13
Oct
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Babban kwamandan rundunar kare al’umma ta CPG reshen Jihar Zamfara, Burgediya Janar Lawal B. Muhammad (rtd) ya tsallake riya da baya daga harin gungun ƴan bindiga a lokacin da suka buɗe wa motarsa wuta a kan babbar hanyar Funtua-Gusau. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Asabar a ƙauyen Kucheri da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar. A cewar majiyarmu wanda ya nemi a sakaya sunansa yayin ganawa da manema labarai, Kwamandan yana kan hanyarsa ta dawowa Gusau daga Kaduna inda isarsa ƙauyen ke da wuya sai ya gamu da ƴan…
