21
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Dakta Folasade Yemi-Esan, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, HOCSF, ta ce aikin tantance ma'aikata da ofishinta ya yi kwanan nan, ya bankaɗo ma’aikatan da ke zaune a ƙasashen waje kuma har yanzu suna samun albashi daga Nijeriya. Yemi-Esan ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ta yi da shugabannin kafafen yaɗa labarai a ranar Laraba a Abuja, kasancewar wani ɓ angare na ayyukan bikin Makon Ma’aikata na 2024. Taken bikin na 2024 shi ne 'Koyar da Ƙwararriyar Afirka don Ƙarni na 21: Gina Tsarukan Ilimin Juriya don Ƙarfafa Samun Haɗuwa, Tsawon Rayuwa, Inganci da…
