ukarofi

12636 Posts
Sarki Sunusi II zai jagoranci hawan sallah – Gwamnatin Kano

Sarki Sunusi II zai jagoranci hawan sallah – Gwamnatin Kano

Daga USMAN KAROFI Gwamnatin jihar Kano State ta tabbatar da cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zai jagoranci bikin hawan sallah na wannan shekara duk da rikicin sarauta da ke gudana. Wannan mataki ya biyo bayan amincewar gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya ce an ɗauki wannan shawara ne domin tabbatar da zaman lafiya yayin bukukuwan Sallah. A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa za a gudanar da hawan Idi ƙarƙashin jagorancin Sarkin, inda za a fara daga filin Idi na Ƙofar Mata zuwa wasu muhimman wurare a cikin…
Read More
Gwamnatin Kano ta sanya ƙa’idoji masu tsauri kan hawan sallah saboda tsaro

Gwamnatin Kano ta sanya ƙa’idoji masu tsauri kan hawan sallah saboda tsaro

Daga RABIU SANUSI Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da sabbin tsauraran matakai domin tafiyar da bukukuwan hawan Sallah, biyo bayan rahotannin sirri da ke nuni da yiwuwar wasu su tayar da tarzoma da kawo cikas ga zaman lafiya a jihar. A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar, ya ce matakin ya biyo bayan bayanan tsaro da majalisar tsaron jiha ta bayar wanda ke nuna cewa wasu na shirin haddasa ruɗani a lokacin bukukuwan. Ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da jajircewa wajen kare al’adun gargajiyar…
Read More
Muhimmancin haɗin kai a cikin al’umma

Muhimmancin haɗin kai a cikin al’umma

Tare da BILKISU YUSUF ALI Haɗin kai yana daga cikin manyan ginshiƙai da suke tabbatar da zaman lafiya, cigaba da ɗorewar kowace irin al’umma. Al’umma ba ta iya bunƙasa sai idan mutane suna yin aiki a tare, suna girmama juna, suna taimakon juna tare da fifita muradun kowa a kan na kansa. A tarihi da al’adance, Hausawa sun gina rayuwarsu bisa haɗin kai, wanda ya bayyana ta hanyar karin maganganu kamar “Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka” da “Taimakon juna ke kawo arziƙi”. Ma’anar haɗin kai Haɗin kai na nufin aiki tare tsakanin mutane ko ƙungiyoyi domin cimma wata manufa…
Read More
Tarihi da gwagwarmayar Nelson Mandela

Tarihi da gwagwarmayar Nelson Mandela

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An haifi Nelson Rohlihlahla Mandela ne a ranar 18 ga watan Yulin 1918 a ƙauyen Mɓezo na yankin Umtata wanda a lokacin ya ke lardin Cape na ƙasar Afirka ta kudu. Asalin sunan da mahaifinsa ya naɗa masa shi ne ‘Rolihlahla’ wanda a yaren ƙabilarsa ta ɗhosa yana nufin ‘mai ƙiriniya’ ko ‘neman fitina’ wanda kuma daga baya lalle sunan ya bi shi saboda irin ƙiriniyar da aka ce yana da shi tun yana ƙarami sannan kuma ya ci gaba da binsa wanda ana ganin yana daga cikin abubuwan da suka sanya shi shiga ƙungiyoyin fafutuka…
Read More
CAF ta ƙwace kofin AFCON daga hannun Senegal ta bai wa Morocco

CAF ta ƙwace kofin AFCON daga hannun Senegal ta bai wa Morocco

Daga USMAN KAROFI Hukumar ƙwallon kafa ta Afirka (CAF) ta ƙwace kofin gasar AFCON na shekarar 2025 daga Senegal tare da bai wa Morocco nasara. Wannan hukunci ya biyo bayan rikicin da ya faru a wasan ƙarshe, inda ‘yan wasan Senegal suka bar fili na wani lokaci domin nuna rashin amincewa da hukuncin alƙalin wasa. A cikin sanarwar da CAF ta fitar, ta bayyana cewa an soke sakamakon wasan da Senegal ta ci da ci 1-0, tare da mayar da shi 3-0 a hukumance a matsayin nasarar Morocco. Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan saɓa dokokin wasa, musamman yadda…
Read More
Cire ni daga Sarkin Kano a 2020 bai firgita ni ba – Sarki Sunusi na ll

