ukarofi

12636 Posts
Gwamna Raɗɗa ya buɗe masallacin Juma’a da mataimakinsa ya gina a Ƙanƙara

Gwamna Raɗɗa ya buɗe masallacin Juma’a da mataimakinsa ya gina a Ƙanƙara

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya ƙaddamar da buɗe sabon katafaren masallacin Juma’a da mataimakin gwamnan Jihar, Hon. Faruk Lawal Joɓe, ya gina a garin Ƙanƙara. Ranar juma'a da ta gabata gwamnan ya samu wakilcin sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari ya buɗe masallacin. Masallacin, wanda aka gina a fili mai tsawon mita 200 da faɗin mita 200, an yi shi da tsarin gine-ginen zamani tare da kyawawan kayayyakin ƙawa. Haka kuma, masallacin yana da sashi na musamman domin mata. Taron buɗe masallacin ya samu halartar manyan baƙi daga ciki da wajen Jihar Katsina,…
Read More
Gwamnatin Katsina ta raba kayayyakin inganta karatun ɗaliban makarantar makafi

Gwamnatin Katsina ta raba kayayyakin inganta karatun ɗaliban makarantar makafi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A wani taro da aka gudanar a makarantar makafi a Katsina, an rabawa ɗalibai kayayyakin karatu da gwamnati ta samar domin tallafa musu wajen samun ingantaccen ilimi. Kayayyakin da aka raba sun haɗa da katifu, rigunan karatu, takardun A4 da kuma kayan karatun Braille, waɗanda aka tanada domin taimaka wa ɗaliban da ke da buƙata ta musamman su samu damar cigaba da karatunsu cikin sauƙi. A yayin taron, da yake jawabi, sarkin makafi, Alhaji Garba Nahuta, ya bayyana godiya ga Gwamnan jihar malam Dikko Raɗɗa bisa wannan tallafi da ya samar domin inganta harkar ilimi…
Read More
Yadda aka kashe Naira biliyan biyar wajen sauya sunan NNPC zuwa NNPCL – Sanata Wadada

Yadda aka kashe Naira biliyan biyar wajen sauya sunan NNPC zuwa NNPCL – Sanata Wadada

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a ya gayyaci tsofaffin shugabannin Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPCL), ciki har da tsohon Babban Darakta na rukunin kamfanin, Mele Kyari, domin amsa tambayoyi kan wani zargin giɓin kuɗi da ya kai kimanin Naira tiriliyan 210 a cikin rahotannin kuɗaɗen kamfanin da aka tantance daga shekarar 2017 zuwa 2023. Shugaban kwamitin kuma Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma, Sanata Aliyu Wadada, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a harabar Majalisar Dokoki da ke Abuja. Sanatan ya ce, kwamitin ya fara wannan bincike ne a ƙarƙashin ikon…
Read More
Gyare-gyaren da na yi a rundunar ’yan sanda ne suka jawo mini tsana – Egbetokun

Gyare-gyaren da na yi a rundunar ’yan sanda ne suka jawo mini tsana – Egbetokun

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa hare-haren da kafafen yaɗa labarai suka riƙa kai wa jagorancinsa a lokacin da yake kan shugabanci ba su kasance na bazata ba, sai dai wani shiri ne da wasu masu ruwa da tsaki masu ƙarfi suka ƙulla domin su daƙile gyare-gyaren da ya kawo a rundunar ’yan sanda. A wani cikakken bayani da ya yi kan lokacin da yake jagorantar Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, Egbetokun ya ce shugabancinsa ya fuskanci ƙalubale da dama wajen kawar da wasu tsofaffin halaye marasa kyau da suka…
Read More
Kananan tashoshin lantarki za su magance matsalar lantarki a Nijeriya – Shugaban REA

Kananan tashoshin lantarki za su magance matsalar lantarki a Nijeriya – Shugaban REA

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara ta Tarayya (REA), Dr. Abba Aliyu, ya bayyana cewa sabon tsarin girke ƙananan tashoshin samar da wutar lantarki da hukumar ke yi a sassa daban-daban na ƙasar nan zai taimaka matuƙa wajen shawo kan matsalolin da suka daɗe suna addabar tsarin babbar hanyar wutar lantarki ta ƙasa. A wata hira da ya yi kwanan nan, Dr. Aliyu ya ce hukumar ta fara aiwatar da sabon tsarin girke mini-grids, wato ƙananan cibiyoyin samar da wuta masu zaman kansu, kai tsaye a cikin ƙauyuka da al’ummomin da ke nesa da…
Read More
Yadda matashiya mai sikila ta rasu shekara guda bayan kammala digiri

