Kuskure ne babba mace ta bar gida don za a yi mata auren dole – Jamila Abdullahi R.Lemo

Cigaba daga makon jiya

Daga AISHA ASAS 

A satin da ya gabata idan mai karatu bai shafa’a ba, mun ɗauko tattaunawa da Jamila Abdullahi R.Lemo da kuma Lantana Jafar kan maudu’in mu na auren dole. 

Idan mai karatu bai manta ba, mun faro maudu’in tun daga farko, inda muka soma da bayyanin shi kansa auren dole da yadda ake yin sa, alaƙarsa da auren da ake yi a baya na haɗi tare kuma da illolin da ke tattare da auren dole zuwa bambancin sa ga mace da namiji. 

Daga ƙarshe muka dasa aya a tambayar da muka yi alƙawarin kawo maku amsar ta kafin wasu tambayoyin su biyo baya. Harwayau dai Aisha Asas ce tare da Lantana Jafar da kuma Jamila Abdullahi Rijiyar lemo.

MANHAJA: Sis Lantana ko akwai wani ƙarin bayani da za ki yi akan wannan?

Illar auren dole ga lafiyar mace yana ɗauke farin ciki tare da gushewar walwalar. Wanda hakan barazana ce ga lafiyarta, musamman idan ta nesanta kanta da mutane. Daga lokacin da ta faɗa a wannan yanayin cuta ta samu gurin zama, musamman ‘Depression’, hawan jini da ciwon zuciya.

Sis Lantana, Matan da ke barin gida a lokacin da aka ce za a yi masu auren dole, ko za a iya kiran hakan a matsayin mafita?

Sam! Hakan ba mafita ba ce. Barin gida na nufin tarwatsa rayuwa gabaɗaya, matuƙar ba a faɗa a hannu na gari ba. Sai dai idan gurin wani shaƙiƙi a ka nufa domin samun maslaha.⁩

Sis Jamila zan so ki yi tsokaci kan matan da ke barin gidan iyayensu da sunan ba za su bari a masu auren dole ba.

Kuskure ne babba ba ƙarami ba, saboda za a yi wa mace auren dole ta ce za ta gudu ta bar iyayenta. 

Wa kike da su waɗanda suka fi su? Ina kike da shi inda ya fi na su? Wa yake sonki a duniya wanda ya fi na su? 

Indai kin yarda da amsa cewa babu, to babu dalilin barin su a kan ƙoƙarinsu na yi miki auren dole. Ina so ki sani duk irin abin da oyaye za su yi wa ‘ya’ya ko su zava musu ba don ba sa sonsu ba ne, sai dai akasi da rashin fahimta, ko kuma bin son ransu. Don haka ki sake tunani wajen zava wa kanki mafita mai kyau wadda ba za ki sava wa Allah da iyayenki ba, kuma sannan ba ki cutar da kanki ba.

Lantana, baya ga lafiyar jiki ko akwai wata matsala da auren dole ke haifarwa mace?

Ƙwarai ma kuwa. Na farko yana haifar da ƙiyayya a tsakanin su ma’auratan,wanda sanadiyyar hakan yake haifar da kisan da mata suke yiwa mazajensu.

Za ki ji an ce mace ta kashe mijinta ko kuma ta yi mai yankar rago. Duk wannan yana faruwa ne sakamakon babu soyayya a tsakaninsu.

Duk tsawon daɗewar da za su yi wannan abin ya riga da ya zama tsa-tsa a zuciyarta.

Kuma mata suna da wannan riƙon ‘naturally’ ko da ta zauna da mutum sama da shekara talatin sai wannan abin ya yi tasiri. A ƙarshe macen ma tana iya kashe kanta.

Bari mu duba auren dole ta vangaren maza. Sis Jamila, shin yi wa namiji auren dole na da illa gare shi?

