ukarofi

11225 Posts
Shari’ar ta’addanci: Nnamdi Kanu ya nemi sulhu da gwamnati

Shari’ar ta’addanci: Nnamdi Kanu ya nemi sulhu da gwamnati

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, inda ya bayyana cewa a shirye yake ya tattauna da wakilan gwamnati.  Kanu ya bayyana hakan ne a cigaba da shari’ar da mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ke jagoranta. Shugaban ƙungiyar ta IPOB ɗin dai yana hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) tun a shekarar 2021 inda aka sake kama shi tare da dawo da shi domin ci gaba da shari’ar sa bisa zarginsa da laifin ta'addanci da cin amanar ƙasa. Sai dai a zaman da aka cigaba da sauraron ƙarar…
Read More
Kamfanin Multichoice ya miƙa wuya, ya rage farashin DSTV da GOtV

Kamfanin Multichoice ya miƙa wuya, ya rage farashin DSTV da GOtV

Fitaccen kamfanin tashoshin talabijin na MultiChoice ya miƙa wuya busa caccakar sa da ake yi, inda ya sake rage farashin biyan kuɗin DSTV da masu amfani da GOtV a Nijeriya, biyo bayan umarnin kotu da ta umurce shi da ya dakatar da yunƙurin ƙarin farashin. Duk da cewa kamfanin na ƙasar Afirka ta Kudu ya dage kan ƙalubalantar hukuncin Kotun Kare Masu Sayayya da Gasa Tsakanin Kamfanoni ta Nijeriya a Abuja, MultiChoice ya rage farashi a manhajarsa a ranar Lahadi, 16 ga Yuni, 2024. Bayan rafe farashin, yanzu masu amfani da DSTV za su biya Naira 29,500 maimakon Naira 37,000…
Read More
‘Ƴan sanda sun kama mutum 16 da ake zargi da faɗan daba a Kano

‘Ƴan sanda sun kama mutum 16 da ake zargi da faɗan daba a Kano

Tsakanin 15 da 20 na watan Yuni, an samu ƙaruwar yawaitar faɗan daba a anguwannin sharaɗa, Ja'in da Dala da ke cikin birnin jihar Kano. A dalilin haka ne, rundunar ƴan sandan jihar Kano suka ɗau alwashin ganin sun yi ƙokari wajen ganin hakan bai cigaba ba. A anguwar Sharaɗa-Ja'in, wani hari da aka kaiwa shugaban yan vigilante Muktar Garba, yayi sanadiyar rasa ransa. Manyan waɗanda ake zargi, Umar Shaibu da Umar Kabiru suna hannun yan sanda. Domin sune ake da zargin ke yawan tada hankula a wannan anguwan. Haka ma a anguwar Dala, faɗan daban yayi sanadiyar mutuwar wani…
Read More
Dalilan da ya sa yan sanda ba za su fitar da Sarki Aminu Ado ba- Kwamishinan ‘yan sanda

Dalilan da ya sa yan sanda ba za su fitar da Sarki Aminu Ado ba- Kwamishinan ‘yan sanda

Kwamisshinan Yan sandan Jihar kano, AIG Usaini Gumel ya bayar da dalilan da ya sa ba su bi umarnin Gwamnan Kano ba na tsige Aminu Ado Bayero daga gidan sarki da ke Nasarawa. In bamu manta ba, Gwamnan kanon ta hannun Kwamishinan sharia na jihar kano, Bar Haruna Isa Dederi ya fitar da sanarwar wadda ta umarci Kwamishinan ya tsige tsohon sarkin da gidan. Sai dai Kwamishinan 'yan sandan a wata hira da aka yi dashi ta wayar salula ya ce bin umarnin gwamnatin zai kasance gaggawa ne, saboda gwamnatin da ta bayar da wannan umarnin ta kuma shigar da…
Read More
Soja ya kashe wani mutum ta hanyar caka masa wuƙa

Soja ya kashe wani mutum ta hanyar caka masa wuƙa

An samu wata yar hatsaniya a kasuwar kugbo bangaren da ake siyar da kayan gyaran mota jiya. Ana zargin wani soja ya soka wa wani mutum wuƙa, wanda sanadiyar haka mutumin ya mutu. Kamar yadda jaridar daily trust ta gano, wanda ake zargin yan kawo gyaran motar shi ne wajen wani bakanike da ake kira yellow. Wanda daga bisani, muhawara ta shiga tsakanin su, sai sojan ya fiddo wuƙa ya caka masa. Hakan ya jawo mutane sun lakaɗa ma sojan duka wanda ya samu ya tsere da kyar. Kuma suka ƙona motar sojan. Komai dai ya dawo dai dai bayan…
Read More
DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Kano ta umarci ƴan sanda su fitar da Aminu Ado daga gidan sarki na Nassarawa don ta yi kwaskwarima

