ukarofi

12636 Posts
Mutane 15 suka mutu sakamakon ƙazamin faɗa tsakanin yan sa kai da tubabbun ‘yan bindiga a Katsina

Mutane 15 suka mutu sakamakon ƙazamin faɗa tsakanin yan sa kai da tubabbun ‘yan bindiga a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu'azu Ɗanmusa ya fitar da sanarwar aukuwar lamarin. Ya bayyana cewa faɗan ya faru ne a ƙauyukan Falale da Kadobe a ƙaramar hukumar jibiya inda yan sai ka sukai taho mu gama da tubabbun 'yan bindiga a yaƙin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 15. Dr Ɗanmusa ya ƙara da cewa wannan taho mu gama da yan sa kai su kayi da 'yan bindigan da yayi sanadiyar mutuwar mutane uku shine yasa 'yan bindiga suka dawo ɗaukar fansa da aka ƙara samun mutanen da suka mutu. Amma a…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis da Juma’a a matsayin hutun Ƙaramar Sallah

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis da Juma’a a matsayin hutun Ƙaramar Sallah

Daga USMAN KAROFI Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis 19 ga watan Maris da Juma’a 20 ga watan Maris 2026 a matsayin ranakun hutun bikin Eid al-Fitr, wanda ke nuna ƙarshen watan azumin Ramadan. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar ga manema labarai a ranar Talata. A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin Ramadan cikin nasara. Ya kuma buƙaci Musulmi da su ci gaba da riƙe kyawawan ɗabi’u kamar soyayya, karamci, zaman lafiya, haƙuri da sadaukarwa da aka koyar a lokacin azumi. Ministan…
Read More
Sautus Sunnah ya buƙaci al’ummar Katsina su jajirce wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

Sautus Sunnah ya buƙaci al’ummar Katsina su jajirce wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban JIWIBS a jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan Sautus sunnah ya yi wannan kira ga ɗaukacin al’umma da su haɗa kai wajen yaƙar safarar da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, inda yana mai gargaɗin cewar matsalar na barazana ga makomar matasa da ci gaban al’umma baki ɗaya. Malamin ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabin rufe Tafsirin Alkur’ani mai girma na watan Ramadan na bana a Masallacin Modibbo (Kandahar) da ke birnin Katsina. A cewarsa, yawaitar shigo da miyagun ƙwayoyi cikin al’umma da kuma bazuwarsu a tsakanin matasa na barazana ga…
Read More
‘Yan bindiga su kashe mutum ɗaya da sace mutum bakwai a Kaduna

‘Yan bindiga su kashe mutum ɗaya da sace mutum bakwai a Kaduna

Daga USMAN KAROFI Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari a unguwar Sabon Gyero da ke Millennium City a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum guda tare da sace wasu bakwai. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga yankin ne da sanyin safiyar ranar Litinin cikin adadi mai yawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da alhini. Majiyoyi daga yankin sun ce ‘yan bindigar sun nufi wani gida kai tsaye inda suka sace mata uku da ƙananan yara huɗu. Haka kuma, sun kai hari wani wajen cajin waya inda suka harbe wani matashi mai…
Read More
Iran na harin kasuwancin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya

Iran na harin kasuwancin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya

Daga USMAN KAROFI Rahotanni daga yankin Gabas ta Tsakiya sun nuna cewa rikicin da ke gudana a Tekun Gulf na ƙara tsananta, inda Iran ta fara faɗaɗa nau’in wuraren da take kai wa hari. A farkon makonnin rikicin, hare-haren sun fi karkata ne kan cibiyoyin soji na Amurka, ciki har da na’urorin kariyar makamai masu linzami da jiragen yaƙi da ke sansanonin soja. Sai dai a yanzu, bayan shigowar mako na uku, dakarun IRGC sun bayyana cewa dukkan kadarorin kasuwancin Amurka a yankin sun zama halattattun wuraren hari. Hukumomin Iran sun kuma yi gargaɗi cewa duk bankunan Amurka da ke…
Read More
Ƙungiyar masu keke napep ta yaba da ƙoƙarin Gwamna Uba Sani wajen inganta sufuri a Kaduna

