ukarofi

12636 Posts
ADC ta yi barazanar kai ƙara ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam kan tsare El-Rufai

ADC ta yi barazanar kai ƙara ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam kan tsare El-Rufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, a matsayin take haƙƙin ɗan adam mai tsanani. Jam’iyyar ta ce ana tsare da El-Rufai a hannun Hukumar ICPC tsawon kwanaki sama da 30, lamarin da ta bayyana a matsayin wanda ya saba doka da kundin tsarin mulki. A cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Laraba, ADC ta zargi hukumomin tsaro da ƙoƙarin tilasta wa El-Rufai sauya matsayinsa na siyasa ta hanyar matsin lamba. Jam’iyyar ta bukaci ICPC da ta mutunta dokar ƙasa…
Read More
Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda sama da 60, ciki har da kwamandojin ISWAP a Borno

Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda sama da 60, ciki har da kwamandojin ISWAP a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sojojin rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya sun hallaka sama da ’yan ta’adda 60 a garin Mallam Fatori da ke ƙaramar hukumar Abadam a jihar Borno. Rahotanni sun nuna cewa daga cikin waɗanda aka kashe akwai wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram/ISWAP da suka shahara wajen kai hare-hare. Rundunar sojin ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun taso ne daga yankin Duguri suna tafiya a ƙafa, tare da samun goyon bayan jiragen sama marasa matuƙi masu ɗauke da makamai, domin kai hari kan sansanin Bataliya ta 68. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun…
Read More
Sallah: NRC ta ƙaddamar da aikin zirga-zirgar sufurin jiragen ƙasa domin sauƙaƙa wa matafiya

Sallah: NRC ta ƙaddamar da aikin zirga-zirgar sufurin jiragen ƙasa domin sauƙaƙa wa matafiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta sanar da ƙaddamar da karin zirga-zirgar jiragen ƙasa a manyan hanyoyin sufuri a faɗin ƙasar nan domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a yayin bikin Eid-el-Fitr. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Callistus Unyimadu ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne domin samar da sufuri mai sauƙi, tsaro da inganci sakamakon karuwar matafiya da ake sa ran samu a lokacin bukukuwan Sallah. Hukumar ta bayyana cewa za a ƙara yawan tafiye-tafiye a muhimman hanyoyi kamar Legas–Ibadan da Abuja–Kaduna domin biyan buƙatar jama’a. A kan…
Read More
Gwamna Soludo ya sauke dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a Jihar Anambra

Gwamna Soludo ya sauke dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a Jihar Anambra

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya sauke dukkan muƙarraban siyasa da ke aiki a gwamnatinsa, inda ya umarce su da su miƙa ragamar aiki ga sakatarorin dindindin ko kuma manyan ma’aikatan gwamnati mafi girma a ma’aikatunsu da hukumominsu. Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan rantsar da shi karo na biyu a matsayin gwamnan jihar. A cikin wata sanarwa da Sakatare Dindindin na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Nwabufo Nwankwo ya fitar, an umarci dukkan wadanda abin ya shafa da su kammala mika ragamar aiki kafin ƙarshen ranar Laraba, 18 ga watan Maris,…
Read More
Gidauniyar Al-Ihsan ta raba tallafin abinci da kayan Sallah ga marayu da marasa ƙarfi

Gidauniyar Al-Ihsan ta raba tallafin abinci da kayan Sallah ga marayu da marasa ƙarfi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gidauniyar Al-Ihsan ƙarƙashin jagorancin Dr. Hauwa’u Yakubu Bako ta gudanar da rabon tallafin kayan abinci da kayan Sallah ga marayu da marasa ƙarfi a wani ɓangare na ayyukan jinƙai da take yi lokaci-lokaci domin rage raɗaɗin rayuwa ga al’umma. An gudanar da rabon tallafin ne a wani taro da ya gudanar a makarantar Yombe da ke Kurmin Mashi Kaduna, inda ya samu halartar masu ruwa da tsaki da kuma waɗanda suka amfana, inda aka raba kayayyaki da suka haɗa da shinkafa, wake, gero da kuma kayan sawa na Sallah domin bai wa waɗanda suka…
Read More
Muhimmancin kare sirrin asusun banki a zamani mai cike da ’yan damfara

