ukarofi

11228 Posts
Sufeto Janar ya yi wa jami’ai da dama ƙarin girma

Sufeto Janar ya yi wa jami’ai da dama ƙarin girma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A cikin makon nan ne Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya yi wa sabon mataimakin sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya DIG Yahaya Sahabo Abubakar ƙarin girma tare da mataimakan Sufeto Janar na 'yan sanda tara, da liƙa wa kwamishinonin 'yan sanda 15 sabbin muƙamansu a wani gagarumin biki da aka gudanar a ɗakin taro na Goodluck Ebele Jonathan da ke hedikwatar rundunar a Abuja. Sabbin Mataimaka Sufeto Janar na 'yan sandan da aka yi wa ƙarin girma sun haɗa da AIG Ahmed Ammani, Dankwara Adamu Mohammed, Mohammed Usaini Gumel, Adebola…
Read More
APC ta buƙaci Tinubu ya saka dokar ta-ɓaci a Ribas

APC ta buƙaci Tinubu ya saka dokar ta-ɓaci a Ribas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam'iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta sake yin kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya saka dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin siyasar da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa. Jam'iyyar ta buƙaci da a tura sojoji da makamai a girke su a wurare na musamman a jihar domin kare abin da ta kira ɓarkewar rikici. An ruwaito cewa shugaban riƙo na jam'iyyar a jihar, Chief Tony Okocha, shi ne ya yi kiran a ranar Laraba a wani taron manema labarai a babban birnin jihar, Fatakwal, yana mai cewa akwai lamau ƙarara…
Read More
An kashe jami’an tsaro biyu a rikicin siyasar Ribas

An kashe jami’an tsaro biyu a rikicin siyasar Ribas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An kashe aƙalla mutum biyu a Jihar Ribas lokacin da wasu matasa suka mamaye gine-gine hedikwatar Ƙananan Hukumomi da dama, bayan da wa'adin shugabannin ƙananan hukumomin jihar 23 ya ƙare. Lamarin ya faru ne a jiya Talata, bayan da gwamnan jihar, Siminialayi Fubara, ya umarci shugabannin sassan mulki na ƙananan hukumomin su karɓi ragamar tafiyar da ƙananan hukumomin. Tun a ranar Litinin aka shiga zaman ɗar-ɗar bayan da wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin suka lashi takobin cigaba da zama a ofis, bisa dalilin cewa ’yan majalisar dokokin jihar 27 da ke rikici da gwamnan, waɗanda…
Read More
Ba mu da ƙarancin ma’aikata da kayan aiki a asibitin ƙwararru na Gombe – Daraktan asibitin 

Ba mu da ƙarancin ma’aikata da kayan aiki a asibitin ƙwararru na Gombe – Daraktan asibitin 

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Asibiitn ƙwararru na jihar Gombe shi ne mafi daɗewar asibiti a fadar jihar da aka gina shi tun kafin samun ‘yancin kan Nijeriya a shekarar 1958, kuma asibitin ya samu canje-canje sosai domin an fara shi ne tun daga matakin dispensary, ya koma cibiyar lafiyar matakin farko Primary Health Center, daga baya ya zama General sannan aka mayar da shi asibitin ƙwararru wato Specialist. Jin ana kukan cewa asibitin yana fama da ƙarancin kayan aiki da ƙwararrun ma’aikata, wakilinmu ya ziyarci asibiti inda ya zanta da Daraktan Asibitin Dokta Mu’azu Shu’aibu Ishaƙa, don jin…
Read More
Sarkin Gona ya yi kira ga gwamnati da masu kuɗi wajen taimakon masu ƙaramin ƙarfi

Sarkin Gona ya yi kira ga gwamnati da masu kuɗi wajen taimakon masu ƙaramin ƙarfi