Yadda matashiya mai sikila ta rasu shekara guda bayan kammala digiri

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata matashiya ’yar Nijeriya kuma mai fafutukar wayar da kai kan cutar sikila, Anisa Ishaƙ-Balogun, ta rasu shekara guda kacal bayan ta kammala karatun digiri na farko da sakamako mafi girma a jami’a. Marigayiyar, wacce aka fi sani da sunan @Nerdy_neesah a dandalin sada zumunta na ɗ, ta rasu ne ranar Laraba bayan shafe shekaru tana fama da cutar Sikila. Rahotanni sun nuna cewa marigayiyar ta kasance mai jajircewa wajen karatu duk da ƙalubalen rashin lafiya da take fuskanta. A shekarar 2025, ta kammala karatun digiri na farko a fannin Cell Biology and Genetics daga Jami'ar…
Read More
Ba mu da alhakin rashin tura masu HND zuwa NYSC – JAMB

Ba mu da alhakin rashin tura masu HND zuwa NYSC – JAMB

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta sake jaddada cewa, ba ita ce ke da alhakin shigar ɗalibai zuwa karatun Babbar Difloma ta HND ba, haka nan kuma ba ita ce ke da alhakin matsalolin da suke hana wasu masu wannan shaidar takardar samun damar shiga shirin hidimtawa ƙasa na NYSC ba. Shugaban hukumar, Is-haƙ Oloyede, ne ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar ɗaliban Kwalejojin Kimiyya (NAPS) a ofishinsa, inda suka je domin tattaunawa kan matsalolin da ke addabar wasu ɗaliban kwalejojin kimiyya, musamman dangane da rashin samun damar shiga NYSC…
Read More
Don al’umma zan tsaya takara, ba don ƙalubalantar Fintiri ba – Buba Kwacham

Don al’umma zan tsaya takara, ba don ƙalubalantar Fintiri ba – Buba Kwacham

Daga AISHA ASAS Alhaji Abdulrahaman Buba Kwacham ba baƙon suna ne a kafafen yaɗa labarai ba, kasancewarsa gogaggen ɗan siyasa kuma jigo a Jam'iyyar APC, musamman a Jihar Adamawa da Arewa bakiɗaya. Shine Sarkin Fulanin Mubi kuma Shugaban ƙungiyar ‘Movement for North East’. A ’yan kwanakin nan ne aka samu cece-kucen siyasa tsakaninsa da Gwaman Jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Fintiri, wanda kwanan nan ya canza sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC, inda ya yi wasu maganganu da ake hasashen ya yi su ne akan Hon. Buba Kwacham. Da wannan ne Hon. Kwacham ya tattauna da Blueprint Manhaja, don fahimtar da al'umma…
Read More
Haka ‘yan adawa za su ci gaba da zama cikin ruɗu har a gama zaɓen 2027 – Akpabio ga PDP, LP

Haka ‘yan adawa za su ci gaba da zama cikin ruɗu har a gama zaɓen 2027 – Akpabio ga PDP, LP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Asabar ya yi wa ‘yan jam’iyyar adawa shaguɓe tare da bayyana su a matsayin waɗanda ba su shirya wa zaɓe ba. Ya kuma yaba wa shugaba Tinubu da jam’iyyar APC kam yadda ta mamaye ko’ina. Akpabio ya yi wannan kalamai ne a yayin filin wasan Godswill Akpabio da ke Uyo a jihar Akwa Ibom a lokacin wani taro da uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta halarta albarkacin ranar mata ta duniya ta 2026. A yayin da yake jawabi, shugaban majalisar ya ce ‘yan jam’iyyar adawa kansu na…
Read More
Harƙallar biliyan N4.65: Kotu ta hana Kwamishinan Kuɗi na Bauchi izinin zuwa aikin Hajji

Harƙallar biliyan N4.65: Kotu ta hana Kwamishinan Kuɗi na Bauchi izinin zuwa aikin Hajji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da bukatar Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, na neman izinin tafiya zuwa Makka a ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji. Mai shari’a Emeka Nwite ya yanke hukuncin ne a ranar Litinin, inda ya ce wanda ake tuhuma da laifin harkallar kuɗi har Naira biliyan 4.65 bai gabatar da isassun hujjoji a gaban kotu da za su tabbatar da bukatar tafiyar ba. A hukuncin da Manhaja ta tabbatar a ranar Talata, alƙalin ya goyi bayan ƙorafin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da…
Read More