Daga SHEHU YAHAYA a Kaduna
Ƙungiyar masu tuƙa keke napep a Jihar Kaduna ta bayyana gamsuwarta da matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin inganta harkar sufuri da sauƙaƙa zirga-zirgar al’umma a faɗin jihar.
Shugaban ƙungiyar na jihar, Aminu Ibrahim Goronyo, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar Kaduna.
A cewarsa, ƙoƙarin da gwamnan jihar, Uba Sani, yake yi na gyaran hanyoyi da tsara harkokin sufuri ya taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa aikin masu keke napep da sauran masu sana’ar sufuri a jihar.
Ya ƙara da cewa, matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka sun taimaka wajen rage matsalolin zirga-zirga tare da samar da yanayi mai kyau ga masu sana’o’in sufuri domin gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali.
Shugaban ƙungiyar ya kuma yaba da irin ci gaban da gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin gwamna Uba Sani ta kawo a ɓangarori daban-daban na rayuwar al’umma.
A ƙarshe, Aminu Ibrahim Goronyo ya tabbatar da cewa ƙungiyar masu keke napep ta jihar Kaduna za ta ci gaba da bai wa gwamnatin jihar cikakken goyon baya domin tabbatar da cigaban jihar da walwalar al’umma.