Ƙungiyar masu keke napep ta yaba da ƙoƙarin Gwamna Uba Sani wajen inganta sufuri a Kaduna

Daga SHEHU YAHAYA a Kaduna Ƙungiyar masu tuƙa keke napep a Jihar Kaduna ta bayyana gamsuwarta da matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin inganta harkar sufuri da sauƙaƙa zirga-zirgar al’umma a faɗin jihar. Shugaban ƙungiyar na jihar, Aminu Ibrahim Goronyo, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar Kaduna. A cewarsa, ƙoƙarin da gwamnan jihar, Uba Sani, yake yi na gyaran hanyoyi da tsara harkokin sufuri ya taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa aikin masu keke napep da sauran masu sana’ar sufuri a jihar. Ya ƙara da cewa, matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka sun…
Read More
Gwamnan Zamfara na cikin tawagar da za su raka Tinubu zuwa Birtaniya

Gwamnan Zamfara na cikin tawagar da za su raka Tinubu zuwa Birtaniya

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, na cikin jerin manyan jami’an da aka zaɓa su raka Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a wata muhimmiyar ziyarar aiki ta ƙasa zuwa Birtaniya, wadda ake kallon ta a matsayin ziyarar tarihi tsakanin ƙasashen biyu. Shugaban Ƙasa tare da Uwargidansa da sauran ’yan tawagarsa za su tashi daga Abuja ranar Talata domin fara wannan ziyara ta musamman. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa Sarkin Birtaniya, King Charles III, zai karɓi baƙuncin Shugaba Tinubu, Uwargidansa da tawagarsu a fadar sarauta ta Windsor Castle daga…
Read More
Shugaban ƙungiyar Izala reshen Katsina ya buƙaci al’umma su tashi tsaye wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi

Shugaban ƙungiyar Izala reshen Katsina ya buƙaci al’umma su tashi tsaye wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi

Daga UMAR GARBA a Katsina Fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Katsina, Sheikh Dr. Yakubu Musa Hassan, ya yi kira ga ɗaukacin al’umma da su haɗa kai wajen yaƙar safarar miyagun ƙwayoyi da sayar da su, yana mai gargadin cewar matsalar na barazana ga makomar matasa da ci gaban al’umma baki ɗaya. Malamin ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabin rufe Tafsirin Alqur’ani mai girma na watan Ramadan na bana a Masallacin Modibbo (Kandahar) da ke birnin Katsina. A cewarsa, yawaitar shigo da miyagun ƙwayoyi cikin al’umma da kuma bazuwarsu a tsakanin matasa na barazana ga…
Read More
Sabbin darussa 70 sun samu amincewa a kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli

Sabbin darussa 70 sun samu amincewa a kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli

Gyare-gyaren da gwamnatin Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Uba Sani ke aiwatarwa a ɓangaren ilimi na ci gaba da haifar da sakamako mai kyau, inda  Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya ta samu gagarumin ci gaba a fannin tantance darussa, gina ababen more rayuwa da kuma kula da jin daɗin ɗalibai. Shugaban kwalejin  Injiniya Muhammad Kabir Abdullah, ne ya bayyana haka yayin da yake karɓar tawagar ‘yan jarida a rangadin da suka kai harabar makarantar da ke Zariya. Ya ce goyon bayan da gwamnatin jihar ke bayarwa ya taimaka matuƙa wajen samun amincewar sabbin shirye-shiryen karatu daga hukumomin…
Read More
Arewa a rage barci haka nan

Arewa a rage barci haka nan

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ba haka kawai na ke wannan rubutun ba sai da hujjoji kwarara kamar hasken rana da ƙarfe 12 pm. ‘Yan kwangilar tada fitinar addini da ƙabilanci da amfani da rigar bagaye ta Hausawa ba Hausawa ba ne sam. Duk wanda ya san Arewa da gaske zai amince ba wani abu mai kama da wai Bahaushe ya mulki kansa! Neman tada fitina ne kawai don kwangila, tun da a hakika Arewa 100% na hannun Hausawa da masu amfani da harshen Hausa a matsayin harshensu na farko a rayuwa. Wautar ‘yan kwangilar ita ce sun dauka da…
Read More