ukarofi

12636 Posts
Nauyin bashi na ci gaba da matsin lamba ga tattalin arzikin Nijeriya – Rahoto

Nauyin bashi na ci gaba da matsin lamba ga tattalin arzikin Nijeriya – Rahoto

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matsin tattalin arziƙi na ci gaba da ƙara tsananta wa Nijeriya yayin da kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke kashewa wajen biyan bashin ƙasa suka zarce kuɗin da ake warewa domin ayyukan raya ƙasa da kimanin Naira tiriliyan 3.9 a cikin shekaru biyu da suka gabata. Rahoton bayani da jaridar News Point Nigeria ta samu daga Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta kashe jimillar Naira tiriliyan 27.2 wajen biyan bashi tsakanin shekarun 2024 da 2025. Wannan na nuni da yadda nauyin bashi ke ƙara danna tattalin arzikin ƙasar. Takardar bayanin, wadda Mai Ba…
Read More
Annobar tsutsa na barazana ga noman tumatiri a Kano, inji manoma rani

Annobar tsutsa na barazana ga noman tumatiri a Kano, inji manoma rani

Daga DAUDA USMAN Kungiyar Manoman Rani a jihar Kano ta bayyana damuwarta kan wata annoba ta tsutsa mai suna Sharon wadda ke lalata gonakin tumatiri, lamarin da ke janyo asarar maƙudan kuɗi ga manoma a duk shekara. Shugabannin ƙungiyar sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta gaggauta ɗaukar mataki domin nemo maganin da zai kawo ƙarshen wannan matsala. Shugabannin ƙungiyar manoman rani ta ƙasa da kuma na reshen jihar Kano da ke yankin kasuwar ‘Yan Gwari ta Kwanar Gafan a ƙaramar hukumar Garun Malam ne suka bayyana haka yayin wani taron ƙungiyar da aka gudanar a Kano ranar…
Read More
Kwara: Kungiyar Ci Gaban Shiya ta kai ƙorafi hukumar NHRC kan zaɓen sarauta

Kwara: Kungiyar Ci Gaban Shiya ta kai ƙorafi hukumar NHRC kan zaɓen sarauta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Ci Gaban Shiya ta aike da takardar koke ga Hukumar Kare Haƙƙin ɗan Adama (NHRC) a Abuja, tana neman shiga tsakani kan yadda aka gudanar da zaben sarautar Shiya da ta ce bai bai wa zaɓin jama’a adalci ba. A cikin takardar koken da ƙungiyar ta rubuta, ta bayyana cewa al’ummar Shiya da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Baruten a jihar Kwara sun fara tsarin zaɓen sabon shugaban gargajiya ne bayan samuwar gibi a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2024. Sai dai ƙungiyar ta ce tsarin ya kasance cike da kura-kurai, nuna ɓangaranci da kuma tsoma…
Read More
Rashin tsaro barazana ce ga tattalin arzikin Arewa — NYEEF

Rashin tsaro barazana ce ga tattalin arzikin Arewa — NYEEF

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar ƙarfafa Matasan Arewa da Wayar Musu da Kai, wato Northern Youth Empowerment & Enlightenment Forum (NYEEF), ta fitar da wata muhimmiyar sanarwar manufofi bayan kammala Taron Tattaunawa na Shekara karo na uku da ta gudanar a watan Janairun 2026 a jihar Kaduna. Taron, wanda aka shirya domin karrama marigayi Alhaji Suleiman Abubakar Uban Doman Gudu, tsohon Daraktan Harkokin Sarauta na ƙungiyar, ya haɗa manyan malamai, shugabannin addini, kwararrun harkokin tsaro, masu tsara manufofi, shugabannin matasa da kuma ‘yan jarida domin nazarin manyan matsalolin da ke addabar Arewacin Nijeriya da ma kasa baki ɗaya. A sanarwar…
Read More
Yara miliyan 6.4 na fama matsanancin rashin abinci a Arewacin Nijeriya — ICRC

Yara miliyan 6.4 na fama matsanancin rashin abinci a Arewacin Nijeriya — ICRC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ƙungiyar Bayar da Agaji ta Duniya, wato International Committee of the Red Cross (ICRC), ta bayyana damuwa kan ƙaruwar matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara a yankunan da ke fama da rikici a Arewacin Nijeriya. ƙungiyar ta ce, kimanin yara miliyan 6.4 ’yan ƙasa da shekara biyar a yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ne ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki. A cewar ƙungiyar, rikicin da aka shafe kusan shekara 15 ana yi ya lalata rayuwar jama’a, noma da samar da abinci, wanda ya sa…
Read More
Wane zaɓi ya rage wa PDP gabanin zaɓen 2027?

