ukarofi

11225 Posts
Gobara ta kama a Ado Bayero Mall da ke Kano

Gobara ta kama a Ado Bayero Mall da ke Kano

Wani sashen babban kantin nan na Ado Bayero ya kama da wuta. Duk da cewar har yanzu ba a samu cikakken bayanin dalilin da yasa wutar ta kama ba, amma ma'aikatan kashe gobara sun halarci wurin. An hana mutane zirga zirga a sashen da wutar ta kama har sai ma'aikata sun gama aikinsu.
Read More
Wani mai gadi ya rasa ranshi yayin raba faɗa

Wani mai gadi ya rasa ranshi yayin raba faɗa

Rundunar yan sandan jihar Legas ta tabbatar da cewa wani mai gadi mai suna Yusuf Akadogo, ya rasa ransa yayin da yake raba faɗa tsakanin wani ɗan achaɓa da wani mutum. Mai magana da yawun yan sandan na Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya sanar da hakan a yau talata. Ya ƙara da cewa ɗan achaɓar dai ya gudu, har yanzu ana neman shi.Ya kuma ƙara da cewa an yi hanzarin kai Mai gadin asibitin jami’ar jihar Legas, saidai a can ne rai ya yi halinsa.
Read More
Mahaifiyar Bukola Saraki ta  rasu

Mahaifiyar Bukola Saraki ta rasu

Allah yayi wa mahaifiyar Abubakar Bukola Saraki, MADAM Florence Morenike Saraki rasuwa. Jaridar daily trust ta rawaito, mahaifiyar mai shekaru 88 ta yi doguwar suma kafin a kai ta asibiti a jihar Legas. Wata majiya na cewa, abun ya faru ne da yammacin yau lokacin da mama tai doguwar suma, a ka dauketa a ka tafi da ita asibiti, wanda daga bisani a ka kwantar da ita a dakin jinyar masu kula ta musamman. Marigayiyar, ta kasance mata ga tsohon sanatan jamhuriya ta biyu Olusola Saraki, wanda shine jagoran siyasar jihar Kwara kafin Rasuwar shi a shekarar 2012.
Read More
Waƙa: ALLAH JIƘAN SARKI ADO

Waƙa: ALLAH JIƘAN SARKI ADO

Daga KHALID IMAM Lokacin da muke da sarki, Kada sarki a tafki, Goro daushe mai kamala, Wanda kowa ke muradi, Mararin ya gani a kullum, Kowa a cikin ƙasarmu, Kewayenta da duniya kaf, Yasan darajar Kanawa. Lokacin Sarkinmu Ado, Kano da dukkan Kanawa, Sun yi ƙima babu shakka, Lokacin babban sadauki, Dodo namijin mazaje, Ado ɗan abdu zaki, Dukkanin jama'ar Arewa, Sun san a Kano da sarki. Lokacin sarkinmu Ado, Ba ma a Jihar Kano ba, Dukkanin mutumin Arewa, Yai alfahari da tsauni, Wanda ba a yi wa dundu, Lokaci na giye a sarki, Dukkan wani ɗa Bahaushe, Jinjina ya…
Read More
Rarara: Matar aure ko karuwa?

Rarara: Matar aure ko karuwa?

Tare da FARFESA IBRAHIM MALUMFASHI Don Allah Yakubu Musa idan ana kwatancin mawaƙan Hausa, a bar auna Shata da Rarara, hanyar jirgin daban, ta mota daban. Yin haka ina ga "daƙile" muhibba da zalaƙa da gwaninta da ɗaukaka da kuma mutuncin da Shata yake da shi a duniyar waƙar Hausa ne. Rarara ba ajin Shata yake ba, ba ma makarantarsu guda ba kamar yadda na sha faɗa, manta ma da zamani, domin ba a taɓa yin wani irin Shata ba, bare wani ya ce ya kai abin kwantancen sa! Rarara mawaƙin siyasa ne, ko kuma jam’iyyar siyasa da ke iya…
Read More
Sacred Heart: Asibitin farko da aka fara kafawa a Nijeriya

Sacred Heart: Asibitin farko da aka fara kafawa a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Asibitin Sacred Heart da ke Lantoro, Abeokuta ita ce mafi daɗewa kasancewa asibitin farko da aka fara ginawa a Nijeriya, wacce aka kafa a shekarar 1895 a ƙarƙashin kulawar cocin Katolika masu zuwa Abeokuta, wanda Reɓerend Father Coƙuard ya jagoranta. Asibitin ta zuciya ta fara ne a gine-gine na wucin gadi har zuwa kafuwar babban asibitin. An kwantar da asibiti a Itesi, Abeokuta, ranar 14 ga Oktoba, 1904 kuma an kammala shi a ranar 4 ga Mayu, 1914. An kafa ta ne sakamakon cutar kuturta da ta addabi Egbaland tsakanin 1857 zuwa 1859. Asibitin tana cikin…
Read More
Thomas Fuller: Masanin lissafi mafi sauri ɗan Afirika

Thomas Fuller: Masanin lissafi mafi sauri ɗan Afirika

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Thomas Fuller, wanda ake yi wa laƙabi da "Mai lissafin tunani", ɗan asalin Afirka ne da masu satar bayi suka sace shi tun yana da shekaru goma sha huɗu, sannan suka sayarwa Turawa masu sayen bayi a shekarar 1724. Fuller yana da tsananin fikira wajen warware matsalolin lissafi da ka, kuma a cikin ƙanƙanin lokaci. Wata rana an tambaye shi, "daƙiƙu nawa ne a cikin shekara ɗaya da rabi" cikin minti biyu ya bada amsar cewa, "daƙiƙa miliyan arba'in da bakwai, da dubu ɗari uku da huɗu". Haka an taɓa tambayarsa; daƙiƙa nawa mutumin da ya…
Read More
MAKAMASHI: Tallafi, manufa da buri bisa al’ada

MAKAMASHI: Tallafi, manufa da buri bisa al’ada

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI Kafofin yaɗa labarai, musamman jaridu da mujallu, su na da fili daga cikin filayensu da su ke kira da ‘record’, wanda wasu jaridun na harshen Hausa a gida Najeriya su ke kiran wannan fili da fayil, amma a jamhuriyar Nijar kuwa na fassara wannan fili da Dose duk dai da nufin cewa fili ne na a jiyar wani tarihi ga mutumin daya baiyana wannan batu ga karan kansa ko kuma ga ƙasar da yake ciki da ma duniya baki ɗaya. Babban misali da yake cikin fayil-fayil na tarihin ƙasannan shine yadda Marigayi Malam Aminu Kano…
Read More
Batun dawo da martabar noma a Nijeriya

Batun dawo da martabar noma a Nijeriya

Kamar dai yadda kowa ya sani ne cewa, akwai gayar muhimmanci ga gwamnati ta sake duba batun bunƙasa harkokin noma a ƙasar nan, duba da rawar da ɓangaren ke takawa wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasa da samar da wadataccen abinci. Ayyukan noma su ne ginshiki kuma babbar hanyar da za ta iya jure kowace irin kwaramniya ga ci gaban ƙasa tare da al’ummarta baki ɗaya. Noma babbar abu ce a Nijeriya, ana ma kallon cewa ita ce sana’ar da ta fi kowace sana’a muhimmanci, wacce idan babu ita rayuwar ma sam-sam ba za ta yiwuwa ba.Haka zalika, kamar yadda…
Read More