ukarofi

12641 Posts
Iran da ƙasashen Musulunci: Abinda ya taɓa gira fa shi ne zai taɓa ido

Iran da ƙasashen Musulunci: Abinda ya taɓa gira fa shi ne zai taɓa ido

Daga AISHA ASAS A can kwanakin bayan a shafin Iyali mun taɓa darasi kan yadda rarabuwar kawuna a addini ya jefa Musulunci cikin halin da yake a yanzu. Inda a halin da muke ciki kowane ɓangare na kallon ɗaya a matsayin wanda ba muslmi ba. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ya rage ƙarfin Musulunci duk da tarin mabiya da yake da shi. Shafin ƙasashen Waje na wannan makon zai tattauna kan yaƙin Iran da yadda ƙasashen Musulunci suka koma gefe suna kallo yayin da wasu ke ganin hakan a matsayin daidai. Tun bayan juyin juya halin Musulunci na…
Read More
Kotu ta garƙame uwa da ’yarta kan satar manja

Kotu ta garƙame uwa da ’yarta kan satar manja

Wata kotun majistare da ke Ile-Ife a ranar Alhamis ta yanke wa wata mata da ’yarta hukuncin ɗaurin watanni shida kowacce, bisa samunsu da laifin satar manja. Waɗanda aka yanke wa hukuncin su ne Toyin Ojo mai shekaru 57 da Esther Ojo mai shekaru 23. Rundunar ’yan sanda ta gurfanar da su ne kan tuhume-tuhume biyu da suka haɗa da haɗa baki da kuma satar lita 25 na man gyaɗa da kuma lita 25 na manja. Dukkaninsu sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi bayan an karanta musu tuhumar a gaban kotu. Mai gabatar da kara, Sufeto Adesina Elijah,…
Read More
Karancin gas ya janyo raguwar lantarki zuwa megawat 4,300 – NISO

Karancin gas ya janyo raguwar lantarki zuwa megawat 4,300 – NISO

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Tsarin Lantarki ta ƙasa (NISO), ta danganta raguwar samar da wutar lantarki a faɗin Nijeriya da matsalar ƙarancin iskar gas da kuma takurawar ƙarfin samar da wuta daga tashoshin samarwa. A cikin wata sanarwa da mahukuntan ɓangaren gudanar da tsarin wutar suka fitar a ranar Juma’a, sun bayyana cewa matsalolin biyu sun haddasa faɗuwar matsakaicin wutar da ake iya samarwa zuwa megawatt 4,300 kacal. Hukumar ta ce, mafi yawan tashoshin samar da wutar lantarki na tururi (thermal plants) ba su iya aiki yadda ya kamata ba sakamakon rashin wadataccen gas. Sanarwar ta yi…
Read More
Hukumar NDIC ta bayyana yadda ake biyan masu ajiya a bankunan da suka rushe

Hukumar NDIC ta bayyana yadda ake biyan masu ajiya a bankunan da suka rushe

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Hukumar Inshorar Ajiya ta Nijeriya (NDIC), Oludare Sunday, ya yi cikakken bayani kan yadda hukumar ke biyan masu ajiya a bankunan da suka gaza tare da shiga matakin rushewa, yana mai jaddada cewa akwai iyaka da doka ta gindaya wajen biyan kuɗaɗen. Ya bayyana hakan ne a lokacin zaman kare kasafin kuzin shekarar 2026 a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Inshora da Ilimin Kimiyyar Lissafin Haɗari, wato ‘Actual Matters’, wanda ya gudana a Abuja. A yayin zaman, Mai Magaba da Yawun Majalisar Wakilai kuma mamba a kwamitin, Honarabul Akin Rotimi Jr, ya nemi ƙarin…
Read More
Tinubu zai kafa yankin kasuwanci na musamman mai faɗin hekta 4,000 a Kogi

