kaiama na Jihar Kwara da Borgu a Jihar Neja, ganin yadda mayaƙanta ke kai hare-hare ga ƙauyuka. Mayaƙanta sun kashe mutane da dama da garkuwa da wasu gami da ɗaiɗaita dukiyoyin al'umma, lamarin da ya jafe jama'a da dama cikin zaman ɗar-ɗar a yayin da hukumomin tsaro suka nuna gazawa wajen daƙile ayyukan ƴan ta'addar. Don haka ne Ƙungiyar Ɗaliban Kaiama ta Ƙasa, a wata takarda…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Zanga-zanga ta ɓarke a Jos bisa kashe-kashen sassan Filato

Daga BELLO A. BABAJI A yau Litinin ne aka samu cincirindon al'umma a Jos, babban birnin Filato sun fito zanga-zanga don nuna damuwarsu game da kashe-kashe da ke faruwa a wasu sassan jihar, wanda ake zargin ƴan bindigar Fulani da aikatawa. Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) reshen jihar, Reberen Polycarp Lubo da wasu jagororin addinin ne suka jagoranci zanga-zangar. A gano masu gangamin ɗauke da alluna da wasu ababe da ke nuna kaɗuwarsu da aukuwar hare-haren, inda suka cika manyan titina tare da haddasa cinkoso. Suna kira ne ga gwamnatin jihar da ta gaggauta tsoma baki a lamarin tare da…
Read More

Hukumar kashe gobara a Kano ta magantu bisa gobara a Rijiyar Zaki

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta yi tsokaci kan kiraye-kiyaren da ta samu game da ɓarkewar gobara a Kwanar Ƴan Kifi dake Unguwar Rijiyar Zaki a ranar Lahadi. A sanarwar Kakakinta, Saminu Yusuf Abdullahi, hukumar ta ce wani gida da ake harkokin kasuwanci aciki mai faɗin ƙafa 100 da 50 ne ya kama da wuta. Lamarin da ya yi sanadin ƙonewar shaguna uku, motoci uku da wasu ajijuwa bakwai na makarantar 'Young Marshall Science Academy' da wani sashinta. Wani shaida ya bayyana cewa, lamarin ya auku ne a lokacin da wasu mutane daga wata mota…
Read More

Pafaroma ya rasu – Vatican

Cocin Vatican ya sanar da mutuwar shugaban majami'ar katolika ta duniya, Pafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya. A shekarar 2023 ne cocin ya zaɓi Pafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance sa, bayan saukar Pafaroma Benedict XVI daga kan muƙamin. Ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya, inda a baya ya shafe makonni a wani asibiti wanda aka bayyana cewa yana fama da sanyin haƙarƙari mai tsanani. A lokacin da aka naɗa shi, ana kallon Francis a matsayin mai sassaucin ra'ayi. Ya yi ƙoƙarin sassauta ra'ayin cocin kan abubuwan…
Read More

Kashe-kashe: Ku kare kawunanku – TY ga ƴan Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Laftanal Janar Theophilus Ɗanjuma (mai ritaya), ya koka game da kashe-kashen al'umma da ke faruwa a sassa daban-daban na Nijeriya. A ƙarshen mako ne TY ya bayyana hakan a Hedikwatar Ƙaramar Hukumar Takum dake Jihar Taraba, a yayin taron jinjina ga ma'aikatansa, inda ya ce lallai mahara a shirye suke da muggan makamai wajen kai farmaki ga al'umma. Don haka ne ya yi kira ga al'ummar jihar da ma ƙasa baki ɗaya da su tashi tsaye waje kare rayukansu da dukiyoyinsu. Hakan ya biyo bayan samun rahotannin kashe-kashe ne a wasu…
Read More

NDLEA ta kama wasu bisa safarar tabar ibilis cikin litattafan addini zuwa Saudiyya

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), sun yi nasarar kama wasu ƙullin hodar ibilis guda 20 acikin littatafai da aka nufi kai su ƙasar Saudiyya. Kakakin hukumar, Femi Babafemi ya faɗi hakan a wata takarda a ranar Lahadi, inda ya ce sun gano hakan ne daga wani kamfanin jigilar kayayyaki a Legas a ranar 15 ga watan Afrilu, 2025 yayin binciken kayan da za a yi safarar su zuwa ƙasar. Haka kuma a ranar ne suka kama tabar wiwi mai nauyin kilogram 2.8 a hannun irin kamfanin, wanda aka yi jigilar sa daga…
Read More

Easter: Yahaya Bello ya taya Kiristoci murna

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya miƙa gaisuwar taya murna ga Kiristoci a jihar da ma Nijeriya baki ɗaya yayin da suke bikin zagayowar lokacin Easter. Ya yaba masu bisa cika kwanaki 40 na sadaukarwa da addu'o'i, inda ya ce hakan zai taimaka wajen cin nasara ga ayyukan Gwmantin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bila Tinubu. A saƙon da Kakakinsa, Ohiare Micheal ya fitar a ranar Asabar, Bello ya bayyana muhimmancin lokacin ga al'ummar wanda ya ce hakan wani nau'i ne na ƙarfafa koyarwar addini da al'adunsu. Ya kuma kiraye su da su cigaba da bai…
Read More

Borno: ‘Yan sanda sun kama mutum takwas da hannu a kisan jariri a asibiti

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda a Jihar Borno, ta yi nasarar kama wasu mutane takwas bisa tuhumar su da hannu a kisan wani jariri da binne shi a wani asibitin kuɗi dake yankin Kwatam a hanyar Baga dake Maiduguri, babban birnin jihar. Kakakin rundunar, Nahun Daso ya bayyana hakan ga manema labarai a Maiduguri, ranar Asabar. Ya ce, lamarin ya auku ne a ranar Juma'a da misalin ƙarfe 1 na rana, a lokacin da wasu shaidu suka kira ƴan sanda domin sanar da su batun. Daga lokacin ne jami'ansu suka kai same asibitin tare da kamo waɗanda ake…
Read More

NELFUND: Ɗalibai sun koka yayin binciken badaƙala a jami’o’i

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Hana Rashawa da Makamantanta, ICPC, ta fara binciken wasu jami'o'i da bankuna ganin yadda ɗalibai suka gaza samun kuɗaɗe daga Shirin Asusun bada Lamunin Kuɗin Karatu ga Ɗalibai, wato NELFUND da Gwmantin Tarayya ta ƙaddamar. Hakan ya biyo bayan ƙudirin Majalisar Wakilai ne na gudanar da bincike game da zargin wasu jami'o'i da bankuna da riƙe kuɗaɗen da aka ware don tallafa wa ɗaliban. Hukumar Wayar da kan Al'umma, NOA ta bankaɗo wani aikin rashin gaskiya a yayin aiwatar da shirin, inda da dama daga ciki makarantun sun riƙe kuɗaɗen. A shekarar 2024 ne Gwamnatin…
Read More