07
Mar
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Gwamnonin Jihohin Nijeriya (NGF), ta bayyana cikakken goyon bayanta ga sabbin gyare-gyaren da ke wajabta tura dukkan haƙƙoƙin kuɗaɗen shiga daga man fetur da iskar gas kai tsaye cikin Asusun Tarayya. Kungiyar ta ce, wannan mataki yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya a harkokin kuɗi, daidaito a tsari, da kuma bin tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki. Wannan matsayi na ƙungiyar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na NGF, Yunusa Tanko Abdullahi, ya sanya wa hannu a ranar 2 ga Maris, 2026. A cewar sanarwar, ƙungiyar ta yi nazari…