Cire ni daga Sarkin Kano a 2020 bai firgita ni ba – Sarki Sunusi na ll

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana dalilin da ya sa ya kasance cikin natsuwa da jajircewa bayan rasa manyan mukaman da ya taba rike wa a rayuwar jama’a. Sanusi ya yi wannan bayani ne yayin jawabinsa a taron Fola Adeola Annual Ramadan Lecture, inda ya yi magana kan muhimmancin juriya da imani da Allah wajen fuskantar sauye-sauyen rayuwa. Ya ce dogaro da Allah ne ya taimaka masa wajen tsallake mawuyacin lokaci bayan dakatar da shi daga muƙamin gwamnan CBN da kuma cire shi daga sarautar…
Read More
Zuwa ga maza kan rashin fahimtar mata

Zuwa ga maza kan rashin fahimtar mata

Assalamu alaikum, barka da warhaka, Edita. Da fatan kowa yana lafiya. A lokuta da yawa aure yakan mutu saboda rashin sani ko ƙarancin ilimin maza game da yanayin mata a lokacin da za su fara al’ada (menstruation), ko suke yi; ko lokacin da suke ɗauke da ƙaramin ciki, wato lokacin laulayi da lokacin da cikin ya kai wata bakwai zuwa lokacin da za su haife shi. Kwana 5 ko 8 kafin su fara al’ada suna zama kwanakin haƙuri ga duk magidancin da ya gane haka. Duk da yake cewa ba a cika tattauna irin waɗannan abubuwa a nan ƙasar Hausa…
Read More
Matsalolin da ke hana matasa rungumar noma

Matsalolin da ke hana matasa rungumar noma

Assalam alaikum Wani binciken masana da ƙungiyar Heifer International ta gudanar ya bayyana cewar, manoma a nahiyar Afirka basa samun damar da ta dace na amfani da sabbin na’urorin zamani wajen bunƙasa aikin noman da suke yi, abinda ke hana su samun ci gaban da ake buƙata. Rahotan ƙungiyar Heifer International da aka yi nazari a ƙasashe 11 da ke nahiyar Afirka ya gano cewar rashin samun na’urorin zamani wajen tafiyar da harkar noman da kuɗaɗe da kuma horarwar da ta dace na matuƙar illa ga ɓangaren noman da samar da abinci. Rahotan da aka yiwa laƙabi da 'makomar aikin…
Read More
POS: Tarihinsa da hukuncin amfani da shi wajen kasuwanci da fitar da kuɗaɗe da tura su (2)

POS: Tarihinsa da hukuncin amfani da shi wajen kasuwanci da fitar da kuɗaɗe da tura su (2)

Daga FARFESA AHMAD MURTALA Ci gaba daga makon jiya. 7- Waɗannan ayyuka na POS dukkansu sun halatta ta fuskoki marasa iyaka ba tare da wani dabaibayi ba. Ga kaɗan daga cikinsu: i- Akwai abubuwa masu yawa da banki koda kuwa wanda ba na Musulunci ba ne yake yi. Kuma ba a ƙirga su a matsayin haram. Wannan sun haɗa da tura kuɗi daga wani wuri zuwa wani “transfer’. Wannan ba wani laifi akansa. Mutum kuma zai biya banki ladan aikin da ya yi masa. Abin da masu shagunan POS suke yi a matsayinsu na wakilan banki, waɗanda ya san da…
Read More
Yadda dillalan gidaje ke cutar da masu neman haya a Abuja – Bincike

Yadda dillalan gidaje ke cutar da masu neman haya a Abuja – Bincike

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matsalar tsadar gidaje da ke addabar mazauna Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, da kuma wasu manyan biranen Nijeriya na ci gaba da tsananta, inda wani bincike ya nuna cewa wasu dillalan gidaje marasa ƙwarewa suna amfani da damar da ke tattare da ƙarancin gidaje domin cutar da masu neman haya. Binciken ya nuna cewa ayyukan da ba su dace ba da wasu dillalan gidaje ke yi suna taka rawa wajen ƙara tsadar haya, tare da jefa masu neman gidaje cikin halin ƙunci. A birane kamar Legas, Fatakwal da Kano, masu neman gidaje kan gamu da ƙalubale…
Read More