ukarofi

12639 Posts
Kotu ta yanke masa hukuncin kisa kan kashe tsohuwar matarsa a Gombe

Kotu ta yanke masa hukuncin kisa kan kashe tsohuwar matarsa a Gombe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babbar Kotun Jihar Gombe, ta yanke wa wani matashi mai shekaru 25, Hassan Mohammed, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin kashe tsohuwar matarsa, Halima Sadiya Adamu. Hassan Mohammed ɗan asalin ƙauyen Falangaya ne, da ke ƙaramar Hukumar Dukku a Jihar Gombe. Mai shari’a Abdulhamid Mohammed Yakubu na Babbar Kotun Jihar Gombe mai lamba ta biyu ne, ya yanke hukuncin bayan kotun ta tabbatar da laifin kisan. Kotun ta ce laifin ya saɓa da sashe na 221 na Dokar Penal Code. A cewar ɓangaren gwamnati, lamarin ya faru ne a…
Read More
Majalisa ta amince da ɗaurin shekara biyu ga wanda aka samu cikin jam’iyya sama da ɗaya

Majalisa ta amince da ɗaurin shekara biyu ga wanda aka samu cikin jam’iyya sama da ɗaya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar Wakilai ta yi gyara sashe na 77 na sabuwar Dokar Zaɓe ta 2026, inda ta tanadi hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari ko biyan tarar Naira miliyan 10 ga duk wanda aka samu cikin jam’iyyun siyasa biyu a lokaci guda. Manhaja ta ruwaito cewa ’yan majalisar sun yi wannan gyara ne bayan muhawara mai zafi, inda suka ƙara yin gyara a sashe na 8, 9 da kuma 10 a cikin dokar. Sabon sashe na 8 ya bayyana cewa duk wanda aka samu a cikin jam’iyyu biyu a lokaci guda ba za a…
Read More
Sojoji sun ragargaza motocin yaƙin ’yan ta’adda a dajin Sambisa

Sojoji sun ragargaza motocin yaƙin ’yan ta’adda a dajin Sambisa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta kai wani farmaki ta sama cikin dajin Sambisa, inda ta lalata motocin yaƙi guda hudu tare da wasu muhimman kayayyakin aiki na ’yan ta’adda. Rundunar sojin saman ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis, tana mai cewa an gudanar da harin ne a ranar Laraba, 11 ga Maris, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma sa ido na tsawon lokaci kan ayyukan ’yan ta’adda a yankin. Daraktan Hulɗa da Jama’a da Watsa Labarai na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an aiwatar da harin cikin kwarewa, wanda…
Read More
Birtaniya ta ƙaƙaba takunkumin samaniya da taƙaita zirga-zirga gabanin ziyarar Tinubu

Birtaniya ta ƙaƙaba takunkumin samaniya da taƙaita zirga-zirga gabanin ziyarar Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja Gwamnatin ƙasar Birtaniya ta sanar da ƙaƙaba takunkumi kan sararin samaniya da wasu hanyoyi a garin Windsor gabanin ziyarar aiki da Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai kai ƙasar a mako mai zuwa. ’Yan sandan Thames Valley sun bayyana cewa, matakin na daga cikin tsauraran matakan tsaro da ake ɗauka, domin tabbatar da tsaron manyan baƙi a ƙasar, masu kallo da sauran jama’a yayin ziyarar Shugaban ƙasa Tinubu. A cikin wata sanarwa, jami’in rundunar Thames Valley Police Joint Operations Unit, Chief Superintendent Adrian Hall, ya ce takunkumin sararin samaniya wani ɓangare ne kawai na manyan…
Read More
Fadar Vatican ta kori bishop bisa satar kuɗi da halartar gidan karuwai

Fadar Vatican ta kori bishop bisa satar kuɗi da halartar gidan karuwai

Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja Fadar Vatican ta sallami wani bishop ɗan ƙasar Amurka, Emanuel Hana Shaleta, bayan ya miƙa takardar murabus ɗinsa sakamakon zarge-zargen satar kuɗaɗe da kuma halartar wuraren karuwai a ƙasar Meɗico. Rahotanni sun bayyana cewa an zargi bishop ɗin da satar sama da dala 250,000 daga kuɗaɗen cocin da yake jagoranta, tare da zargin cewa yana yawan zuwa wani gidan karuwai da ke Mexico. Vatican ta sanar da amincewa da murabus ɗin nasa a ranar Talata, inda Paparoma Pope Leo XIV ya karɓi murabus ɗin daga muƙaminsa na jagorantar Eparchy of Saint Peter the Apostle of…
Read More
Ramadan: Abba Minista ya tallafa wa malamai da limamai 1,000 da kayan abinci 

