ukarofi

12636 Posts
Gwamna Bago ya umarci masu muƙaman siyasa da ke son tsaya takara su ajiye aiki

Gwamna Bago ya umarci masu muƙaman siyasa da ke son tsaya takara su ajiye aiki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin jihar Neja ya bai wa masu riƙe da mukaman siyasa da masu riƙe da ofisoshin gwamnatin da ke tunanin tsayawa takara a zaben 2027 da su ajiye aikinsu kafin ko a ranar 23 ga watan Maris ɗin 2026. Ko’odinetan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar Neja, Lawal Tanko, ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi a ranar Lahadi, inda ya kafa hujja da fitar da jadawalin zaɓe da hukumar INEC ta yi. A cewar jawabin da sakataren gwamnatin jihar (SSG) ya fitar, Abubakar Usman, ya ce, umarnin ya zama dole domin…
Read More
Modu Mustapha ya yaba wa Gwamna Zulum kan ayyukan raya ƙasa

Modu Mustapha ya yaba wa Gwamna Zulum kan ayyukan raya ƙasa

Daga GAMBO ISA a Abuja Sakataren Dindindin na Ma’aikatar ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu ta Jihar Borno, Alhaji Modu Mustapha, ya yaba wa Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Baba Gana Umara Zulum, bisa ƙoƙarinsa na ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da kuma inganta shugabanci mai haɗa kan al’umma a faɗin jihar. Modu Mustapha ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar, wadda aka rabawa jaridar Blueprint Manhaja, inda ya kuma nuna godiyarsa ga gwamnan bisa naɗin da ya yi masa a matsayin sakataren dindindin a ma’aikatar. A cewarsa, gwamnatin Zulum ta samu gagarumin ci…
Read More
Mu muka ceci Nijeriya daga durƙushewa – Tinubu

Mu muka ceci Nijeriya daga durƙushewa – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar Litinin ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa ƙasar nan ba za ta lamunci duk wani abu da zai yi barazana ga zaman lafiya da haɗin kan Najeriya ba. Shugaba Tinubu ya ba da wannan tabbaci ne a lokacin da yake shan ruwa da shugabannin addini da sarakuna a fadar gwamnati a Abuja, inda ya yaba da irin rawar da suke takawa wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali da kyawawan halaye a tsakanin al’umma. “Tabbas muna fuskantar ƙalubale. ‘Yan ta’adda suna cikin wani hali saboda ana kai musu…
Read More
Manoma da makiyaya a Roni sun buƙaci tallafin gwamnati don bunƙasa noman rani

Manoma da makiyaya a Roni sun buƙaci tallafin gwamnati don bunƙasa noman rani

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano Wasu manoma da makiyaya da ke gudanar da harkokin noman rani da kiwo a yankin ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa sun buƙaci Majalisar ƙaramar Hukumar da gwamnatin jihar da su ɗauki matakan bunƙasa harkokin noma da samar da ababen more rayuwa domin inganta rayuwar al’ummar yankin. Buƙatar ta fito ne daga bakin wani manomi kuma mai kiwo a yankin, Malam Nura Bala, wanda ya yi magana a madadin manoma ‘yan asalin yankin Roni. Malam Nura Bala ya yi kira ga Majalisar ƙaramar Hukumar Roni karkashin jagorancin Shugaban ƙaramar Hukumar, Hon. Abba Ya’u, tare…
Read More
Amurka ta gargaɗi ‘yan ƙasarta kan yiwuwar hari a ofishin jakandancin ƙasar a Nijeriya

Amurka ta gargaɗi ‘yan ƙasarta kan yiwuwar hari a ofishin jakandancin ƙasar a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ofishin jakadancin Amurka da ke Nijeriya ya fitar da sanarwar tsaro inda ya gargaɗi ‘yan kasarsa kan yiwuwar harin ta’addanci da ka iya shafar cibiyoyinta da kuma makarantu masu alaka da ƙasar a fadin Nijeriya. A sanarwar da ofishin jakadancin da ke Abuja ya fitar, an buƙaci ‘yan Amurka su ƙara yin taka-tsantsan idan za su ziyarci ofisoshin diflomasiyyar Amurka ko kuma cibiyoyin da ke da alaƙa da ƙasar. Sanarwar ta ambaci ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Legas, inda aka buƙaci ‘yan ƙasar su kasance cikin…
Read More
ICPC ta gano kadarori na biliyoyin naira da ake zargin suna da alaƙa da El-Rufai a Misra 