Muhimmancin kare sirrin asusun banki a zamani mai cike da ’yan damfara

Gargaɗin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi wa ’yan Nijeriya kan kare lambobin sirri, kalmomin shiga da sauran bayanan banki ba kawai saƙon faɗakarwa ba ne na yau da kullum, illa wata muhimmiyar kira ce ga jama’a su ɗauki mataki cikin gaggawa domin kare dukiyoyinsu. A wani lokaci da damfarar kuɗi ke ƙara yawaita tare da ɗaukar sabbin salo na zamani, sakaci da bayanan banki na iya jefa mutum cikin babbar asara cikin ƙanƙanin lokaci. A yau, kusan duk mu’amaloli — daga biyan kuɗin abinci zuwa sayayya da kasuwanci — ana yin su ta hanyar fasahar zamani, wanda hakan…
Read More
Sheikh Lukuwa ya bijire wa umarnin Sultan, ya yi sallar idi yau a Sokoto

Sheikh Lukuwa ya bijire wa umarnin Sultan, ya yi sallar idi yau a Sokoto

Daga USMAN KAROFI a Abuja Wani malamin addinin Musulunci a jihar Sokoto, Sheikh Musa Lukuwa, ya jagoranci mabiyansa wajen gudanar da sallar idi a ranar Alhamis, saɓanin umarnin da majalisar sarkin musulmai ta bayar. Wannan ya zo ne bayan Saad Abubakar ya ayyana Juma’a a matsayin ranar Sallah, sakamakon rashin ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya. Rahotanni sun nuna cewa Sheikh Lukuwa ya jagoranci sallar ne a masallacinsa da ke Mabera da misalin ƙarfe 9:10 na safe, bayan ya yi bayani ga mabiyansa kan dalilan ɗaukar wannan mataki. Ya ce ya samu sahihan rahotanni na ganin jinjirin watan a Jamhuriyar…
Read More
Sallah ƙarama: Raɗɗa ya buƙaci Musulmi su haɗa kai da ƙaunar juna

Sallah ƙarama: Raɗɗa ya buƙaci Musulmi su haɗa kai da ƙaunar juna

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun babban jami'in hulɗa da jama'a na gwamnan,Dikko Raɗɗa ya taya al'ummar jihar Katsina murna zagayowar ƙaramar sallah. Gwamnan mai riƙe da sarautar Gwagwaren Katsina ya kuma taya al'ummar musulmi a jihar murnar kammala azumin watan Ramadan tare da kira da samun haɗin kai da kaunar juna a tsakanin al'ummar jihar. "A lokacin gudanar da bukukuwan Sallah,ina kira da Musulmi da su ƙaunaci juna,su haɗa kansu da zama masu wadatar zucci kamar yadda muka nuna a cikin watan Ramadan,"inji malam Dikko. Yayi fatan darussan da Musulmi suka koya…
Read More
‘Yan sanda sun hana ‘yan tauri shiga zagayen hawan sallah a Katsina

‘Yan sanda sun hana ‘yan tauri shiga zagayen hawan sallah a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Haɗin gwiwan 'yan sanda da kwamitin tsara gudanar da hawan sallah na masarautar Katsina ne suka haramtawa 'yan tauri shiga hawan sallah kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da sanarwar. Ya ce rundunar 'yan sanda da haɗin gwiwa na sauran jami'an tsaro sun ɗauki ƙwaƙƙwarar mataki na tabbatar da tsaro a yayin da ake gudanar da hawan sallah a Katsina. DSP Abubakar Sadiq ya tabbatar wa al'ummar Katsina cewa jami'an tsaro sun shirya tsaf domin ba kowa kariya yayin gudanar da bikin sallah…
Read More
Ayyukan marubuta a cikin watan Ramadan 

Ayyukan marubuta a cikin watan Ramadan 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Duk watan Ramadan mu kan tafi hutu daga fitar da labarai don yin ayyukan ibada - Zainab Abdullahi A kowacce shekara a lokaci irin wannan na Ramadan, musulmi a ko'ina a duniya na shagaltuwa da ayyukan ibada da neman kusanci da Allah, marubuta adabin Hausa su ma sukan jingine ayyukan rubuce-rubuce na nishaɗi da faɗakarwa da suke yi, zuwa ga tilawar Alƙur'ani, da faɗakarwa kan al'amuran addini, da koyar da girke-girke ga mata. A irin wannan lokaci mambobin ƙungiyar marubuta ta Jajirtattu Writers Association suna ware tsawon watan Ramadan don gudanar da shirye-shirye da suka shafi…
Read More