Daga Abubakar A Bolari, a Gombe Mai martaba Sarkin Gona da ke yankin Ƙaramar Hukumar Akko a jihar Gombe, Alhaji Umar Abdulkadir Abdussalam, ya yi kira ga gwamanti da masu hannu da shuni da cewa a dinga taimakon masu ƙaranin ƙarfi ganin cewa rayuwa ta yi tsanani. Sarkin Gona, ya ce taimako ya yi ƙarancin al'umma na cikin matsin rayuwa hakan tasa  matasa masu tasowa ke zama barazana a cikin al'umma. Mai martaba ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar sa inda yace dole sai gwamanti ta tashi tsaye tayi abunda ya dace…
Read More
Shettima ya buƙaci likitocin Nijeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Shettima ya buƙaci likitocin Nijeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya, Kashim Shettima ya yi kira ga likitocin ƙasar, su riƙa zama a ƙasar, don taimaka wa magance matsalar da ƙasar ke fuskanta ta ƙarancin likitoci. Shettima ya yi kiran ne a lokacin da ƙungiyar likitocin ƙasar - ƙarƙashin jagorancin sabon shugabanta, Farfesa Bala Audu - suka kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata. Mataimakin shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda likitocin ƙasar ke yawan ficewa daga ƙasar domin neman ayyuka a ƙasashen waje. A baya-bayan nan dai ana samun yawaitar ficewar likitocin Nijeriya daga ƙasar, zuwa ƙasashen wajen domin…
Read More
Ta ƙona mahaifiyarta ‘yar shekara 86 kan zargin jefa ta a ƙangin talauci

Ta ƙona mahaifiyarta ‘yar shekara 86 kan zargin jefa ta a ƙangin talauci

Wata mata 'yar shekara 45 mai suna Abiodun ta banka wa mahaifiyarta ’yar shekara 86 wuta a garin Ondo da ke Ƙaramar Hukumar Ondo ta Yamma a Jihar Ondo. Abiodun, wadda aka fi sani da ‘Iya Sunday’ ta ce ta ƙona mahaifiyarta ne saboda zargin ta da zamowa silar wahalhalunta a rayuwa. Wani ganau mai suna Sola Oladele ya bayyana cewa wadda ake zargin ta zo gidan mahaifiyarta ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 5 na safe ta kira ta kafin ta zuba mata man fetur sannan ya banka mata wuta. Ganau ɗin ya ce, matar da faɗa masa…
Read More
Kotu ta tasa ƙeyar jami’an EFCC na bogi zuwa gidan yari

Kotu ta tasa ƙeyar jami’an EFCC na bogi zuwa gidan yari

Kotu ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 30 ga wasu mutane biyu da aka kama suna yin sojan gona a matsayin jami’an hukumar  (EFCC. Dubun jami’an EFCC na bogi, Ugwu Chijioke da Ibrahim Adekunle, ta cika ne a lokacin da suka je domin zartar da wani jabun umarnin kotu a unguwar Lekki da ke Legas a watan Mayun 2021. Abubuwan da aka kama a hnnun waɗannan jami’an EFCC na bogi sun hada da jabun katin shaidar aiki da rigunan hukumar da kuma takardar umarnin gobi daga Kotun Majistare da ke zamanta a Mushin. Hukumar ta gurfanar da su a gaban Kotun…
Read More
Ɗan sanda ya harbe alƙali ana tsaka da shari’a a kotu

Ɗan sanda ya harbe alƙali ana tsaka da shari’a a kotu

Wani babban jami'in 'yan sandan Kenya ya harbi mai jagorantar shari'a a wata kotun majistare da ke Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya. Ɗan sandan mai muƙamin babban Isfekta ya buɗe wa mai shari'a Monica Kiɓuti wuta jim kaɗan bayan ta yanke wa matarsa hukunci kan wani laifi da ake zarginta da aikatawa. Rahotonni sun ce jami'in ɗan sandan ya fusata ne bayan da kotun ta ƙi amincewa da buƙatar belin matar tasa. Daga nan ne, Sufeto Samson Kipchirchir Kipruto, wanda ke jagorantar ofishin 'yan sanda na Londiani da ke yammacin ƙasar, ya zaro bindigarsa tare da harbe alƙalin inda ya…
Read More
Amurka ta ce a fusace ta ke da Chana kan goyon bayan Rasha a yaƙin Ukraine

Amurka ta ce a fusace ta ke da Chana kan goyon bayan Rasha a yaƙin Ukraine

Amurka ta cacaki Ƙasar Chana da game da zargin bai wa Rasha tallafi da kuma goyon bayanta a yaƙin da ta ke yi da Ukraine. Da ya ke bayyana takaicinsa game da batun, sakataren harkokin wajen ƙasar Antony Blinken, ya ce lokaci ya yi da ya kamata duniya ta juyawa Chana baya, har sai ta tsame hannunta daga tallafa wa Rahsa a wannan yaƙi. A mabambantan lokuta dai, Chana ta sha musanta zargin bai wa Rasha tallafi ta kowaccce fuska game da yaƙin, to sai dai Blinken wanda ke magana gaban wani taron manema labarai tsakanin sa da shugaban ƙungiyar…
Read More