ukarofi

11225 Posts
Dalilina na sauka daga muƙamin kocin Super Eagles – Finidi George

Dalilina na sauka daga muƙamin kocin Super Eagles – Finidi George

Finidi George ya bayyana dalilan ajiye muƙamin mai horar da Super Eagles. Tsohon dan wasan Ƙungiyar kwallon kafa ta Ajax ya bayyana haka ne a wata takardar ajiye aiki da ya aikewa shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya Alhaji shehu Gusau. Hakan ya biyo bayan canjin da ake so ayi wa tawagar masu aiki da mai horar wa. "Ina miƙa saƙon godiya da hukumar ƙwallon kafa ta Najeriya da ita kanta Ma'aikatar wasannin ta ƙasa"
Read More
Ban damu ba don wata rana wani gwamna ya cire ni – Sarki Sanusi

Ban damu ba don wata rana wani gwamna ya cire ni – Sarki Sanusi

Alhaji Muhammadu Sanusi II, sarkin kano na 16 yace ba zai damu ba don wata gwamnatin ta zo ta cire shi ba. Tsohon Gwamna Abdullahi Gamduje ya tsige Sanusi saboda wani matsala dake tsakanin su. Yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara naɗa Sarki Sanusi, Sarkin kano na 15 Aminu Ado ya garzaya Kotu domin Ƙalubalantar cirewar. Yayin da yake ganawa da jaridar Saturday Sun, Sarki Sunusi ya ce, bai san tsawon lokacin da zai daɗe a kan karagar mulkin. Ya ƙara da cewa, shi kansa da yake kai yanzu, Allah ne kaɗai ya san lokacin da zai kai…
Read More
Gwamna Dauda Lawal ya karrama askarawa 20 a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal ya karrama askarawa 20 a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal yayi alƙawarin ɗaukar nauyin iyalan askarawan wanda suka rasa ransu a yayin yaƙi da ɓarayin daji. Askarawa 20 ne aka karrama da lambobin girma saboda jajircewar su a ranar Alhamis a gidan Gwamnatin da ke Gusau. A wani jawabi da mai magana da yawun Gwaman Sulaiman Bala Idris yayi, yace askarawan tabbas sun nuna bajinta sosai. A cewar jawabin, askarawan na ƙarkashin Jagorancin Birgediya Janar Lawal Bature Muhammad. "A ranar Alhamis, Gwamna Dauda Lawal ya karrama 20 daga cikin askarawan saboda jajircewa wajen yin aiki tuƙuru. Dukkan 20 din suna kan gaba gaba wajen yaƙi da ɓarayin…
Read More
Gwamnoni na amfani da ɓatagari wajen magudin zaɓe —Jonathan

Gwamnoni na amfani da ɓatagari wajen magudin zaɓe —Jonathan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi zargin cewa wasu gwamnonin jihohi sun shagaltu da karfafawa masu aikata laifuka don amfani da su wajen cimma manufar siyasa, maimakon karfafa gwiwarsu su zama kwararru a ma’aikatun gwamnati. Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Benin yayin da yake kaddamar da sakatarorin jihar da Gwamna Godwin Obaseki ya gyara. Tsohon shugaban kasar ya ce, lokacin da shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa Obaseki ya dauki wadanda suka kammala digiri na farko aiki, ya ji dadi matuka, yana mai cewa “yana bukatar wani mai hangen nesa…
Read More
Muƙamin Matawalle a matsayin ministan tsaro bai amfana wa Zamfara komai ba — Gwamna Lawal

Muƙamin Matawalle a matsayin ministan tsaro bai amfana wa Zamfara komai ba — Gwamna Lawal

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce jihar ba ta ci gajiyar nadin da aka yi wa magabacinsa, Bello Matawalle a matsayin karamin ministan tsaro ba. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani shiri na kai-tsaye a gidan Talabijin na Channels Television na Sunrise Daily a ranar Talata. “Abin mamaki ne ko yaushe idan wannan batu na Ministan Tsaro ya taso. Eh, shi ne Karamin Ministan Tsaro, amma me ya amfana mana? Kimanin makonni kadan da suka gabata ne ‘yan bindiga suka je garinsu, suka kashe mutane da dama, me ya yi akai? “Eh,…
Read More
Yuni 12: Uba Sani ya yi wa fursinoni 110 afuwa a Kaduna

