ukarofi

12636 Posts
Majalisar Birtaniya ta rusa tsarin kujerun gado na sarakuna a majalisar dattijai 

Majalisar Birtaniya ta rusa tsarin kujerun gado na sarakuna a majalisar dattijai 

Majalisar dokokin ƙasar Birtaniya ta amince da wata sabuwar doka da za ta kawo ƙarshen tsohon tsarin da ke bai wa wasu ‘yan aristocrats damar zama mambobin Majalisar Dattijai saboda gadon sarauta kawai. Sabuwar dokar, wadda aka fi sani da Hereditary Peers Bill, ta samu amincewa a daren Talata a Majalisar Dattijai ta ƙasar, lamarin da ya kawo ƙarshen wani tsarin siyasa da ya shafe ƙarni da dama yana aiki a Birtaniya. Wannan mataki wani muhimmin ɓangare ne na shirin gyaran majalisar da gwamnatin Firaminista Keir Starmer ta jam’iyyar Labour ta ɗauka domin sabunta tsarin majalisar dokokin ƙasar. A cikin…
Read More
Za su farmake mu cikin mako guda, inji Trump bayan gano ƙarfin makaman Iran ya wuce yadda yake tunani

Za su farmake mu cikin mako guda, inji Trump bayan gano ƙarfin makaman Iran ya wuce yadda yake tunani

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce Iran tana da makamai masu linzami sama da yadda ake tunani da fari, wanda hakan ya sa take shirin kai wa Amurka hari. Trump ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin jawabi ga ‘yan majalisa na jam’iyyarsa ta Republican a taron shekara-shekara na nazarin tsare-tsaren da aka yi a Florida. A cewarsa, ƙasar za ta iya kai musu hari cikin mako ɗaya duba da shirin da suka yi wa yaƙin. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan jawabin Shugaban na Amurka cewa hare-haren soji da take kai wa Iran ka iya ƙarewa nan…
Read More
Ashraf Mahrous: Jarumin ɗan Masar da ya ja jirgi mai nauyin tan 700 da haƙoransa

Ashraf Mahrous: Jarumin ɗan Masar da ya ja jirgi mai nauyin tan 700 da haƙoransa

Wani ɗan dambe daga ƙasar Masar mai suna Ashraf Mahrous ya jawo hankalin duniya bayan da ya ja jirgi mai nauyin tan 700 (kusan kilo 635,000) da haƙoransa a gaɓar tekun Hurghada da ke yankin Bahar Maliya. Mahrous, wanda ake kira “Kabonga”, kuma aka fi saninsa da laƙabin “Jarumi Mai ƙarfi” a Masar, ya kuma ci gaba da jan wasu jiragen ruwa biyu tare da nauyin tan 1,150 (fiye da kilo miliyan ɗaya) gaba ɗaya. “Na zo yau domin kafa tarihi a duniya,” inji Mahrous bayan gwajin. “Na jawo su duka, da taimakon Allah, domin in tabbatar wa duniya cewa…
Read More
Dangote ne kan gaba yayin da ’yan Nijeriya huɗu suka shiga jerin attajiran Afirka

Dangote ne kan gaba yayin da ’yan Nijeriya huɗu suka shiga jerin attajiran Afirka

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fitaccen ɗan kasuwar Nijeriya, Aliko Dangote, ya sake riƙe matsayinsa na mutum mafi arziki a nahiyar Afirka, bayan da mujallar tattalin arziki ta duniya ta fitar da jerin attajiran Afirka na shekarar 2026. Rahoton ya nuna cewa dukiyar Dangote ta kai kimanin dala biliyan 28.5, abin da ya sa ya ci gaba da zama na ɗaya a jerin. Sabon rahoton da mujallar Forbes ta fitar ya kuma nuna cewa attajiran Afirka sun ƙara tara sama da dala biliyan 20 cikin dukiyarsu a cikin shekara guda da ta gabata, sakamakon bunƙasar kasuwanni da kuma daidaituwar kuɗaɗen wasu…
Read More
Kara jari: Manyan bankuna 30 sun cika sabbin sharuɗɗan CBN

