ukarofi

12641 Posts
Kungiyar Tsangaya ta naɗa Gwani Ibrahim a matsayin shugabanta na ƙasa

Kungiyar Tsangaya ta naɗa Gwani Ibrahim a matsayin shugabanta na ƙasa

Daga WAKILINMU Kungiyar Tsangaya da ke fafutukar samar da ci gaba ga malaman tsangaya da almajirai a faɗin Nijeriya, ta naɗa Gwani Ibrahim Mai Bindiga Hadejia a matsayin sabon Shugabanta na ƙasa. An gudanar da bikin naɗin ne a yau Talata, 27 ga watan Janairu, a dakin taro na Naicon Luɗury Hotel da ke Abuja. Taron ya samu halartar manyan shaihunnai da gwanayen Alƙur’ani mai girma daga sassa daban-daban na ƙasar nan. Mahalarta taron sun bayyana naɗin a matsayin wani babban ci gaba ga harkokin ƙungiyar Tsangaya, suna masu cewa shugabancin Gwani Ibrahim Mai Bindiga zai samar wa almajirai dama…
Read More
Yadda APC da ADC ke sabunta rajistar mambobinsu

Yadda APC da ADC ke sabunta rajistar mambobinsu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam'iyyun siyasa a Nijeriya sun ƙara ƙaimi wajen sabinta rijartar mambobinsu yayin da wa'adin da aka gindaya domin kowacce ta miƙawa hukumar zaɓen ƙasar cikakkiyar rijistar ke kawo jiki. Wannan na daga cikin shirye-shiryen tunkarar baban zaɓen ƙasar na 2027. A ƙarƙashin sabon jaddawalin zaɓen da hukumar zaɓen Nijeriya, INEC ta fitar, ana buƙatar jam'iyyun siyasar ƙasar su gabatar da cikakkiyar rijistar mambobinsu ya zuwa ranar 2 ga watan Afirelun 2026. Umarnin da INEC ta bai wa jam'iyyun siyasar na daga cikin tanadin dokar zaɓen Nijeriya ta 2026, wadda ke neman inganta yadda jam'iyyun…
Read More
Da na ci amanar Geidam gara na mutu — Mai Mala Buni

Da na ci amanar Geidam gara na mutu — Mai Mala Buni

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce ba zai taɓa cin amanar ubangidansa na siyasa kuma tsohon gwamnan jihar ba, Ibrahim Geidam, wanda yanzu shi ne Ministan Harkokin ’Yan Sanda. Buni ya bayyana hakan ne yayin taron zaɓen shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar Yobe da ke Damaturu. Gwamnan ya ce siyasarsa ta fara ne da goyon baya da amincewar Geidam. Kafin ya zama gwamna, Buni ya taɓa zama Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Siyasa a lokacin mulkin Geidam. Daga baya kuma ya zama Sakataren jam’iyyar APC…
Read More
Doguwa ya zama shugaban  jam’iyyar APC na Jihar Kano

Doguwa ya zama shugaban  jam’iyyar APC na Jihar Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Tsohon Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Hon. Umar Haruna Doguwa, ya zama sabon Shugaban jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) a Jihar Kano. An gudanar da zaɓensa ne a taron babban zaɓen jam’iyyar na jiha, wanda ya kammala a safiyar Laraba ƙarƙashin kulawar Kwamishinan Zaɓe na INEC a Kano, Ambasada Zango Abdu. Wakilai daga ƙananan hukumomi 44 na jihar sun amince da Doguwa da sauran ‘yan takarar maslaha ta hanyar kaɗa ƙuri’ar murya, a wani tsari da majiyoyin jam’iyyar suka bayyana a matsayin mai cike da zaman lafiya da gaskiya. An ware kujerar shugabancin ga Yankin Sanatan Kano…
Read More
Adamawa: Dan Atiku Abubakar ya ajiye muƙaminsa na kwamishina bayan sauyin sheƙar Fintiri zuwa APC

Adamawa: Dan Atiku Abubakar ya ajiye muƙaminsa na kwamishina bayan sauyin sheƙar Fintiri zuwa APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Adamu Atiku-Abubakar ya ajiye muƙaminsa a matsayin kwamishinan ayyuka da bunƙasa makamashi na jihar Adamawa. Mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Abdulaziz Jauro, ne ya sanar da hakan. Ana dai sa ran ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai koma jam’iyyar ADC. Tsohon kwamishinan ya gode wa gwamna Ahmadu Fintiri “kan ba shi dama da ganin cancantarsa na rike muƙamin.” Ya kuma bayyana cewa wannan dama karramawa ce a gare shi inda ya yi alƙawarin ci gaba da mara wa shirin gwamnatin baya na kawo ci gaba a jihar. “Tsohon kwamishinan ya miƙa…
Read More
Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 45 a Katsina

