ukarofi

12639 Posts
Yadda waken soya ke rage tasirin tsufar fata

Yadda waken soya ke rage tasirin tsufar fata

Daga AISHA ASAS  Masu karatu ya ibada. Barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyarmu. Allah Ya karbi idabunmu. Idan Blueprint Manhaja ta makon da ya gabata ba ta wuce ku ba, za ku iya tuna mun faro bayyani kan irin tasirin da waken soya yake da fata da yadda yake taimakonta a yayin da ta shiga matsala ko take buƙatar taimako sakamakon gajiyawa ta shekaru.  Kuma mun sanar da ku irin sinadarai da yake cikin sa da yadda suke warkar da wasu matsaloli. A wannan makon za mu yi duba ne kan…
Read More
Kwanon maigida daban da na ‘yan gida (2)

Kwanon maigida daban da na ‘yan gida (2)

Daga AISHA ASAS Masu karatu idan ku na biye da mu, kun ji yadda baƙuwarmu ta koro bayani kan wannan darasi na mu, ta bayyana asali da kuma yadda wannan ɗabi'a ke tasiri ga tarbiyya da kuma dukiyarmu. A wannan satin za mu ba ta dama don ta kawo mana mafita kan wannan matsala, domin dai an ce babu damuwar da ba ta da magani, ko a hannun mutum ko ta wurin wanda ya yi mutum. SA'ADATU SAMINU KANKIA ce a shafin na iyali: Ta yaya kike ganin za a iya shawo kan wannan matsala? Abu ne mai sauƙi Hajiya…
Read More
Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da cibiyar kula da masu lalurar tarin-fuka a Rimi

Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da cibiyar kula da masu lalurar tarin-fuka a Rimi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Cibiyar TBL wadda gwamnatin jihar Katsina ta assasa ta a ƙaramar hukumar Rimi, domin duba masu lalaurar Tarin-Fuka, (Tuberculosis) tun daga matakin awon cutar, bayar da magani, aiki idan ta kama, da sauransu, za su zamo kyauta ga masu ɗauke da cutar, sannan kuma bayar da maganin a gare su, yana ɗaukar makonnin biyu zuwa shida. Dr. Muktar Aliyu shugaban yaƙi da cutar tarin-fuka ta jihar Katsina, ya bayyana jin daɗin game da ƙaddamar da cibiyar da gwamantin jihar Katsina ta yi, ya ƙara da cewa, samar da cibiyar zai samar ma al'ummar da ke…
Read More
‘Yan Shi’a sun zargi jami’an tsaro da yunƙurin kai masu hari a Katsina

‘Yan Shi’a sun zargi jami’an tsaro da yunƙurin kai masu hari a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A wata hira da manema labarai Shehu Usman Dalhatu Karkarku wanda yayi magana a madadin 'yan uwa mabiya Sayyid Ibrahim Zakzaky ya zargi jami'an sojoji da 'yan sanda da bibiyar su a yayin da suke gudanar da muzahara. Yace suna gudanar da muzahara ne domin nuna jimami, juyayi da damuwa kan kisan da aka yiwa Sayyid Ali Khamene'i da ƙasashen Amurka da Isra'ila suka aiwatar. "Sai muka ga gamayyar jami'an tsaron sojoji da 'yan sanda ɗauke da muggan makamai a motocin yaƙi masu sulke suna sintiri a cikin garin Katsina tun tsawon mako guda,"inji Dalhatu…
Read More
Sanata Yar’Adua ya raba tallafin shinkafar azumi a Katsina

Sanata Yar’Adua ya raba tallafin shinkafar azumi a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mutanen da suka amfani da tallafin sun fito daga ƙananan hukumomi 11 na shiyar Katsina da ke mazaɓar ɗan majalisar. Sanarwar ɗauke da sa hannun ɗaya daga cikin mataimaka na musamman kan yaɗa labarai malam Lawal Gwanda ya sanya, ƙungiyoyin 'yan siyasa, malama,masu unguwanni,mata da musu buƙata na musamman suka amfana da tallafin shinkafar da tuni aka raba. A jawabinsa Sanata Abdul'aziz Musa Yar'Adua wanda ya sami wakilcin Janaral Manajan na KASSAROMA, Manjo Yahaya Garba Rimi mai ritaya,yayi kira ga al'ummar mazaɓar sa da suyi amfani da wannan wannan wata mai alfarma su sanya jihar…
Read More
Mutuwa rigar kowa!