Tinubu zai kafa yankin kasuwanci na musamman mai faɗin hekta 4,000 a Kogi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa Yankin Kasuwanci na Musamman (Free Trade Zone) mai faɗin hekta 4,000 a Jihar Kogi, a wani mataki da ake ganin zai buɗe sabuwar babi wajen farfazo da masana’antu da kuma cika burin sake tayar da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta da ya daɗe yana tangal-tangal. Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin karcar takardar lasisin sabuwar Ajaokuta Free Trade Zone daga hannun Hukumar Kula da Yankunan Sarrafa Kayayyakin Fitarwa ta Nijeriya (NEPZA). Gwamnan ya bayyana matakin a matsayin tsalle zuwa sahun gaba na bunƙasar masana’antu,…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta fara tura kuɗaɗen fetur kai tsaye zuwa Asusun Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta fara tura kuɗaɗen fetur kai tsaye zuwa Asusun Tarayya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da Umarnin Zartarwa na 9 na shekarar 2026, wanda ya tanadi cewa dukkan kuɗaɗen shiga daga harkokin man fetur su riƙa shiga kai tsaye zuwa Asusun Kwamitin Raba Kuɗin Tarayya (FAAC). Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Wale Edun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya yi bayani kan muhimman matsayi da aka cimma a taron kwamitin aiwatar da umarnin. Matakin ya biyo bayan umarnin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na cewa a riƙa mayar da dukkan kuɗaɗen man fetur da suka…
Read More
Matsin lamba ko son rai: Yadda BBL da bilicin suka zama al’ada a masana’antun nishaɗi

Matsin lamba ko son rai: Yadda BBL da bilicin suka zama al’ada a masana’antun nishaɗi

Daga AISHA ASAS A cikin 'yan shekaruna nan an samu sauyi mai girma a yadda mata musamman masu harkar fim ke kallon matsayin jikinsu da fata. Tagomashin dirin jikin mace da kuma hasken fata sun zama ababen mafi tattaunawa a kafafen sada zumunta. Maza da yawa na yaba mata masu hasken fata da kuma diri, wataƙila hakan ne ke sa mata fita hayyacinsu wurin neman mallakar waɗannan abubuwa ido rufe. A can baya, mata kan dogara da ababen jiƙo ko kayan magunguna don ƙara girman mazaunai ko nono, ko kuma samun hasken fata, waɗanda akasari ba su cutarwa saidai su…
Read More
AFAN ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta rage farashin kayan aikin gona

AFAN ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta rage farashin kayan aikin gona

Daga WAKILINMU ƙungiyar Manoma ta ƙasa, wato AFAN, ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta yi ƙoƙarin rage kuɗin kayan aikin gona domin manoman ƙasar nan su samu damar bunƙasa sana’ar noma cikin nasara. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Muhammad Magaji Gettado, shi ne ya yi wannan roƙo yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya bayyana cewa idan aka samar da rangwamen kayan aikin gona kamar taki da iri da kuma magungunan feshi, babu shakka noma zai kara bunƙasa a Nijeriya. Ya ce idan kayan aikin gona sun zama masu sauki, manoma za su ƙara ƙarfin gwiwar faɗaɗa ayyukansu na noma,…
Read More
Tsarin tattalin arzikin Tinubu ya ceto Nijeriya daga almubazzaranci – IMPI

Tsarin tattalin arzikin Tinubu ya ceto Nijeriya daga almubazzaranci – IMPI

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Kafofin Yaɗa Labarai Masu Zaman Kansu da Shirye-Shiryen Manufofi (IMPI) ta bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo gagarumin sauyi a tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar aiwatar da manufofin ci gaba na tattalin arziki, wanda ya taimaka wajen fitar da ƙasar daga dogon zamani na almubazzaranci da rashin tsari. A cikin wata sanarwar manufofi da Shugaban ƙungiyar, Dakta Omoniyi Akinsiju, ya rattaba hannu a kai, IMPI ta jaddada cewa wannan salo na gyaran tattalin arziki shi ne mafi dacewa wajen warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye tsarin kuɗi da tafiyar da harkokin…
Read More
AMATA ta koka kan rashin wakilci a kwamitin binciken gobarar kasuwar Singa

AMATA ta koka kan rashin wakilci a kwamitin binciken gobarar kasuwar Singa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ’Yan Kasuwa ta Jihar Kano (AMATA) ta bayyana ƙorafi kan cewa ba a ba ta wakilci a ƙunshin kwamitin da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin duba batun gobarar da ta auku a Kasuwar Singa. ƙungiyar ta kuma gudanar da taron saukar Alƙur’ani da addu’o’i na musamman domin neman kariya ga jihar da kasuwanninta, sakamakon yawaitar gobara, musamman wadda ta auku a Kasuwar Singa. Shugaban AMATA na jihar, Alhaji Abdul’Aziz ɗalha Musa, ya bayyana cewa an shirya addu’o’in ne domin neman yafiya da kariyar Allah kan iftila’in gobarar da ta jawo asarar dukiya…
Read More