ukarofi

12636 Posts
Yadda ta’addanci a cikin Ramadan ke cutar da Musulmi

Yadda ta’addanci a cikin Ramadan ke cutar da Musulmi

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Watan Ramadan wata ne mai tsarki da daraja ga al'ummar Musulmi a ko'ina, wanda a cikin sa masu azumi ke shagaltuwa da ayyukan ibada, taimakawa juna, da gujewa faɗa ko tayar da fitina. Sai dai abin takaici da damuwa shi ne a bana al'ummar Musulmi sun gudanar da ibadar azumin Ramadan cikin fargaba da tashin hankali, musamman a Nijeriya da wasu yankunan Gabas ta Tsakiya, inda ake cigaba da luguden wuta tsakanin ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka da kuma Isra'ila.  A Nijeriya, yankin arewacin ƙasar nan na cigaba da shiga tasku daga hare-haren 'yan…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta gudanar da gasar sauyin yanayi

Gwamnatin Katsina za ta gudanar da gasar sauyin yanayi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A cewar mai magana da yawun gwamna Kaula Muhammad an shirya gasar fahimtar sauyin yanayi ta shekarar 2026 ga ɗalibai, inda aka gayyaci dubban matasa daga makarantu daban-daban su nuna fahimtarsu kan matakan kare muhalli da sauyin yanayi. An shirya gasar ne ta hannun sakatariyar sauyin yanayi ta Jihar Katsina ƙarƙashin shirin “Governor Dikko Umaru Raɗɗa Green Prize Initiative,” wanda ke da burin ƙarfafa matasa su taka rawa wajen kare muhalli da tabbatar da ɗorewar albarkatun ƙasa. Mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin sauyin yanayi, Hon. Suleiman Ribadu, ya bayyana cewa ɗalibai…
Read More
Gombe: Sarkin Gona ya tallafa wa marayu 40 da abinci da tufafi

Gombe: Sarkin Gona ya tallafa wa marayu 40 da abinci da tufafi

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Mai Martaba Sarkin Gona, Alhaji Umar Abdulkadir Abdulsalam, ya tallafa wa marayu 40 da kayan abinci da tufafi a Jihar Gombe, a wani yunƙuri na taimaka wa marasa galihu a cikin al’umma. An kai tallafin ne ta hannun wata tawaga daga masarautar Gona wadda ta kai ziyara gidan marayu da ke Tumfure domin miƙa kayan tare da nuna ƙauna da kulawa ga yaran. Ziyarar ta gudana ne bisa umarnin Mai Martaba Sarkin Gona, wanda ya jaddada buƙatar shugabannin al’umma da masu hali su rika taimaka wa marayu da sauran marasa galihu domin rage musu raɗaɗin…
Read More
Gidauniyar jin ƙai ta raba ɗinkunan Ƙaramar Sallah ga marayu a Dutsinma

Gidauniyar jin ƙai ta raba ɗinkunan Ƙaramar Sallah ga marayu a Dutsinma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gidauniyar jin ƙai, da ke garin Dutsinma wadda ke ayyukan ta na tallafawa marayu, kiwon lafiya da kula da maƙabartu da sauransu ta raba tallafin ɗinkunan kayan sawa ga marayu maza da mata da ke a ƙarƙashin kulawar gidauniyar. An gudanar da rabon tallafin ne domin bai wa waɗannan marayu kayan Sallah, ta yadda su ma za su gudanar da bukukuwan Sallah cikin farin ciki da walwala. Daga cikin mahalarta taron akwai shugabannin gidauniyar da abokan hulɗar gidauniyar. Gidauniyar ta ƙunshi irin su Abdul AK Foundation, Lado Development Foundation, ƙungiyar NUT reshen Dutsinma, ƙungiyar ɗalibai…
Read More
PDP tsagin Nyesom Wike ya zaɓi sabbin shugabaninta a Yobe

PDP tsagin Nyesom Wike ya zaɓi sabbin shugabaninta a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMIN, Damaturu Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Nijeriya, ƙarƙashin ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ta zaɓi shugabannin jam'iyyar a matakin jihar, ƙananan hukumomi tare da na gundumomi daban-daban a faɗin jihar Yobe. Jam'iyyar PDP a Jihar Yobe, ta zabi Hon. Yusuf Abdullahi Mallushe, a matsayin shugaban jam'iyyar PDP ba tare da hamayya ba, biyo bayan amincewar masu ruwa da tsaki a jam'iyyar, a babban taron da suka gudanar, ranar Asabar, a Damaturu, babban birnin jihar Yobe. A jawabinsa, jim kaɗan da rantsar da shi, sabon shugaban jam'iyyar PDP, ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda taron ya gudana…
Read More
Neman aure a zamanin da da yanzu