Wane zaɓi ya rage wa PDP gabanin zaɓen 2027?

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  A ranar Litinin 9 ga Maris, 2026, ne kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar soke hukuncin kotun farko, wanda ya hana hukumar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) amincewa da sakamakon babban taron Jam'iyyar PDP da aka yi a ranar 31 ga Oktoba, 2025. A bara ne dai mai shari'a James Omotosho na babban koton tarayya da ke Abuja ya soke babban taron PDP da aka yi a birnin Ibadan na jihar Oyo a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban bara. A hukuncin, wanda dukkan alƙalan kotun guda uku suka yanke, kotun ɗaukaka ƙarar…
Read More
Dalilin da ya sa na sauya sheƙa zuwa APC – Gwamna Dauda

Dalilin da ya sa na sauya sheƙa zuwa APC – Gwamna Dauda

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rikicin cikin gida da kuma taƙaddamar shari’a da ke addabar Jam’iyyar PDP su ne manyan dalilan da suka sa ya yanke shawarar sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC. Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Mani Mummuni, ne ya sanar da sauyin sheƙar a hukumance a ranar Litinin, bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Gusau. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa sauyin daga Jam’iyyar PDP zuwa APC ya zama dole…
Read More
2027: Yankin Kudu maso Yamma zai yi wa Tinubu ruwan ƙuri’u miliyan 10 – Bamidele

2027: Yankin Kudu maso Yamma zai yi wa Tinubu ruwan ƙuri’u miliyan 10 – Bamidele

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce Jam’iyyar APC ta tsara shirin tattara ƙuri’u domin tabbatar da cewa yankin Kudu maso Yamma ya bai wa Shugaba Bola Tinubu aƙalla ƙuri’u miliyan 10 a zaɓen Shugaban ƙasa na 2027. Bamidele ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gwamnan Jihar Ekiti na 2026 mai mambobi 57 a birnin Ado Ekiti, babban birnin jihar. Shi ne shugaban wannan kwamitin. Yankin Kudu maso Yamma ya ƙunshi jihohin Ekiti, Ondo, Ogun, Osun, Lagos da Oyo, kuma Shugaba Tinubu ya…
Read More
ADC za ta bada mamaki a zaɓen 2027, inji jigo a jam’iyyar

ADC za ta bada mamaki a zaɓen 2027, inji jigo a jam’iyyar

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani jigo a jam’iyyar ADC, Cif Ogochukwu Agabus Umunnakwe Onyema, ya bayyana cewa jam’iyyarsa na da ƙwarin gwiwar kawo babban sauyi a zaɓen shekarar 2027, inda ya ce ADC za ta ba da mamaki a siyasar Nijeriya. Onyema ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a birnin Enugu, inda ya ce shugabancin jam’iyyar ADC a halin yanzu yana da tsari mai kyau tare da ƙudurin kwace mulki daga hannun jam’iyya mai mulki ta APC a babban zaɓen da ke tafe. Ya ce, duk da ƙalubalen da ake fuskanta a siyasar ƙasar,…
Read More
KASSAROTA ta fara kai samame kan haramtattun tashoshin mota a Katsina

KASSAROTA ta fara kai samame kan haramtattun tashoshin mota a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Samamen, da aka fara ya shafi wurare da dama ciki har da tashar mota da manyan hanyoyi inda jami’an hukumar suka gargaɗi masu gudanar da ayyuka a wuraren su koma tashoshin da aka amince da su. Jami’an hukumar sun kuma gargaɗi masu sayar da kayayyaki a kan tituna da masu wankin motoci da babura, suna mai cewa irin waɗannan ayyuka na haddasa cunkoso, toshe hanyoyin masu tafiya a ƙafa, da kuma lalata kwalta. Babban daraktan KASSAROTA, Manjo Garba Yahaya Rimi (mai ritaya), ya ce an ɗauki matakin ne bayan gargaɗi da dama da aka sha…
Read More