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Kano ta umarci ƴan sanda su fitar da Aminu Ado daga gidan sarki na Nassarawa don ta yi kwaskwarima

Daga Ibrahim Hamisu Gwamnatin jihar Kano ta umurci kwamishinan ‘yan sanda da ya fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero daga gidan sarki na Nasarawa GRA da ke yake zaune. A yayin wani taron manema labarai da kwamishinan shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isa Dederi ya yi, ya bayyana cewa gwamnati ta kammala shirye-shiryen sake gina gidan Sarkin.Gwamnatin ta kuma bada umarnin sake gina katangar gidan saboda ta lalace. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da a yammacin yau babbar Kotun tarayya dake Kano Karkashin jagorancin mai shari'a Abdullahi Liman ta yanke hukuncin rushe duk wani…
Read More
Kotu ta tabbatar da Aminu Ado a matsayin sarkin Kano

Kotu ta tabbatar da Aminu Ado a matsayin sarkin Kano

Wata babbar kotu a Kano ta jingine dokar da ta kawo naɗin Sarki Sanusi na II. Mai sharia Abdullahi Liman shine ya tabbatar da haka a yayin zaman da akai a kotun yau. Mai shari'ar ya kuma ba masu ƙara cewa kowa ya zauna matsayin sa har sai kotu ta gama zaman sauraren ƙarar baki ɗaya. Bayan haka ne ya miƙa cigaba da sauraren shari'ar ga babbar kotu ta uku.
Read More
Gwamnatin Nasarawa za ta cigaba da hukunta masu harƙar ma’danai ba bisa ƙa’ida ba a jihar

Gwamnatin Nasarawa za ta cigaba da hukunta masu harƙar ma’danai ba bisa ƙa’ida ba a jihar

DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya Gwamnatin jihar Nasarawa tace zata cigaba da tsare tareda hukunta masu haƙar ma'danai ba bisa ka'ida ba a jihar.Kwamishinan ma'aikatan muhalli da albarkatun ƙasa na jihar honorabul Kwanta Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattauna da manema labarai a ofishin sa dake Lafia. Yace ba shakka hakan haƙƙi ne daya rataya a wuyar gwamnatin jihar ta tabbatar tana kare duka ma'adanai da sauran kaddarorin jihar musamman Idan akayi la'kari da yadda wasu Ke shigo jihar daga wasu jihohin daban don haƙar ma'adanan ba bisa ƙa’ida ba Kuma basa karban lasisin aikin.…
Read More
Kuɗaɗen ƙananan hukumomi: RMAFC ta goyi bayan Gwamnatin Tarayya

Kuɗaɗen ƙananan hukumomi: RMAFC ta goyi bayan Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga da Raba Kuɗaɗen Shiga (RMAFC) ta bayar da shawarar samar da cikakken ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomin ƙasar nan kamar yadda ta goyi bayan gwamnatin tarayya a ƙoƙarin da take yi na ƙwato ƙananan hukumomin daga hannun gwamnatocin jihohi ta hanyar dokar bada tasiri ga tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki. Shugaban RMAFC, Mohammed Bello Shehu, a cikin wata sanarwa, ya lura cewa LGCs a matsayin matakin gwamnati na uku na cikin gida a matakin farko ya kamata su kasance daga hannun gwamnatocin jihohi da na Tarayya domin an kafa su…
Read More
Kwastom da sojoji sun fatattaki ‘yan fasa ƙwauri bayan kai wa jami’ansu hari a Legas

Kwastom da sojoji sun fatattaki ‘yan fasa ƙwauri bayan kai wa jami’ansu hari a Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kwastom ta Nijeriya, reshen ayyuka na tarayya, Zone A (FOU A), ta tabbatar da harin da ‘yan fasa-ƙwauri suka kai wa jami’anta da sojojin Nijeriya a yayin da suke gudanar da ayyukan yaƙi da fasa ƙwauri. A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na sashin, SC Theophilus Duniya ya sanya wa hannu, a ranar Talata, 3 ga watan Yuni 2024, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni 2024 da misalin ƙarfe 3 na safe. Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Tawagar ‘yan sintiri ta haɗin gwiwa da…
Read More