Neman aure a zamanin da da yanzu

Daga AISHA ASAS Akwai iyaye da dama da ba su san wa 'yarsu ta aura ba - Aisha Gambo Mai karatu barka da war haka, barkanmu da sake kasancewa a shafin Gimbiya na jaridarku mai farin jini, Manhaja. Kamar yadda ku ka sani, shafin namu bai tsaya a iya tattaunawa da mata kan sana'oinsu ko ayyukansu ko kuma ƙalubalen da suke fuskatan a rayuwa ba. Shafin kan yi duba kan darrusan da ke buƙatar tattaunawa, don wayar da kan al'umma. A wannan makon, za mu tattauna kan lamarin da ya shafi neman aure, wanda da yawa kan ce yana da…
Read More
‘Yan daba sun kai wa ɗan jarida hari saboda ya tsawatar musu kan rashin yin azumi

‘Yan daba sun kai wa ɗan jarida hari saboda ya tsawatar musu kan rashin yin azumi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wasu gungun 'yan daba sun ji wa wani ɗan jarida kuma mai aikin Hisbah, Idris Usman Alhassan rauni a jihar Kano. Daily Nigerian Hausa ta samu labarin cewa lamarin ya faru a Unguwar Kurna Tudun Bojuwa Titin Rufaidah a ƙaramar hukumar Fagge inda ƴan daban su ka jikkata Idris saboda ya ga su na share-shaye da tsakar rana yayin da ake azumin watan Ramadan. Rahotanni sun nuna cewar ɗan jaridar ya tsallake rijiya da baya ne bayan da wani daga cikin ƴan daban da aka bayyana sunan sa da Yusuf Mai Ƙarfi ya yi yinƙurin…
Read More
Buɗe bakin Ramadan: Sanata Wadada ya baƙunci ƙungiyar ALGON ta Nasarawa

Buɗe bakin Ramadan: Sanata Wadada ya baƙunci ƙungiyar ALGON ta Nasarawa

DAGA JOHN DOGO WADA a Keffi Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Nasarawa ta Yamma a majalisar dattawa ta tarayya sanata Ahmed Aliyu Wadada ya baƙunci shugabannin ƙananan hukumonin jihar Nasarawa a ƙarƙashin ƙungiyar ALGON da masu ruwa da tsaki na jam'iyar APC mai ci a jihar don cin abincin buɗe baki na azumin watan Ramadan. Zaman buɗe bakin an gudanar da shine a gidan sanatan da ke GRA a birnin Keffi. Da yake jawabi jim kaɗan bayan buɗe bakin, Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya gode wa duka baƙin nasa musammam shugabannin ƙananan hukumonin dangane da amsa gayyatarsa da yace suka…
Read More
Gobarar Kerzers Switzerland: Mutane shida suka rasa rayukansu bayan wani ya kunna wuta a jikinsa

Gobarar Kerzers Switzerland: Mutane shida suka rasa rayukansu bayan wani ya kunna wuta a jikinsa

Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon wata gobara mai muni da ta tashi a cikin wata bas a garin Kerzers da ke yammacin ƙasar Switzerland. Hukumomin ‘yan sanda sun bayyana cewa gobarar ta faru ne a daren Talata, kuma akwai alamun cewa wani mutum a cikin bas ɗin ne ya janyo gobarar da gangan. Kakakin ‘yan sandan yankin Fribourg, Frederic Papaux, ya ce binciken farko ya nuna cewa wani mutum da ke cikin bas ɗin na iya aikata wannan aiki da gangan. Rahotanni daga wasu kafafen watsa labarai sun nuna cewa mutumin ya…
Read More
Mu ne za mu yanke hukuncin lokacin da yaƙin zai ƙare – Martanin Iran kan kalaman Trump na yaƙinsu ya kusa ƙarewa

Mu ne za mu yanke hukuncin lokacin da yaƙin zai ƙare – Martanin Iran kan kalaman Trump na yaƙinsu ya kusa ƙarewa

Rundunar juyin juya halin ƙasar Iran ta yi watsi da kalaman Shugaba Donald Trump na cewa yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar akan Iran ya kusa ƙarewa, yayin mayar da martani akan furucin shugaban Amurkan. Trump ya bayyana a wani taro a Florida cewa Amurka ta samu gagarumar nasara a yaƙin, kuma akwai yiwuwar kawo ƙarshensa nan kusa. Shugaban Amurka ya ce Iran na shirin kai hari kan Amurka kuma tana ƙoƙarin farfado da shirinta na Nukiliya. A kan yiwuwar kai hari kan sabon jagoran addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, Trump ya ce ba abu ne da ya kamata…
Read More