ukarofi

12639 Posts
Na sa hannu kan dokar zaɓe ne don tserar da Nijeriya – Tinubu

Na sa hannu kan dokar zaɓe ne don tserar da Nijeriya – Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada ƙudurinsa na kare tsarin dimokuraɗiyya da bin doka a ƙasa, yana mai cewa aƙidar dimokuraɗiyya ita ce ginshiƙin rayuwarsa ta siyasa wadda za ta ci gaba da jagorantar dukkan matakansa a harkokin mulki. Shugaban ya kuma bayyana dalilin da ya sa ya amince da sanya hannu kan Dokar Zaɓe da aka yi wa kwaskwarima, inda ya buƙaci dukkan ‘yan siyasa da jam’iyyun ƙasa da su gudanar da harkokinsu cikin ƙa’idojin da doka ta tanada yayin fafatawa don neman muƙaman siyasa. An dai sha suka daga wasu ɓangarorin adawa…
Read More
2027: Lokacin Peter Obi bai yi ba amma mutumin kirki ne, inji Dino Melaye

2027: Lokacin Peter Obi bai yi ba amma mutumin kirki ne, inji Dino Melaye

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Tsohon Sanatan yankin Kogi ta Yamma a Majalisar Dattawa, Dino Melaye, ya bayyana cewa har yanzu lokaci bai yi ba da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, zai jagoranci Nijeriya a matsayin shugaban ƙasa. Melaye ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata hira da ya yi a tashar talbijin na Channels, inda ya yi bayani kan siyasar Nijeriya da kuma batun zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027. A yayin hirar, Melaye ya bayyana Obi a matsayin mutum nagari kuma ɗan Nijeriya mai kima, amma ya ce a ra’ayinsa, har yanzu bai kai lokacin…
Read More
Sanatoci tara sun koma ADC

Sanatoci tara sun koma ADC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu sanatoci tara na Majalisar Dattawan Nijeriya sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyunsu na siyasa zuwa ADC, lamarin da ya zama zaya daga cikin manyan sauye-sauyen siyasa da aka gani a majalisar a ‘yan watannin baya-bayan nan. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da hakan a zaman majalisar na ranar Alhamis bayan karanta wasiƙun da sanatocin suka aike, inda suka sanar da majalisar shawarar barin jam’iyyunsu na baya. Sanatocin da suka fice sun haɗa da Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato ta Kudu), Mohammed Ogoshi Onawo (Nasarawa ta Kudu), Binos Dauda Yaroe (Adamawa ta Kudu), Austin…
Read More
Shugaban PDP na Zamfara ya koma APC

Shugaban PDP na Zamfara ya koma APC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, Dokta Jamil Jibo Magayaki, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa APC. Dokta Jamil ya koma jam’iyyar mai mulki ne bayan komawar Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, APC. A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, tsohon shugaban PDP na jihar, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bisa halin da siyasa ta ke ciki a Jihar Zamfara. Sanarwar ta ce, “Ni, Dakta Jamil Jibo Magayaki, shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, ina sanar da ku a hukumance cewa na koma jam’iyyar APC.” Ya ƙara da…
Read More
Kisan Ayatollah: Ba makawa sai mun ɗauki fansa – Iran

Kisan Ayatollah: Ba makawa sai mun ɗauki fansa – Iran

*An yi mana kisan ƙare dangi, inji Mojtaba Khamenei *Amurka ta kashe Dala biliyan 11 a kwana shida na yaƙin Iran Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya ce, Iran za ta ɗauki fansar mutanenta da aka kashe, ciki har da yara da ɗaliban makarantar Minab, baya ga jagoran addini, Ayatollah Khamenei da aka kashe a farkon yaƙinta da Amurka da kuma Isra’ila. Ya bayyana hakan ne a sanarwarsa ta farko da ya fitar tun bayan da aka naɗa shi a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar wanda gidan talabijin gwamnatin ƙasar ta karanto. "Dole…
Read More
Haɗin gwiwar yaɗa labarai zai ƙarfafa daidaiton tsaron ƙasa – Idris

Haɗin gwiwar yaɗa labarai zai ƙarfafa daidaiton tsaron ƙasa – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce kafa tsarin yaɗa labarai na haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatu da kuma dabaru zai taimaka ƙwarai wajen ƙarfafa daidaiton ayyukan tsaro a ƙasar nan. Ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya kai ziyarar aiki ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo. Idris ya ce: “Gwamnatin Tarayya ta yi imanin cewa ta hanyar mu’amala tsakanin ma’aikatu da sassa daban-daban na gwamnati, za a iya samar da tsarin sadarwa na haɗin gwiwa wanda zai ƙarfafa daidaita matakan tsaro a yaƙin da ake yi…
Read More
Bauchi: An yi nasarar inganta noman doya da dankali babu takin zamani

Bauchi: An yi nasarar inganta noman doya da dankali babu takin zamani

Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi Shugaban kamfanin Golbokki ɓentures Limited, Alhaji Aminu Barau Liman Katagum, ya bayyana cewa kamfanin ya samu nasarar inganta fasahar noman doya da dankalin Hausa da na Turawa ba tare da amfani da takin zamani ba. Alhaji Aminu Barau ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a ofishinsa da ke unguwa masana’antu a kan hanyar Dumi a Bauchi, inda ya ce nasarar ta samu ne bayan dogon bincike da kamfanin ya gudanar domin bunkasa harkar noma a Nijeriya. Ya ce kamfanin Golbokki ɓentures Limited na ci gaba da gudanar da bincike tare da…
Read More
CP Bello Shehu ya zama mataimakin sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya

CP Bello Shehu ya zama mataimakin sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar Kula da ayyukan 'yan sandan Najeriya PSC ta ɗaga muƙamin kwamishinan 'yan sanda na Jihar Katsina, CP Bello Shehu zuwa mataimakin sufeto janar na yan sandan Najeriya (Assistant Inspector General Of Police AIG) . CP Bello Shehu ɗan asalin garin Dukku ne a jihar Gombe, wanda ya shafe kusan shekara ɗaya a matsayin kwamishinan ƴan sanda a jihar Katsina.
Read More
Sarki Aminu Ado ya sanar da ’yan sanda shirin gudanar da hawan salla a Kano

Sarki Aminu Ado ya sanar da ’yan sanda shirin gudanar da hawan salla a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja   Fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ta sanar da rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, cewa ta fara shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Hawan Salla idan an kammala azumin watan Ramadan. Wannan na cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 7 ga watan Maris, 2026, wadda aka aike wa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori. Fadar ta ce za a gudanar da bukukuwan hawan sallar daga fadar sarkin da ke unguwar Nassarawa a Kano. Sakataren Sarkin, Abdullahi Haruna Kwaru ne, ya sanya wa wasiƙar hannu, inda ya ce Sarkin da mambobin majalisar…
Read More
Namadi Dala ya yaba da yadda aka samar da sabbin shugabannin APC a Kano

Namadi Dala ya yaba da yadda aka samar da sabbin shugabannin APC a Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMADU a Kano Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Kano kuma tsohon Kwamishinan Sufuri, Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda aka gudanar da zaɓen sabbin shugabannin jam’iyyar a jihar. Namadi Dala ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, inda ya ce zaɓen da aka gudanar wanda ya samar da sabon shugabanci ƙarƙashin Hon. Umar Haruna Doguwa ya gudana cikin fahimtar juna, haɗin kai da kuma kwanciyar hankali. Ya taya dukkan sabbin shugabannin jam’iyyar da aka zaɓa daga matakin mazaɓu zuwa ƙananan hukumomi da kuma matakin jiha murna,…
Read More