13
Mar
Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya taya wasu ‘yan jihar biyu, Bello Shehu da Dankombo Morris Fallings, murna kan ɗaga su zuwa muƙamin mataimakan babban sufeton ‘yan sanda ta Najeriya. A cikin saƙon taya murna da aka fitar ranar Jumma’a ta bakin darakta janar na harkokin yaɗa labarai na fadar gwamnati, Isma’ila Uba Misilli, gwamnan ya bayyana cewa wannan ɗaga muƙamin ya nuna yabo ne ga shekaru da suka shafe suna aiki tuƙuru, ƙwarewa da hidimar da suka bayar a cikin rundunar ‘yan sanda. Gwamnan ya ce wannan ɗaga muƙamin na nuna irin…