Kara jari: Manyan bankuna 30 sun cika sabbin sharuɗɗan CBN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar cewa, manyan bankuna 30 a faɗin ƙasar sun riga sun samu damar cika sabbin sharuɗɗan mafi ƙarancin jari da bankin ya gindaya a cikin shirin sake ƙarfafa jarin bankuna. Sanarwar ta fito ne a safiyar ranar Asabar ta bakin Muƙaddashin Daraktar Sashen Hulɗa da Jama’a na bankin, Hajiya Hakama Sidi Ali. Ta bayyana cewa zuwa ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2026, shirin ƙarfafa jarin bankuna na tafiya yadda ya kamata, inda bankuna 30 suka riga suka cika sabon mafi ƙarancin jari da aka tanada bisa lasisin da kowanne…
Read More
Farashin abinci ya ragu da kashi 50 a Nijeriya – Gwamnatin Tarayya

Farashin abinci ya ragu da kashi 50 a Nijeriya – Gwamnatin Tarayya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Noma da Tsaron Abinci na Tarayya, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa sabon mayar da hankali da gwamnatin ƙasa ta yi kan harkar noma ya fara haifar da sakamako mai kyau, inda farashin kayayyakin abinci a faɗin Nijeriya ya ragu da kusan kashi 50 cikin ɗari. Ministan ya bayyana haka ne a wani zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma ’yan ƙasa da aka gudanar a birnin Abuja ranar Juma’a. Ya ce, Gwamnatin Tarayya ta sanya batun tsaron abinci a sahun gaba na manufofinta na ƙasa, saboda muhimmancinsa wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki…
Read More
Matsin lamba ko son rai: Yadda BBL da bilicin suka zama al’ada a masana’antun nishaɗi

Matsin lamba ko son rai: Yadda BBL da bilicin suka zama al’ada a masana’antun nishaɗi

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS  *Ba a amince da allurar glutathione don sauya launin fata ba - Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka An samu rahotannin mace-mace da suka danganci BBL fiye da wasu hanyoyin gyaran jiki - ASERF Mercury na iya haddasa lalacewar ƙoda, matsalar jijiyoyin jiki da kuma illa ga jarirai idan mai ciki na amfani da shi - WHO  2. Kafafen sada zumunta: Wasu za su yi mamakin sanyo kafafen sada zumunta cikin wannan layin, saidai da taimakon bayanin da zan yi yanzu za a fahimci inda na dosa. Kafafen sada…
Read More
Yadda Arewacin Nijeriya ya fi fama da matsalar ’yan mata masu ɗaukar ciki – Rahoto

Yadda Arewacin Nijeriya ya fi fama da matsalar ’yan mata masu ɗaukar ciki – Rahoto

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani sabon rahoto kan lafiyar al’umma ya bayyana cewa matsalar ɗaukar ciki a tsakanin ’yan mata ƙanana na ci gaba da zama babban ƙalubale ga lafiyar jama’a a Nijeriya, musamman a jihohin arewacin ƙasar kamar Kebbi, Zamfara da Kaduna, inda aka ce ake samun mafi yawan adadin wannan matsala. Rahoton, mai taken Rahoton Halin Lafiyar ƙasa na 2025, wanda aka fitar a ranar Lahadi a Abuja, an samar da shi ne ƙarƙashin dokar Dokar Kiwon Lafiya ta ƙasa ta shekarar 2014. Rahoton ya yi nazari kan yanayin lafiyar haihuwa na ’yan mata a faɗin Nijeriya, inda…
Read More
Nijeriya ta fice daga tsananin matsin tattalin arziki – Tinubu

Nijeriya ta fice daga tsananin matsin tattalin arziki – Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ƙasar ta fara fita daga mawuyacin halin tattalin arzikin da ta shiga a baya, yana mai cewa a halin yanzu gwamnoni a jihohin ƙasar ba sa sake komawa bankuna domin karɓar bashi don biyan albashin ma’aikata. Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin addinai da sarakunan gargajiya domin buɗa-baki na haɗin gwiwar addinai a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja. Bayanin hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai…
Read More
Kwastom ta kama ƙwayoyin Tramadol 248,500 masu darajar miliyan N273 a Yobe

Kwastom ta kama ƙwayoyin Tramadol 248,500 masu darajar miliyan N273 a Yobe

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kwastom ta Nijeriya ta samu gagarumar nasara a yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi bayan ta kama ƙwayoyin Tramadol Hydrochloride (mai nauyin 250mg kowanne) guda 248,500, waɗanda aka kiyasta kuɗinsu a kasuwa sun kai kimanin Naira miliyan 273.35 a jihar Yobe. Shugaban Sashen Ayyuka na Tarayya na Yanki D da ke Bauchi na Hukumar Kwastom, Kwanturola Abdullahi Ka’ila, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin. Ya ce nasarar ta samu ne sakamakon ingantaccen tattara bayanan sirri, haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, da kuma tsauraran matakan sa ido…
Read More