ukarofi

11225 Posts
First Bank ya ƙwato rancen biliyan N456 daga bankin Heritage kafin a ƙwace lasisinsa

First Bank ya ƙwato rancen biliyan N456 daga bankin Heritage kafin a ƙwace lasisinsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Bankin First Bank ya samu nasarar karɓo cikakken rancen Naira Biliyan 456 da ya baiwa bankin Heritage, a wani ɓangare na shirin bayar da lamuni a zamanin mulkin tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele. Majiyoyi a cikin First Bank, da suke magana da Nairametrics, sun bayyana cewa CBN ya baiwa bankin bashin da ake kira 'tier-one' kafin ya sanar da soke lasisin bankin Heritage. Dakatar da bankin, wanda CBN ya sanar a ranar Litinin, ya bada misali da yadda Bankin Heritage ke ci gaba da fama da matsalar kuɗi da kuma rashin samun damar…
Read More
Gwamnan Zamfara ya yaba wa Gwamnan Sokoto kan samar da ayyukan yi

Gwamnan Zamfara ya yaba wa Gwamnan Sokoto kan samar da ayyukan yi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD  Gwamna Dauda Lawal ya yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu bisa ƙara samar da guraben ayyukan yi ga al’ummar Jihar Sakkwato. A ranar Larabar da ta gabata ne Gwamna Lawal ya jagoranci ƙaddamar da rabon babura da adaidai sahu da gwamnatin Jihar Sakkwato ta samar. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sayo adaidai sahu 500, babura 1,000, da adaidai sahu mai amfani da lantarki 150 domin raba wa matasa a faɗin jihar a matsayin wani mataki na ƙarfafa tattalin arziki. Sanarwar…
Read More
Baitulmalin Nijeriya ya ƙaru da Dala Biliyan 1.43, inji IMF

Baitulmalin Nijeriya ya ƙaru da Dala Biliyan 1.43, inji IMF

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Asusun Nijeriya a halin yanzu ya samu rarar dala biliyan 1.432 a shekarar 2024, a cewar wani rahoto na asusun lamuni na duniya, IMF. Rahoton ‘World Economic Outlook Database’ wanda gidan talabijin na Channels ya gani a ranar Laraba, ya nuna cewa ƙaruwar asusun gwamnatin tarayya na wannan lokacin, ya kasance ci gaba daga rarar dalar Amurka biliyan 1.21 da aka samu a shekarar 2023. An danganta wannan ci gaban ne saboda ƙaruwar kuɗaɗen ajiyar ƙasa da kuma zuba jari da ƙasar ke samu. A shekarar 2024, jimillar kuɗaɗen ajiyar Nijeriya ya ƙaru zuwa kashi 26.32…
Read More
Yadda wasu ke sayen fetur a Nijeriya suna sayarwa kan N1700 a Jamhuriyar Benin

Yadda wasu ke sayen fetur a Nijeriya suna sayarwa kan N1700 a Jamhuriyar Benin

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An nuna damuwa game da yadda ake fasa ƙwaurin man fetur a tsakanin ƙasashen yammacin Afirka da ke makwabtaka da Nijeriya kamar su Jamhuriyar Benin, Kamaru, da sauransu. Farashin man fetur a Nijeriya ya kai kusan Naira 701 a kowace lita yayin da ake sayar da shi kan 1,700 a wasu ƙasashen yammacin Afirka. Wannan bambamcin farashin ya haifar da ƙaruwar masu fasa ƙwaurin fetur ɗin daga Nijeriya cikin makonni biyu da suka gabata. Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Nijeriya Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Yola.  Ya bayyana cewa,…
Read More
Ranar Dimukraɗiyya: Me ‘yan Nijeriya suke wa murna?

Ranar Dimukraɗiyya: Me ‘yan Nijeriya suke wa murna?

Ranar 12 ga watan Yuni muhimmiyar rana ce a tarihin Nijeriya, kasancewarta ranar da aka gudanar da Babban Zaɓen Shugaban ƙasa na shekarar 1993, wanda daga baya gwamnatin mulkin soja ta lokacin ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta soke, bisa zargin an tafka maguɗi. Wannan mataki da gwamnatin ta ɗauka ya haifar da rabuwar kai mai tsanani a tsakanin 'yan Nijeriya, musamman a ɓangaren kudanci da arewacin.  Tun daga wancan lokacin alaƙar Kudu da Arewa ta cigaba da fuskantar ƙalubale, musamman a siyasance. Sakamakon yadda ƙabilar Yarabawa da ke zaune a Shiyyar Gabashin Nijeriya ke kallon 'yan Arewa…
Read More
Muna son matasa su karkato da tunaninsu ga sana’o’in gargajiya, inji Sarkin Askan Jos

