ukarofi

11225 Posts
Zafi ya hana mahajjata jifan shaiɗan

Zafi ya hana mahajjata jifan shaiɗan

Ministan hajji da umarah na ƙasar Saudiyya Dr Abdulfatah bn Sulaiman ya bada umarnin hana mahajjata jifan shaidan daga karfe 11am zuwa 4pm. Sanarwar tace "an ɗauki matakin hana jifan shaidan daga 11am zuwa 4pm. Akwai jami'an tsaro da zasu tabbatar cewa alhazai sun bu wannan umarni domin rashin bin wannan umarni zai zo da hukunci " Muna addu'a Allah ya kiyaye mana mahajjata ya kuma amshi ibadunsu. A wata sanarwar Saudi Gazette, a bana an samu mahajjata kimanin 1,833,164 wanda suka zo daga sassa daban daban na duniya domin sauke farali.
Read More
Ta hanyar faɗaɗa bincike da kallon ƙasata nake samun hikimar rubutu- Safna Jawabi 

Ta hanyar faɗaɗa bincike da kallon ƙasata nake samun hikimar rubutu- Safna Jawabi 

"Akwai ƙalubale ga matasan marubutan da suka dogara ga rubutu" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Mata marubuta sun daɗe suna ba da gagarumar gudunmawa a ɓangaren cigaban adabi da harkokin rayuwa, saboda burin su na ganin sun kawo gyara a cikin al'umma da irin damar da suke da ita. Safna Aliyu Jawabi wata fitacciyar marubuciyar yanar gizo ce, daga Jihar Neja, wacce ta yi suna wajen fitar da littattafai da ke cike da darussa masu muhimmanci. A zantawarta da wakilin Manhaja a Jos, , Safna ta shaida masa cewa, burinta na amfani da muryarta wajen kawo sauyi a rayuwar al'umma shi…
Read More
An tursasa ni auren wanda ba na so, jaruma Ini Edo kan mutuwar aurenta

An tursasa ni auren wanda ba na so, jaruma Ini Edo kan mutuwar aurenta

Daga AISHA ASAS  A karo na farko, fitacciyar jaruma Iniobong Edo Ekim, wadda aka fi sani da Ini Edo, ta buɗe cikinta kan lamarin aurenta da tsohon mijinta, inda ta bayyana takaicinta kan aminta da yin wannan aure da ta yi. A wata tattaunawa da Chude Jideonwo, shahararriyar jaruma kuma mai shirya finafinai, Ini Edo, ta bayyana nadamar ta kan amincewa da ta yi ta auri mijinta wanda suka rabu. Idan mai karatu zai iya kai tunaninsa shekaru baya, jaruma Ini Edo ta auri wani ɗan kasuwa da ke zaune a Ƙasar Amurka mai suna Philip Ehiagwina, a ranar 29…
Read More
Dafin magani ne sanadin mutuwar Mohbad – Rahoto

Dafin magani ne sanadin mutuwar Mohbad – Rahoto

Daga IBRAHIM HAMISU  Rahoton binciken gawar marigayi mawaƙi Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad, ya bayyana yadda dafin ƙwayoyin maganin da ya sha a matsayin dalilin mutuwarsa. A cewa The Cable, gwajin gawar da guba da aka gudanar a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas, ya nuna yiwuwar kamuwa da wata mummunan rashin lafiyar da zai iya zama barazana ga rayuwa ko kuma dafin maganin miyagun ƙwayoyi a matsayin abin da zai iya haifar da mutuwar Mohbad. Rahoton ya bayyana cewa, asibitin ya ɗauko samfurin abubuwan da ke cikin marigayi mawaki Mohbad, na daga hanta, ƙoda da huhu.…
Read More
KSCB ta ƙaddamar da kwamitin mutane 10 kan gasar rubutun da ta shirya 

KSCB ta ƙaddamar da kwamitin mutane 10 kan gasar rubutun da ta shirya 

Daga AISHA ASAS  A wata sanarwar da ta fito daga hannun Abdullahi Sani Sulaiman, Jami’in Watsa Labarai na Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano, ta bayyana shiri na musamman da hukumar ke yi wurin ganin ta gudanar da gasar rubutun da ta saka a makon da ya gabata, don ganin gasar ta samu tsari da nasarar da ake fatan samu. Da wannan ne Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano,  Alhaji Abba El- mustapha ya ƙaddamar da kwamitin mutane 10 da za su bayar da gudunmuwa a gudanar da gasar rubutun Hausa mai zuwa, wadda ta kasance irin ta…
Read More
Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano ta ƙwace yin rajistar ‘yan fim daga ƙungiyoyi zuwa ofishinta

Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano ta ƙwace yin rajistar ‘yan fim daga ƙungiyoyi zuwa ofishinta

DAGA MUKHTAR YAKUBU A yanzu haka dai hukumar tace finafinai ta Jihar Kano ta ƙwace tare da dawo da yin rajistar 'yan fim daga hannun ƙungiyoyin 'yan fim da ta damƙa musu a baya zuwa ofishinta domin ci gaba da yin rajistar 'yan fim ɗin, tare da bayar da tsawon sati uku ga duk wanda bai yi rajistar ba, to ya zama wajibi ya je ofishin Hukumar tace finafinai ya yi rajistar domin kaucewa ɗaukar matakin da ya dace a kansa Haka kuma hukumar ta bayar da umarnin hana daukar duk wani fim ( shooting) ko sakin sa ba tare…
Read More
 Dalilan da ke sa gaban mace wari

 Dalilan da ke sa gaban mace wari

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar Manhaja, a yau za mu tattauna kan dalili ko dalilan da ke sa gaban mace wari, tare da hanyoyin magance shi. Gaban mace wuri ne da ke ɗauke da wani nau'i na ƙamshi da ya saɓa wa wanda gangar jiki ke fitarwa. Wannan ƙamshi dai a wurin wasu suna kiran sa da wari wanda ba a son jin sa, wannan dalilin ne ke sa wasu har turare suke sanyawa a gabansu don kawar da wannan ƙamshin marar daɗi a wurin su. Kaɗan ne suka fahimci cewa,…
Read More
Kuskure ne babba mace ta bar gida don za a yi mata auren dole – Jamila Abdullahi R.Lemo

Kuskure ne babba mace ta bar gida don za a yi mata auren dole – Jamila Abdullahi R.Lemo

Cigaba daga makon jiya Daga AISHA ASAS  A satin da ya gabata idan mai karatu bai shafa'a ba, mun ɗauko tattaunawa da Jamila Abdullahi R.Lemo da kuma Lantana Jafar kan maudu’in mu na auren dole.  Idan mai karatu bai manta ba, mun faro maudu’in tun daga farko, inda muka soma da bayyanin shi kansa auren dole da yadda ake yin sa, alaƙarsa da auren da ake yi a baya na haɗi tare kuma da illolin da ke tattare da auren dole zuwa bambancin sa ga mace da namiji.  Daga ƙarshe muka dasa aya a tambayar da muka yi alƙawarin kawo…
Read More
Kwalera: Adadin wanda suka mutu ya kai 15 a Legas

Kwalera: Adadin wanda suka mutu ya kai 15 a Legas

Kwamisshinan Lafiya na jihar Legas, Farfesa Abayomi Akin ya tabbatar da cewa aƙalla mutane 15 sun rasa ransu sakamakon ɓarkewar annobar kwalera a jihar Legas. Yana faɗin haka ne yayin da yake bayanin irin matakan da gwamnatin take ɗauka domin ganin a daƙile yaɗuwar cutar. Inda yace, an samu mutum 350 da ake zargin suna da cutar daga cikin mazabu 29 a fadin ƙananan hukumomi jihar. Inda aka samu mutum 17 da tabbaacin kamuwa da cutar da kuma 15 da suka rasa ransu. A wata sanarwa daga ma'aikatar lafiya ta jihar Legas, kwamishinan ya nuna cewa an fara samun raguwa…
Read More
Sarki Sanusi ya jagoranci sallar idi a Kano

Sarki Sanusi ya jagoranci sallar idi a Kano

Daga USMAN KAROFI A yau Lahadi ne Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya samu nasarar jagorantar idin Babbar Sallah a Birnin Kano.Gabanin zuwan ranar sallar, an samu barazanar tsaro a Jihar Kano, inda Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta haramta hawan sallah a faɗin jihar biyo bayan taƙaddamar da ke wakana kan karagar Masarautar Kano.A kwanakin baya ne Gwamnatin Jihar Kano ta rattaɓa hannu kan dokar da ta rushe masarautun jihar guda biyar kuma ta dawo da tsohuwar dokar Masarautar Kano ta asali, wanda hakan ya share fagen dawo da Sarki Sanusi a matsayin Sarkin Kano.Wannan lamari…
Read More