12
Oct
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kira ga al'ummar jihar su kasance masu lura da sanya ido tare da ruwaito duk wani abin zargi ga hukumomin da suka dace. Cikin wata takarda da Mai taimaka wa mataimakin gwamnan kan harkar labarai, Ibrahim Garba Shua'ibu ya fitar, ya ce gwamnan ya kiran ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da buɗe wani masallacin juma'a a ƙaramar hukumar Gezawa da ke jihar. Gwamnan, wanda Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilce shi, ya ce tsaro ba abin ya da ake yi wa sako-sako ba ne don haka mutane su ke…