ICPC ta gano kadarori na biliyoyin naira da ake zargin suna da alaƙa da El-Rufai a Misra 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Masu bincike na hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC, sun gano wasu kadarori masu darajar biliyoyin naira a ƙasar Egypt da ake zargin suna da alaƙa da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a cewar wasu jami’ai da ke da masaniya kan binciken kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito. Majiyoyi a cikin hukumar sun ce an sayi kadarorin ne tsakanin shekarun 2021 zuwa 2023. Wasu majiyoyi daga cikin jami’an hukumar, waɗanda suka buƙaci a sakaya sunayensu saboda ba su da izinin yin magana a bainar jama’a, sun bayyana cewa kadarorin…
Read More
Peter Obi ya koka bisa ƙaruwar matsalar rashin tsaro a Nijeriya 

Peter Obi ya koka bisa ƙaruwar matsalar rashin tsaro a Nijeriya 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour Party a zaɓen shekarar 2023, Peter Obi, ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a Nijeriya, yana cewa ƙasar ta shiga wani yanayi mai matuƙar muni sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda a sassa daban-daban. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na ɗ a safiyar Litinin, Obi ya ce hare-haren sun yi ƙamari matuƙa, inda al’ummomi da dama ke fuskantar farmaki akai-akai, yayin da shugabanni ke ci gaba da yin shiru kan lamarin. Ya bayar da misali da wani hari da aka…
Read More
Sojoji sun kashe ƙasurgumin ɗan binidiga Alti, da ya shahara a Tiktok 

Sojoji sun kashe ƙasurgumin ɗan binidiga Alti, da ya shahara a Tiktok 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dakarun Sojin Nijeriya sun kashe wani ƙasurgumin kwamandan ‘yan bindiga da aka fi sani da Alti, wanda ake zargi da addabar yankunan da ke kan hanyar Gusau zuwa Funtua da sauran yankunan Arewa maso Yammacin Nijeriya. Wata majiya daga hedikwatar sojoji ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) cewa an kashe Alti ne a wani samame na soji da aka kai kwanan nan, lamarin da ake ganin babbar illa ce ga ƙungiyoyin ‘yanbindiga a jihohin Zamfara da Katsina da kuma wasu sassan jihar Sokoto. Rahotanni sun nuna cewa duk da ƙarancin shekarunsa,…
Read More
Sojoji sun daƙile harin ‘yan ta’adda a Gadar Azir da Banki

Sojoji sun daƙile harin ‘yan ta’adda a Gadar Azir da Banki

Daga USMAN KAROFI Sojojin rundunar haɗin gwiwa na Operation Haɗin Kai a yankin Arewa maso Gabas sun daƙile wani yunƙurin harin ta’addanci da aka kai kan sansanonin sojoji a Azir Bridge da kuma Banki da safiyar Juma’a, 13 ga Maris, 2026. Rundunar ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai farmakin ne da nufin ƙwace sansanin, amma sojoji sun yi gaggawar tunkararsu. A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar, sojojin sun nuna ƙwarewa da shirin yaƙi inda suka ƙaddamar da hare-haren daƙile farmaki wanda ya tarwatsa tsarin ’yan ta’addan tare da tilasta…
Read More
Burinmu mu mayar da Kaduna cibiyar noma da kiwo a Arewa — Uba Sani

Burinmu mu mayar da Kaduna cibiyar noma da kiwo a Arewa — Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa babban burin gwamnatinsa shi ne mayar da jihar cibiyar noma da kiwo mafi girma a Arewacin Nijeriya. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani shiri da gwamnatinsa ta gudanar na raba tallafi ga ƙungiyoyin manoma kusan 5,000 a sassa daban-daban na jihar domin ƙarfafa harkar noma da kiwo. Uba Sani ya ce tallafin da aka bayar zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona, inganta kiwo, da kuma samar da ayyukan yi ga dubban matasa da manoma a karkara. Ya ƙara da cewa matakin wani ɓangare ne na dabarun gwamnatinsa na bunƙasa tattalin…
Read More