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 45 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wata takarda ɗauke da sa hannun kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu'azu Ɗanmusa, ya bayyana cewa cikin 'yan bindigan da sojojin suka kashe har da babban kwamandan 'yan bindigan Adamu Alieru. Haka kuma Sojojin sun sami nasarar kashe Alti wanda shine mataimakin kwamandan 'yan bindigan kuma ɗan'uwa ga Adamu Alieru da Damale shima ɗaya daga jagororin 'yan bindigan. A cewar kwamishinan ɓangaren sojoji Kaftin Paul Hassan da wasu mutum biyu suka rasa ransa a ɗauki ba daɗi da sojojin suka yi da 'yan bindigan a ƙaramar hukumar Ɗanmusa. Ya ce tun da…
Read More
Ƙungiyar lauyoyi ta bayyana jigon makon shari’a na 2026 a Gombe

Ƙungiyar lauyoyi ta bayyana jigon makon shari’a na 2026 a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen jihar Gombe, NBA, ta bayyana jigo tare da kaddamar da tambarin makon shari’a na shekarar 2026, yayin da manyan lauyoyi suka nuna goyon bayansu ta hanyar bayar da gudummawar kuɗi da kuma alƙawarin tallafawa shirin. Da yake jawabi a wajen taron ƙaddamarwar da aka gudanar a Gombe, shugaban ƙungiyar NBA na reshen Gombe, Barrista Alhassan Mu’azu, ya bayyana cewa taron ya samu halartar sama da mutum 500 da suka haɗa da lauyoyi, ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren shari’a. Ya ce jigon makon shari’ar na…
Read More
Yadda motar NSCDC ta murƙushe jami’a ana tsaka da atisaye a Abuja

Yadda motar NSCDC ta murƙushe jami’a ana tsaka da atisaye a Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata jami’a ta Hukumar Tsaro da Kare Lafiyar Al’umma ta Nijeriya, wato Sibil Difens (NSCDC), ta rasu bayan wata motar aiki ta hukumar ta murƙushe ta yayin atisayen horaswa da aka gudanar a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Lamarin ya faru ne a lokacin wani atisayen nuna ƙarfi da ake kira “show of force” na rundunar mata ta musamman ta hukumar, wacce aka fi sani da Female Strike Force ko Female Sƙuad.  Bidiyon da ya yaɗu na tsawon daƙiƙu 58 ya nuna yadda wata baƙar mota mai ɗauke da rubutun “Female Sƙuad” ta wuce kan jami’ar, yayin…
Read More
Dalibin likitanci a Jami’ar Ibadan ya kashe kansa saboda samun ƙarancin maki

Dalibin likitanci a Jami’ar Ibadan ya kashe kansa saboda samun ƙarancin maki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani ɗalibin likitanci mai karatu a mataki na 200 a Jami’ar Ibadan (UI), mai suna Ifeoluwa Wisdom Akinmade, ya rasu bayan zargin cewa ya sha maganin ƙwari a daren Lahadi. Rasuwar ɗalibin ta fito ne cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar ɗaliban Likitanci ta jami’ar (UIMSA), Folusho Olu-Adegbola, da Sakatarenta, Babatunde Dauda, suka sanyawa hannu a ranar Litinin. A cikin sanarwar, sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne duk da ƙoƙarin gaggawar jinya da likitoci suka yi domin ceton rayuwarsa. Sanarwar ta ce: “Cikin alhini da zuciya mai nauyi muke sanar da rasuwar dan uwanmu kuma…
Read More
VAT: ’Yar kasuwa ta koka kan ƙaƙaba mata harajin Naira miliyan N11.7

VAT: ’Yar kasuwa ta koka kan ƙaƙaba mata harajin Naira miliyan N11.7

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata ’yar kasuwa ’yar Nijeriya ta fito fili a kafafen sada zumunta tana nuna mamaki da kaɗuwa bayan da ta ce jami’an Hukumar Haraji ta Nijeriya sun aike mata da takardar kimanta haraji da ya kai Naira miliyan 11.7. A cikin wani bidiyo da ta wallafa, ’yar kasuwar ta bayyana cewa jami’an haraji sun ziyarci shagonta tare da lissafa mata bashin haraji tun daga shekarar 2022, alhali a cewarta a wancan lokacin ba ta fara amfani da sabon sunan kasuwancinta ba, haka kuma ba ta buɗe asusun kasuwanci a ƙarƙashin wannan suna ba. Ta yi tambaya…
Read More