Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, mai kula da yankin Kudu maso Yamma, Sylvester Alabi, ya ce an janye jami’an ’yan sandan da ke bai wa wasu masu fada a ji a ƙasar nan, a wani mataki na magance matsalar ƙarancin ma’aikata a rundunar ’yan sandan.
Abiodun ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Ado-Ekiti a ziyarar da ya kai hedkwatar ’yan sandan jihar Ekiti.
Da yake magana da ’yan jarida, ya ce, “Akwai lokacin da za a iya kaiwa ga matakin tura jami’an, amma ba a wannan lokaci ba. Mun fahimci cewa akwai wasu wuraren da muke buƙatar sake tura jami’ai musamman ake fama da matsalolin tsaro. An magance batun ɓarnatar da ma’aikata ba gaira ba dalili.
“A taƙaice, ba mu da isassun ma’aikata, shi ya sa gwamnatin tarayya ta amince daɗaukar ƙarin mazaje akai-akai domin ba mu damar gudanar da aikinmu yadda ya kamata,” inji shi.
Alabi ya kuma ce rundunar ‘yan sandan Nijeriya za ta yi la’akari daɗaukar jirage marasa matuƙa da sauran hanyoyin fasaha, domin mayar da jihar Ekiti da sauran ƙananan hukumomin ƙasar nan ba tare da aikata laifuka ba.
DIGɗin ya ƙara da cewa, rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yin amfani da jirage marasa matuƙa, yana mai cewa hukumar tsaron za ta yi amfani da fasahohi iri-iri a wani yunƙuri na cimma matsaya na aikata laifuka a ƙasar.
“Zowata jihar Ekiti shi ne in kammala aikina a shiyyar siyasa ta kudu maso yamma.
“Aiki na ya bi sahun babban sufeton ’yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, wanda ya umurci dukkan DIP da ke kula da shiyyoyin siyasa shida da su fara rangadi a shiyyoyi shida na siyasa tare da samun damar shigar da maƙamanmu dabarun yaƙi da aikata laifuka, duba yadda jami’an mu ke gudanar da ayyukansu.
“Wannan shi ne don mu san ƙalubalen da suke fuskanta a yayin gudanar da aikinsu domin a magance su yadda ya kamata, ta yadda za a inganta ƙarfinsu da sassaukarsu wajen isar da ayyuka masu kyau ga jama’a.
“Har yanzu bai ƙare ba, haɓaka fasaha ya fi muhimmanci. Na’urori kamar jirage marasa matuƙa da za su tattara mana bayanai, za su tono maboyar masu garkuwa da mutane za su taimaka wajen magance su maimakon mu ceto wadanda abin ya shafa.
“Fasaha na da matuƙar muhimmanci, ba shakka za mu yi hijira don kwaikwayi ci gaban fasaha. A bayyane yake cewa ba za mu iya yin amfani da aikinɗan sanda yadda ya kamata ba tare da hada na’urorin fasaha don taimaka mana ba.
“Ba za mu guje wa amfani da jirage marasa matuƙa ba, za mu saba da shi,” inji shi.
A jawabinsa na maraba, kwamishinan ’yan sandan jihar Ekiti, Akinwale Adeniran ya yaba wa DIG bisa jajircewarsa da kuma sadaukar da kai ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
Ya ƙara da cewa, rundunar a ƙarƙashin jagorancinsa ta samu nasarar daƙile ayyukan masu aikata miyagun laifuka a fadin jihar ta hanyar samar da yanayi mai kyau ga ’yan jihar Ekiti ta hanyar amincewa da aiwatar da dabarun aikin ’yan sanda.
