ukarofi

11226 Posts
Mun bankaɗo makircin APC na son ƙwace Jihar Ribas – PDP

Mun bankaɗo makircin APC na son ƙwace Jihar Ribas – PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ce, makirce-makircen da Jam’iyyar APC mai mulkin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ke yi na ƙwace Jihar Ribas da ƙarfin tsiya ya kai intaha na ƙoƙarin ƙwace jihar da ƙarfin tsiya daga PDP, amma ta ce hakan ba zai cimma nasara ba. A ranar Laraba ne shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Ribas suka buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci a jihar, bisa zargin cewa jihar na cikin yanayin tashin-tashina. Shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC, Tony Okocha ne ya yi wannan kiran a yayin wani taron manema…
Read More
Za a mayar da Zaria Hotels aji da ɗakunan kwanan ɗaliban Kwalejin Jiragen Sama

Za a mayar da Zaria Hotels aji da ɗakunan kwanan ɗaliban Kwalejin Jiragen Sama

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ya bayyana Gwamnatin Tarayya na shirin mayar da wasu otel ɗin Zaria (Zaria Hotels) da ke Jihar Kaduna zuwa ajujuwa da kuma ɗakunan kwanan ɗalibai na Kwalejin Fasahar Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAT). Keyamo ya sanar da samun otel-otel ɗin Zaria a matsayin wani ɓangare na walwalar NCAT, yayin wani rangaɗin sanin makamar aiki a ranar Laraba. Ya ƙara da cewa, wannan yunƙuri na da nufin bunƙasa cigaban kwalejin.  “NCAT ta kasance cibiya mafi kyawu na sufurin jiragen sama a Nijeriya da Afirka ta Yamma. Filin da muke da shi…
Read More
Rikicin Masarautar Kano: ’Yan sanda sun sake gargaɗin masu tada zaune tsaye

Rikicin Masarautar Kano: ’Yan sanda sun sake gargaɗin masu tada zaune tsaye

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, reshen Jihar Kano ta roƙi jama'a su zauna lafiya a lokacin da ake dakon hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan rikicin sarautar jihar. Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a Kano ranar Alhamis. Abdullahi Kiyawa ya nanata ƙudurin hukumar na kare rayuka da dukiyoyin al'umma. Kakakin 'yan sandan ya kuma gargaɗi duk wani mai yunƙurin tayar da zaune tsaye bayan hukuncin kotu ya gaggauta canja tunani. "Tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, rundunar 'yan sanda za…
Read More
An sace motar ’yan sanda ta ofishinsu da ke Abuja

An sace motar ’yan sanda ta ofishinsu da ke Abuja

MAHDI M. MUHAMMAD An samu rahoton sace wata farar mota ƙirar Toyota Hiluɗ Pickup mai lamba FG79-A23, mallakar rundunar ’yan sanda ta tarayya a Abuja. Lamarin ya faru ne a unguwar Gwarimpa a daren ranar Talata. Motar da aka sace wata kadara ce ta Gwamnatin Nijeriya kuma ma'aikatar harkokin 'yan sanda ce ke amfani da ita.  Wannan ma'aikatar ita ce ke da alhakin ƙaddamarwa, tsarawa, da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka shafi 'yan sanda da tsaro na cikin gida. Har ila yau, tana bada kulawa da tallafi na gudanarwa ga rundunar 'yan sanda ta Nujeriya (NPF), makarantar horar…
Read More
Kotu ta tsare matar da take ɗaɗara garwashi a al’aurar yarinta

Kotu ta tsare matar da take ɗaɗara garwashi a al’aurar yarinta

Daga MAHD MM. MUHAMMAD Wata Kotun Majistare da ke Abeokuta, reshen Isabo, a ranar Laraba, ta bayar da umarnin tsare wata mata ’yar shekara 25 bisa zargin ta da yi wa wata yarinya 'yar shekara 12 mummunar azaba da wuta ta hanyar ɗaɗara mata a al’aurarta. Wadda ake tuhumar wadda ke zaune a lamba 6 Isewo Dotin a unguwar Obada-Oko a Abeokuta, tana fuskantar tuhuma guda ɗaya da laifin haddasa mummunar ɓarna. Wadda ake tuhumar ta amsa laifin da ake tuhumarta da aikatawa tare da roƙon gafarar kotun. Alƙalin kotun, B.Ɓ. William, ta bada umarnin tsare ta a gidan gyaran…
Read More
Kwastom ta kama katon 2625 na kodin

