Kwalera: Adadin wanda suka mutu ya kai 15 a Legas

Kwamisshinan Lafiya na jihar Legas, Farfesa Abayomi Akin ya tabbatar da cewa aƙalla mutane 15 sun rasa ransu sakamakon ɓarkewar annobar kwalera a jihar Legas.

Yana faɗin haka ne yayin da yake bayanin irin matakan da gwamnatin take ɗauka domin ganin a daƙile yaɗuwar cutar. Inda yace, an samu mutum 350 da ake zargin suna da cutar daga cikin mazabu 29 a fadin ƙananan hukumomi jihar. Inda aka samu mutum 17 da tabbaacin kamuwa da cutar da kuma 15 da suka rasa ransu.

A wata sanarwa daga ma’aikatar lafiya ta jihar Legas, kwamishinan ya nuna cewa an fara samun raguwa daga cutar kamar yadda alkaluman sanya idanu suka nuna.

Ya ƙara da cewa gwamnatin ta buɗe zaman gaggawa a Yaba don gudanar yaƙi da annobar cikin hanzari.