ukarofi

12639 Posts
Rikicin Gabas Ta Tsakiya: Yadda Gurnanin Zaki ke firgita manyan kuraye

Rikicin Gabas Ta Tsakiya: Yadda Gurnanin Zaki ke firgita manyan kuraye

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ƙasa da mako guda mummunan rikici ya ɓarke a yankin Gabas Ta Tsakiya, tsakanin ƙasashen Amurka da Isra'ila a gefe guda da kuma ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Rikici ne wanda an daɗe ana hasashen faruwarsa, sakamakon yadda dangantaka ta daɗe tana tsami tsakanin ƙasar Amurka da Iran, ganin yadda Amurka ke cigaba da goya wa ’yarlelenta, wato ƙasar Yahudawan Isra'ila baya tana cin karenta babu babbaka, kan raunanan ƙasar Falasɗinu da mujahidan ƙungiyar Hizbullahi na ƙasar Lebanon. Da ma yadda take yi wa dokokin ƙasa da ƙasa karan tsaye, wajen barazana ga sauran ƙasashen…
Read More
Jam’iyyar APC a Zamfara ta yi wa Gwamna Dauda lale marhabin

Jam’iyyar APC a Zamfara ta yi wa Gwamna Dauda lale marhabin

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar APC a Jihar Zamfara ta yi maraba da Gwamna Dauda Lawal da magoya bayansa cikin jam'iyyar. Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na jihar Yusuf Idris ya sanya wa hannu a yammacin yau. Sanarwar ta bayyana cewa, shugabannin jam'iyyar, ciki har da ƙaramin ministan tsaro, Bello Muhammad Matawalle, sun bayyana ƙwarin gwiwar cewa shigar Lawal zai ƙarfafa zumunci tsakanin mutanen Zamfara da kuma ƙara wa jam'iyyar ƙwarin gwiwa a babban zaɓen 2027. Jam'iyyar ta tabbatar wa Gwamna Lawal cikakken goyon baya da haɗin kai daga mambobin jam'iyyar,…
Read More
Gwamnan Zamfara da mataimakinsa sun koma APC daga PDP

Gwamnan Zamfara da mataimakinsa sun koma APC daga PDP

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal da mataimakinsa Malam Mani Muminu tare da mambobin majalisar zartarwa ta jihar sun sanar da shawararsa ta barin jam'iyyar PDP zuwa shiga jam'iyyar APC. Mataimakin gwamnan jihar Malam Mani Muminu ya sanar da hakan a wata hira da manema labarai a ƙarshen taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatin Gusau ranar Litinin. "An yanke shawarar ne a taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati da ke Gusau, a daidai lokacin da rikicin cikin gida na PDP ke ƙara ta'azzara". Ya ce. Mataimakin gwamnan Malam Mani Mummuni ya bayyana…
Read More
Boko Haram sun sake kashe wani kwamandan soji a Borno

Boko Haram sun sake kashe wani kwamandan soji a Borno

Daga USMAN KAROFI ‘Yan ta’addar Boko Haram sun kai wani sabon hari kan sansanin sojoji a Jihar Borno, inda suka kashe kwamandan sansanin da wasu sojoji. Harin ya faru ne a ƙaramar hukumar Kukawa da sanyin safiyar ranar Litinin. Wata majiya daga garin ta bayyana cewa maharan sun kai harin ne kusan ƙarfe 12:30 na dare, inda suka shigo daga ɓangarori daban-daban suka afkawa sansanin sojojin. Wata majiya ta tsaro ta ce maharan sun tilasta wa sojojin janyewa daga sansanin, sannan suka kona wasu motocin sojoji tare da kwashe makamai da alburusai. A watan da ya gabata dai maharan sun…
Read More
Yadda badaƙalar Walida Abdulhadi da Ese Oruru suka yi kamanceceniya

Yadda badaƙalar Walida Abdulhadi da Ese Oruru suka yi kamanceceniya

Bai kamata a bambanta shari'ar Walida Ese ba, inji masu sharhi  Daga AISHA ASAS Rayuwar 'ya mace rayuwa ce mai rauni, wanda hakan ya sa a duk tsayin rayuwarta tana yin ta ne a ƙarƙashin kulawar wani. Sai dai idan na ce kulawar wani ba Ina nufin kowa ya tara hannu za ta faɗa ba. Ita mace kamar yadda take da rauni haka take da mautuƙar hatsari idan ta samu kanta a inda ba haka tsarin addini ko al'ada ya tanada ba. A cikin kowane yare ko addinan da muke da su manya a nan Najeriya, babu wanda ya amince…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya yi murnar ranar mata ta duniya