Kwastom ta kama katon 2625 na kodin

Hukumar Kwastom ta kama katan 2625 na kodin da kuma katan 80 na sildenafil. Kwanturola na Area 11 command da ke Onne jihar Ribas ne ya nuna wa manema labarai waɗannan kayan. Aƙalla kayan zasu yi naira 2, 250,654,000. Yace waɗannan kayan suna da illa sosai ga lafiyar mutane. Ya ƙara da cewa wannan aikin haɗin gwiwa ne tsakanin kwastom da hukumar hana safara da shan miyagun ƙwayoyi. Yace waɗannan abubuwan shigo dasu ya saɓawa dokar da ƙasa ta tanada na shigowa da abubuwa daga wani wuri. Ya rufe da yin godiya ga hukumar hana sha da safara miyagun ƙwayoyi…
Read More
An kama ɗan shekara 20 da satar yara a Legas

An kama ɗan shekara 20 da satar yara a Legas

An samu wata hatsaniya a yankin Ojurowo da ke bangaren Eko jihar Legas. Wata mata a ka kama da sata da sayar da ƙananan yara. Jaridar City Round ta rawaito cewa, matar ta saci yaran daga Ijora sannan ta kawo su Eko don ta sayar. A wani faifan video dake yawo a shafin sada zumunta na X, an ga mutane zagaye da wani gini da ake zargin nan wannan matar ke aiwatar da haramtaccen kasuwancin ta. Kamar yadda aka jiyo sautin wani a faifan bidiyon, yana cewa matar ta amsa cewa za ta siyar dasu a kan kuɗi naira 250,000.…
Read More
An gargaɗi al’umma game da amfani da ruwan sama

An gargaɗi al’umma game da amfani da ruwan sama

Daga Ibrahim Hamisu, Kano A yayin da yanayin damina ke ci gaba da kankama, an buƙaci al’ummar jihar Kano da su kula sosai wajen amfani da ruwan sama a wajen sha da sauran ayyukan yau da kullum.Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi gargaɗin a cikin wata sanarwa da ta fito daga sashin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, mai ɗauke da sa hannun shugaban sashin, Ibrahim Abdullahi, aka raba wa manema labarai, yau juma'a Kwamishinan ya ce lokacin saukar ruwan sama lokaci ne da ke tattare da hatsari na samuwar cutar amai da gudawa wanda…
Read More
Kano: APC ta buƙaci jami’an tsaro su kama Kwankwaso

Kano: APC ta buƙaci jami’an tsaro su kama Kwankwaso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta bayyana kalaman da jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi a matsayin abun takaici. Jam’iyyar ta maka Kwankwaso a kotu domin a kama shi bisa zargin da ya yi na cewar gwamnatin tarayya na yin katsa-landan cikin harkokin Kano. Shugaban jam’iyyar na jihar, Abdullahi Abbas, cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce babu wata barazana da Kwankwaso zai iya yi wa gwamnatin tarayya. Manhaja ta ruwaito yadda Kwankwaso ya yi zargin gwamnatin tarayya ƙarkashin jam’iyyar APC na yunƙurin kawo cikas ga zaman lafiya a jihar. Kwankwaso,…
Read More
Masu garkuwa sun kashe matashi bayan karɓar kuɗin fansa miliyan N16

Masu garkuwa sun kashe matashi bayan karɓar kuɗin fansa miliyan N16

’Yan bindiga sun harbe wani matashi mai shekaru 27 har lahira bayan sun karɓ i kuɗin fansar Naira miliyan 16 da babura uku domin sako shi da wasu mutane tara a Jihar Kaduna. A ranar 16 ga watan Afrilu ’yan bindiga suka kutsa gidaje a uguwar Iya da ke garin Jere inda suka sace mutane tara sannan suka nemi kuɗin fansa Naira miliyan 30. Wani mazaunin garin mai suna Shuaibu Hussaini ya tabbatar wa wakilinmu a wayar tarho ranar Laraba cewa masu garkuwar sun kashe Abba ne a ranar Asabar. Shuaibu ya ce masu garkuwar sun harbe Abba ne a…
Read More