Mutuwa rigar kowa!

Assalam Alaikum. Da farko ina roƙon Allah Ya jiƙan dukkan muminai maza da mata da suka rasu tun daga zamanin Annabi Adam har zuwa yau. Mutuwa ƙarar kwana ce, domin kuwa, kowa da tanadin kwanakin da aka yi masa. Ke nan muna iya cewa, mutuwa riga ce da kowa sai ya sanya ta ko mai matsayi ko iko. Wannan ne ya sanya mutuwa ta kasance wa’adi da kowa ke jiran nasa. Saboda haka muna iya cewa mutuwa ƙa’ida ce da kowa sai ya cika, matuƙar an hura masa rai. Bisa irin wannan tunani ne waɗansu ke ganin mutuwa hutu ce…
Read More
Akwai Matsala!

Akwai Matsala!

Abinda iyayen yanzu suka ɗauka jin daɗin aure shi ne namiji ya ke kashewa ɗiyarsu kuɗi kafin ya aureta da bayan ya aureta. Wannan a wajensu shi ne so. kuma shi ne jin daɗin aure. Hakan ya sa su ma matan da yawa suka tafi akan wannan tsarin. Su kuma maza sai su ke amfani da wannan damar wajen cuta da gallazawa matan saboda ganin abin hannunsu su ke so ba ainahin su kansu ba a zallar asalin ɗan adamtaka. Shi ya sa a yanzu babu girmamawa ga wasu mazan ga surukansu. A da surukai kamar iyaye ne ana girmamasu…
Read More
POS: Tarihinsa da hukuncin amfani da shi wajen kasuwanci da fitar da kuɗaɗe da tura su

POS: Tarihinsa da hukuncin amfani da shi wajen kasuwanci da fitar da kuɗaɗe da tura su

Daga FARFESA AHMAD MURTALA Bismillahir rahmanir rahim. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga Annanbinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa bakiɗaya. Bayan haka, a yau Laraba 23 Jumada Ula, 1442 H.-06 Janairu, 2021 M., na sami tambaya ta fuskoki da yawa har sai da aka rubuto cewa: “Malam ana cikin bukatuwar yin cikakken bayani a dangane da POS. Wasu malaman sun haramta, wasu kuma sun halatta, Mun gode”. Wannan ita ce tambayar. Amma jin akwai wannan sabani na malamai a nan Kasar, ya sa na yi kamar ba zan bada amsa ba. Saboda ban cika son shiga irin mas’alolin…
Read More
Iran fa ta shirya yaƙi

Iran fa ta shirya yaƙi

Daga ALI ABUBAKAR SADIK Kusan duk abinda kasar Iran ta alƙawarta cewa za ta aiwatar matukar Amurka da Israila su ka kai mata hari, to a kwana na ukun wannan yaki babu Wanda ba ta aiwatar ba. Sun lashi takobi kaiwa duk kadarorin Amurka da ke Gabas ta tsakiya da Israila hari. Sannan za su rufe zirin mashigar Tekun Pasha, wato Straight of Hormuz. Zuwa yanzu sun kai hari a wurare 27 a kasashen Israila, Saudi Arabia, UAE, Kuwait, Bahrain, ƙatar, Jordan, Oman da sauransu. Sakamakon kashe Ayatollah Ali Khamenei, mutane da dama sun dauka Iran zata maida martani cikin…
Read More
Adalcin Gamji a fili ya ke har gobe

Adalcin Gamji a fili ya ke har gobe

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA  Wannan mako ga amsa ga wani matashi kan salon mulkin Sardauna da matashin ke da ra’ayin ba a yi adalci ba.  Shin Sardauna ya fifita wata kabila kan wata? Ina ganin kai na taɓa yi wa tambaya don sanin kai Bature ne ko Bahaushe don na ga ka maƙala hoton wani mai jan kunne mai ƙananan idanu sanye da hana sallah. Da farko zan ce wallahi ban lura da rubutun ka ba sai yanzu kuma gaskiya ka yi dogon rubutu ko da kuwa kwafi ka yi. Na karanta rubutun kakaf ga amsa ɗaya bayan ɗaya. 1.…
Read More