23
Apr
Daga BELLO A. BABAJI An samu fargaba a tsakanin mazauna wasu yankunan Jihar Kaduna biyo bayan umarnin Gwamna Uba Sani na karɓe gidajen wasu makarantu da filayen da aka raba a Kwalejin Alhuda-huda dake Zariya da Kwalejin Queen Amina da Kwalejin Government Commercial College, Zaria, waɗanda tsohuwar gwamnatin jihar ƙarƙarshin jagorancin Malam Nasiru El-Rufa'i ta sayar da su. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Sakataren Gwamnatin jihar, Dakta Abdulƙadir Mu'azu Meyere, ya ce an ƙwace gidaje da filayen ne sakamakon rashin fifita buƙatun al'umma da kuma duba maslaharsu. Ya kuma ce, tuni gwamnatin ta fara shirye-shiryen mayar…