Yuni 12: Uba Sani ya yi wa fursinoni 110 afuwa a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Domin murnar zagayowar ranar Dimokuradiyya a Nijeriya gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayar da umarnin a saki fursunoni 110 daga gidan gyaran hali da ke jihar. Gwamna Sani ya yi haka ne somin tabi na wani a zaman wani bangare na bikin ranar dimokradiyya na bana da kuma murnar cika shekara guda a kan karagar mulki. Gwamna Sani tare sa wasu manyan jami’an gwamnati sun ziyarci gidan gyaran hali na jihar Kaduna tare da fitattacen lauya Femi Falana (SAN), inda ya bayyana bukatar a yi garambawul a gidajen gyaran hali da ke jihar…
Read More
An bada umarnin bincike kan lamarin makarantar Iyana Ipaja

An bada umarnin bincike kan lamarin makarantar Iyana Ipaja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa ba tare da nuna son kai ba kan lamarin da ya faru a makarantar Sakandaren Sojoji ta Iyana Ipaja, Legas. Wannan matakin dai ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Gwamnati ta Nijeriya (ACSSN) ta nuna dangane da yadda ake yi wa ma'aikata farar hula a makarantar. A cikin wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya sanya wa hannu, ya ce binciken da Proɓost Marshal ya jagoranta, zai yi nazari sosai…
Read More
Yan sanda sun janye jami’ai masu bai wa manya kariya

Yan sanda sun janye jami’ai masu bai wa manya kariya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, mai kula da yankin Kudu maso Yamma, Sylvester Alabi, ya ce an janye jami’an ’yan sandan da ke bai wa wasu masu fada a ji a ƙasar nan, a wani mataki na magance matsalar ƙarancin ma’aikata a rundunar ’yan sandan. Abiodun ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Ado-Ekiti a ziyarar da ya kai hedkwatar ’yan sandan jihar Ekiti. Da yake magana da ’yan jarida, ya ce, “Akwai lokacin da za a iya kaiwa ga matakin tura jami’an, amma ba a wannan lokaci ba. Mun fahimci cewa akwai wasu…
Read More
Sallah: Kiristoci sun taya Musulmai share filin idi a Kaduna

Sallah: Kiristoci sun taya Musulmai share filin idi a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A wani gagarumin bajekoli na hadin gwiwa tsakanin mabiya addinai, wani fasto ya jagoranci Ƙungiyar Kiristoci domin taya Musulmi tsaftace filin sallar Idi a wani ɓangare na bikin Babbar Sallah a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna. Wannan shiri dai an yi shi ne domin samar da zaman lafiya, tattaunawa tsakanin addinai, haƙuri da juna, fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban na yankin da ma jihar bakidaya. Fasto Yohanna Buru, Babban mai sa ido kuma faston cocin Christ Evangelical and Life Intervention, ya shirya tawagar Kiristocin da suka je filin Sallar Idi domin tsaftace filin a…
Read More
Zargin cin zarafin mace: Shugabar Ma’aikata ta dakatar da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje

Zargin cin zarafin mace: Shugabar Ma’aikata ta dakatar da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ofishin Shugaban Ma’aikata na Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ya dakatar da Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje, Ambasada Ibrahim Lamuwa, bisa zargin cin zarafin mata. Shugabar Ma’aikata, Folashade Yemi-Esan, ta ce za a dakatar da sakatare na dindindin har sai an kammala bincike cikin gaggawa kan zargin da ake masa. Wani babban darakta a OHCSF ya shaida wa wakilinmu a Abuja cewa, "an dakatar da sakatare na dindindin har sai kwamitin da a ka kafa ya kammala bincikensa." An tattaro cewa, biyo bayan koken da Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya gabatar a kan…
Read More