13
Mar
Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja Jami’an Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC), sun yi wa Babban Alƙalin Kotun Tarayya, Justice John Tsoho, tambayoyi na tsawon sa’o’i a ranar Talata kan wasu kuɗaɗen dalar Amurka 160,000 da aka gano a hannun matarsa. Rahotanni sun nuna cewa jami’an EFCC sun gayyaci alkalin ne domin yi masa tambayoyi dangane da kuɗin da aka ce an samu a hannun matarsa yayin wata tafiya da take yi. Wani rahoto da SaharaReporters ta wallafa ya ambato wata majiya daga EFCC na cewa an yi wa alƙalin tambayoyi na tsawon lokaci domin…