Muna son matasa su karkato da tunaninsu ga sana’o’in gargajiya, inji Sarkin Askan Jos

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  A yayin da sana'o'in gargajiya daban-daban ke samun koma baya, saboda sauye sauyen zamani da rashin samun tallafin hukumomi. An fara ganin farfaɗowar wasu tsofaffin sana'o'in Hausawa na iyaye da kakanni da ke ƙoƙarin jawo hankalin matasa ga raya al'adunsu na gado, don samun abin dogaro. Harkar wanzanci na daga cikin waɗannan sana'o'in da daruruwan matasa ke cin abinci a cikinta, sakamakon sabbin jinin shugabanni da aka samu da ke ƙoƙarin inganta sana'ar da kuma ƙara kusantar da ƙungiyar raya harkar wanzanci ga gwamnati, don kawo wa sana'ar cigaba. Wakilin Blueprint Manhaja a Jos, ABBA ABUBAKAR…
Read More
Ya kamata maniyyata su zama jakadun Nijeriya nagari a Saudiyya – Shiekh Suleman

Ya kamata maniyyata su zama jakadun Nijeriya nagari a Saudiyya – Shiekh Suleman

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugaban Ƙungiyar Izala ta Ƙasa, reshan Jihar Legas Shiekh Suleman Ibirahim kuma babban limamin masallacin Juma'a na rukunin gidajen unguwar Wantauzan a Legas, ya shawarci maniyyatan Nijeriya masu zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke faralin su a wannan shekara da su ji tsoron Allah. Ya ce, su guji sayen haramtattun kayan da Gwamnatin ƙasar Saudiyya ta haramta a shigar mata da su a ƙasar ta bakiɗaya. Babban limamin na masallacin ya buƙaci hakan ne a lokacin da yake gabatar da huɗubar sa ta sallar Juma'a ga al ummar Musulmin Nijeriya a ranar Juma'ar makon da…
Read More
Hajji: Aƙalla mahajjata 900 ne suka rasu saboda tsananin zafi

Hajji: Aƙalla mahajjata 900 ne suka rasu saboda tsananin zafi

A cewar jaridar AFP, aƙalla mahajjata 600 daga ƙasar Misra suka rasu. Yayin da suke kai adadin a jumlace zuwa 922 a wata ƙididdiga. An sami yawaitar zuwa asibitoci a lokacin aikin hajji, yayin da cigiyar wanda suka ɓace shima ya yawaita. Duk da wannan rahoton na cewa mahajjata 900 suka rasu lokacin aikin hajji, shugaban hukumar alhazai ta ƙasa yace yan najeriya uku ne ƙadai suka rasu. Ya ƙara da cewa, aƙalla mutum 17 ne suka suma saboda tsananin zafi, amma kawo yanzu duk an basu kulawa sun dawo hayyacinsu. An ƙara samun mata biyu masu ciki wanda sukai…
Read More
Atiku ya kai ziyarar sallah ga tsofaffin shugabannin Najeriya a Minna

Atiku ya kai ziyarar sallah ga tsofaffin shugabannin Najeriya a Minna

Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya kai ziyara ga tsofaffin shugabannin ƙasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar da Janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidajen su da ke minna babban birnin jihar Neja. Atiku, shine ya wallafa wannan labarin da kuma hotunan ganawarsu ta shafin sa na sada zumunta. Atiku Abubakar tsohon mataimakin Shugaban ƙasar Najeriya ne daga shekarar 1999 zuwa 2007.
Read More
Abba Kyari zai koma gidan kaso

Abba Kyari zai koma gidan kaso

A yau wata babbar kotu da ke Abuja ta hana Mataimakin kwamisshinan yan sanda wanda aka dakatar Abba Kyari sabon beli. Saboda haka, zai koma gidan kaso na Kuje. Mai sharia Emeka Nwite lokacin da yake yanke hukuncin yace, bada belin wani abu ne da kotu in ta ga dama zata bayar ko akasin haka. Ya ƙara da cewa wanda ake ƙarar bai bada wani ƙwakwaran hujja da zai sanya kotu ta sake bada belin nashi. A 22 ga watan Mayu da ya wuce, kotun ta bada belin Abba Kyari domin bashi damar halartar janaizar mahaifiyar sa. Bayan wannan lokacin…
Read More