Ramadan: Abba Minista ya tallafa wa malamai da limamai 1,000 da kayan abinci 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shahararren mai taimakon jama’a, Alhaji Abba Minista, ya raba kayan abinci ga kimanin malaman addinin Musulunci da limamai 1,000, domin tallafa musu a wannan lokaci na watan azumin Ramadan tare da rage musu raɗaɗin halin ƙuncin da ake ciki. An gudanar da rabon tallafin ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin Alhaji Abba Minista na ci gaba da tallafa wa marasa ƙarfi da sauran sassan al’umma masu buƙatar taimako. Malaman addini da limaman da suka amfana da tallafin, waɗanda suka fito daga sassa daban-daban na al’umma, sun nuna matuƙar godiyarsu kan wannan taimako da…
Read More
Ministan Tsaro ya gargaɗi kafafen yaɗa labarai kan yaɗa farfagandar ’yan ta’adda

Ministan Tsaro ya gargaɗi kafafen yaɗa labarai kan yaɗa farfagandar ’yan ta’adda

Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja Ministan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, ya buƙaci kafafen yadlɗa labarai a faɗin ƙasar nan da su riƙa nuna ƙwarewa da tsantsar gaskiya a rahotanninsu, tare da kauce wa yaɗa farfagandar ’yan ta’adda da ka iya raunana gwiwar sojoji ko ba wa masu aikata laifi ƙwarin gwiwa. Musa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai bayan wata muhimmiyar ganawa da shugabannin rundunonin sojin ƙasar domin duba yadda ake gudanar da ayyukan tsaro a sassa daban-daban na ƙasar. Taron ya haɗa da Babban Hafsan Tsaro da…
Read More
Sanatocin PDP a Majalisar Dattawa sun ragu zuwa 14, APC ta ƙaru zuwa 84

Sanatocin PDP a Majalisar Dattawa sun ragu zuwa 14, APC ta ƙaru zuwa 84

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ƙaruwar sauya sheƙa da yake girgiza jam’iyyar PDP gabanin babban zaɓen shekarar 2027 ya sake bayyana a Majalisar Dattawan Nijeriya, inda wasu sanatoci uku suka fice daga jam’iyyar suka koma jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar. Sanatocin da suka sauya sheƙa sun haɗa da Amos Yunana mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Aminu Iya Abbas mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya da kuma Ikra Aliyu Bilbis mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya. An karanta wasiƙun sauya jam’iyyarsu ne a zaman majalisa na ranar Laraba. Sauya sheƙar sanatocin guda uku ya zo ne kwana guda bayan da Sanata Banigo Ipalibo, mai…
Read More
Gwamna Yusuf ya gargaɗi mambobin majalisar zartarwa kan rashin aminci

Gwamna Yusuf ya gargaɗi mambobin majalisar zartarwa kan rashin aminci

Daga RABIU SANUSI Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi mambobin majalisar zartarwa ta Jihar da su guji rashin aminci ƙasa ta cikin gida da kuma fitar da bayanan sirrin gwamnati yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta ci gaba da lamuntar irin waɗannan halaye ba. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu a ranar Alhamis. Gwamnan ya yi wannan gargaɗi ne yayin taron majalisar zartarwa karo na 38 inda ya buƙaci mambobin majalisar su kasance masu haɗin kai tare da sadaukar da kai ga manufofin…
Read More
Hajiya Hauwa ta roƙi gwamnatin Gombe ta buɗe tashar Daɗin Kowa

Hajiya Hauwa ta roƙi gwamnatin Gombe ta buɗe tashar Daɗin Kowa

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Wata ‘yar kasuwa mai sayar da abinci a tashar motar Daɗin Kowa da ke garin Gombe, Hajiya Hauwa Inuwa, ta roƙi gwamnatin jihar da ta sake buɗe tashar, tana mai cewa rufe ta na tsawon lokaci ya jefa ‘yan kasuwa da direbobi cikin matsananciyar wahala. Hajiya Hauwa, wacce ta shafe shekaru tana gudanar da sana’ar sayar da abinci a tashar, ta ce rufe tashar na kusan watanni goma ya kawo koma baya mai yawa ga rayuwar iyalai da dama da ke dogaro da harkokin da ake yi a wurin domin samun abin dogaro. Ta bayyana…
Read More