Ƙwarai kuwa, amma dai ba kamar mace ba. Kowane ɗan adam yana da ‘yanci; duk wanda aka tauye wa haƙƙi ba zai ji daɗi ba, asali ma yi wa namiji auren dole a kan dai mace illar take ƙarewa, kasancewar da wahala ya iya haƙurin zama da ita a rayuwarsa, ba tare da ya musguna mata ba; ta hanyar tsangwama da ƙyara da gori da sauransu. Ita mace takan iya saduda ta haƙura, kuma idan har namiji ya iya gonarsa koda auren dole a kai wa macen da aka haɗa shi da ita, idan shi cin yana sonta, a cikin ruwan sanyi zai iya shawo kan abar shi, amma ita mace da matuƙar wahala kafin ta samu ta juyo da hankalin namijin da ba ya sonta ya so ta, koda kuwa ita tana son shi.

Sannan shi fa namiji yana da iko da damar auren mace fiye da ɗaya zuwa huɗu muddin zai yi adalci, don haka yana da damar auren wadda yake so koda ya auri zavin iyayensa, ke nan yana da ‘yancin sarara wa ta wani vangaren a rayuwar aure.

Kawai dai babbar illar da za ta iya jefa shi a matsala ita ce, idan ya bari hakan ya yi tasiri wajen tauye haƙƙin matar na rashin sauke nauyin da aka ɗora masa bisa aurenta, domin Allah ba ya barin wani da haƙƙin wani.

Idan aka yi wa namiji auren dole tsakanin shi da kuma matar da aka aura masa wane zai fi cutuwa? Gare ki sis Lantana. 

Mace tafi cutuwa ainun. Saboda zata fuskanci ƙalubale kala daban daban, wulaƙanci iri iri. Ba za ta tava samun kulawa ba, zai dinga yi mata abin da ya ga dama, kamar su duka, hantara, rashin cima maikyau,da sutura da sauran ababen more rayuwa.

Idan aka yi da ce mijin ɗan tasha ne har mace zai kawo mata cikin gida ba yanda za ta yi, mai ɗan imani ne zai ƙara aure.

Sis Jamila, wane kira za ki yi ga matan da iyayensu suka ƙuduri yi masu auren dole?

Su yi ƙoƙarin kwantar da hankalinsu, kada su bijire wa iyayensu domin ladabi da biyayya ne suke sa wa a yi wa mutum komai, akwai yiwuwar su sami canza tunani da ra’ayin iyayen a ruwan sanyi. 

Idan ba haka ba, za su iya neman manya a cikin dangi masu faɗa a ji, waɗanda za su iya fahimtar da iyayen illar abin da suke ƙoƙarin yi musu na auren dole ta hanyar kawo masalaha.

Idan abu ya ci tura suna iya nemo babban malamin addini da zai faɗakar da iyayen cikin nasiha da tattausan lafazi, kuma yana da kyau a riƙa tunasar da su yadda auren Nana Fadima (RA) ya kasance domin ya zama abin koyi ga al’ummar Annabi SAW.

Sis Lantana, wacce shawara za ki ba wa iyaye kan yi wa ‘ya’yansu auren dole?⁩

Babbar shawarar da zan ba wa iyaye ita ce, su ji tsoron Allah. A rage kwaɗayi da dogon buri. Sannan su bar ‘ya’yansu su zavi abokan rayuwa wanda suke ganin zasu iya zama tare cikin farin ciki.

Sis Jamila, me za ki ce wa mazan da iyaye suka aura masu matan da ba sa so?⁩

Su ji tsoran Allah su yi wa iyayensu biyayya domin ta hanyarsu za su iya samun aljannah. Sannan su ji tausayin rauni da rayuwar ‘ya mace su mutumta ta, koda ba sa sonta, su kuma yi mata adalci ko sun sake auro wata ko ba su auro ba, komai na rayuwa mai wucewa ne, yau da gobe ba ta bar komai ba; masoyinka na iya zama maƙiyinka, makiyinka na iya zama masoyinka.