Gwamna Raɗɗa ya yi murnar ranar mata ta duniya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A saƙon sa na bikin ranar Mata na duniya Malam Dikko Raɗɗa ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa rayuwa, mutunci da ‘yancin tattalin arzikin mata a faɗin jihar. Ya bayyana cewa zuba jari ga mata tamkar zuba jari ne ga al’umma baki ɗaya. Ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da wannan kuduri ta hanyar ɗaukar matakai masu amfani a aikace. “Idan ka tallafa wa mata, al’umma baki ɗaya za ta amfana. Wannan shi ne ma’anar taken bana ‘Ba da domin Samu’. A Jihar Katsina ba kawai magana muke yi…
Read More
An yi kira ga Gwamnan Katsina ya shiga lamarin aikin hanyar Bakori zuwa Funtua

An yi kira ga Gwamnan Katsina ya shiga lamarin aikin hanyar Bakori zuwa Funtua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar cigaban yankin Funtua ya yi kira ga Gwamnan Katsina ya shiga lamarin aikin hanyar Bakori zuwa Funtua a hira da manema labarai a Katsina. Ya ce kiran ya zama dole ganin yadda hanyar ta lalace da ta kai ana fashi da makami ga lalacewar ababen hawa. Kwamred Suleiman ya bayyana cewa wannan hanya da ta tashi daga Funtua ta bi ta Bakori itace ta wuce Malumfashi zuwa gidan mutum ɗaya ta kai shekaru 40 da gina wa. Ya ce banda ma fashi da makami da lalacewar ababen hawa akwai yawaitar hare haren 'yan…
Read More
Sojojin Isra’ila 462 da jami’an Mossad 32 ne suka mutu a kwanakin ukun farko na yaƙin Iran da Isra’ila

Sojojin Isra’ila 462 da jami’an Mossad 32 ne suka mutu a kwanakin ukun farko na yaƙin Iran da Isra’ila

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar leƙen asiri ta Rasha ta tabbatar da cewa Isra'ila ta rasa damar mallakar makamin nukiliya na Dimona, tare da asarar manyan masana kimiyyar nukiliya 11 a cikin kwanaki uku na farko bayan Iran ta mayar da martani. Rahoton ya kuma bayyana cewa a cikin wannan lokaci Isra'ila ta yi asarar janar-janar na rundunar sojin ƙasar (IDF) guda 6, da jami'an sojin sama 198. Kazalika, an ce sojoji 462 da kuma jami'an Mossad 32 sun mutu a cikin kwanaki uku na farkon mayar da martanin da Iran ta kai.
Read More
Iran da ƙasashen Musulunci: Abinda ya taɓa gira fa shi ne zai taɓa ido

Iran da ƙasashen Musulunci: Abinda ya taɓa gira fa shi ne zai taɓa ido

Daga AISHA ASAS A can kwanakin bayan a shafin Iyali mun taɓa darasi kan yadda rarabuwar kawuna a addini ya jefa Musulunci cikin halin da yake a yanzu. Inda a halin da muke ciki kowane ɓangare na kallon ɗaya a matsayin wanda ba muslmi ba. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ya rage ƙarfin Musulunci duk da tarin mabiya da yake da shi. Shafin ƙasashen Waje na wannan makon zai tattauna kan yaƙin Iran da yadda ƙasashen Musulunci suka koma gefe suna kallo yayin da wasu ke ganin hakan a matsayin daidai. Tun bayan juyin juya halin Musulunci na…
Read More
Kotu ta garƙame uwa da ’yarta kan satar manja

Kotu ta garƙame uwa da ’yarta kan satar manja

Wata kotun majistare da ke Ile-Ife a ranar Alhamis ta yanke wa wata mata da ’yarta hukuncin ɗaurin watanni shida kowacce, bisa samunsu da laifin satar manja. Waɗanda aka yanke wa hukuncin su ne Toyin Ojo mai shekaru 57 da Esther Ojo mai shekaru 23. Rundunar ’yan sanda ta gurfanar da su ne kan tuhume-tuhume biyu da suka haɗa da haɗa baki da kuma satar lita 25 na man gyaɗa da kuma lita 25 na manja. Dukkaninsu sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi bayan an karanta musu tuhumar a gaban kotu. Mai gabatar da kara, Sufeto Adesina Elijah,…
Read More