ukarofi

12630 Posts
Kammala azumin Ramadan dama ce ta addu’a don kawo ƙarshen gobara a Kano — Sarkin Kasuwar Beirut

Kammala azumin Ramadan dama ce ta addu’a don kawo ƙarshen gobara a Kano — Sarkin Kasuwar Beirut

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Sarkin Kasuwar Wayar Beirut da ke Kano, Alhaji Muhammad Inuwa Labaran, ya bayyana cewa kammala azumin watan Ramadan wata babbar dama ce ga al’umma su ƙara dagewa wajen yin addu’o’i domin samun kariya daga bala’o’i, musamman yawaitar gobara a kasuwannin jihar Kano da ma sauran sassan ƙasar. Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, inda ya ce addu’a ita ce hanya mafi inganci wajen magance irin waɗannan matsaloli da ke addabar al’umma. Ya kuma miƙa sakon jajensa ga waɗanda gobara ta shafa a kasuwannin Sabon Gari, Dakata da kasuwar waya, tare…
Read More
Sallah: NSCDC ta tura sama da jami’ai 3,400 domin samar da tsaro a Kano

Sallah: NSCDC ta tura sama da jami’ai 3,400 domin samar da tsaro a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Hukumar tsaron fararen hula da kadarorin gwamnati ta ƙasa (NSCDC) reshen jihar Kano ta tura sama da jami’ai 3,400 a faɗin jihar domin tabbatar da tsaro kafin, yayin da kuma bayan bukukuwan Eid-el-Fitr. Kwamandan hukumar a jihar, Hassan Mohammed Agalama, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, inda ya ce matakin na daga cikin shirye-shiryen da aka yi tun da wuri domin kare muhimman kadarorin ƙasa da kuma tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan a jihar. A cewarsa, an jibge jami’an a wuraren sallar Idi, wuraren shakatawa,…
Read More
Jam’iyyar LP ta sanya 23 ga watan Mayu domin zaɓen fidda gwani na Shugaban ƙasa 

Jam’iyyar LP ta sanya 23 ga watan Mayu domin zaɓen fidda gwani na Shugaban ƙasa 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar Labour Party ta sanya ranar 23 ga Mayu, 2026 domin gudanar da zaɓen fidda gwani na Shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027. Mai ba shugaban riƙo na jam’iyyar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ken Asogwa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce an amince da jadawalin ne a taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) tare da halartar hukumar zaɓe ta INEC. A cewarsa, jam’iyyar za ta gabatar da rijistar mambobinta ga INEC a ranar 15 ga Afrilu, yayin da za a gudanar da zabukan fidda gwani…
Read More
Mazauna Borno da Yobe sun san waɗanda suka kai hare-haren Maiduguri — CDS

Mazauna Borno da Yobe sun san waɗanda suka kai hare-haren Maiduguri — CDS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya ce mazauna jihohin Borno da Yobe sun san waɗanda ke da hannu a hare-haren ƙunar baƙin wake da aka kai Maiduguri, kuma dole su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar ta’addanci. Ya bayyana hakan ne a Maiduguri bayan shi da Babban Hafsan Sojin ƙasa, suka koma can bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu. Wannan na zuwa ne biyo bayan hare-hare a baya-bayan nan da suka yi sanadiyyar mutuwa da jikkata mutane. Oluyede, ya ce yawancin maharan ’yan yankin ne kuma ana san su yayin da suke rayuwa cikin…
Read More
ADC ta yi barazanar kai ƙara ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam kan tsare El-Rufai

ADC ta yi barazanar kai ƙara ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam kan tsare El-Rufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, a matsayin take haƙƙin ɗan adam mai tsanani. Jam’iyyar ta ce ana tsare da El-Rufai a hannun Hukumar ICPC tsawon kwanaki sama da 30, lamarin da ta bayyana a matsayin wanda ya saba doka da kundin tsarin mulki. A cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Laraba, ADC ta zargi hukumomin tsaro da ƙoƙarin tilasta wa El-Rufai sauya matsayinsa na siyasa ta hanyar matsin lamba. Jam’iyyar ta bukaci ICPC da ta mutunta dokar ƙasa…
Read More
Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda sama da 60, ciki har da kwamandojin ISWAP a Borno

Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda sama da 60, ciki har da kwamandojin ISWAP a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sojojin rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya sun hallaka sama da ’yan ta’adda 60 a garin Mallam Fatori da ke ƙaramar hukumar Abadam a jihar Borno. Rahotanni sun nuna cewa daga cikin waɗanda aka kashe akwai wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram/ISWAP da suka shahara wajen kai hare-hare. Rundunar sojin ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun taso ne daga yankin Duguri suna tafiya a ƙafa, tare da samun goyon bayan jiragen sama marasa matuƙi masu ɗauke da makamai, domin kai hari kan sansanin Bataliya ta 68. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun…
Read More
Sallah: NRC ta ƙaddamar da aikin zirga-zirgar sufurin jiragen ƙasa domin sauƙaƙa wa matafiya

Sallah: NRC ta ƙaddamar da aikin zirga-zirgar sufurin jiragen ƙasa domin sauƙaƙa wa matafiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta sanar da ƙaddamar da karin zirga-zirgar jiragen ƙasa a manyan hanyoyin sufuri a faɗin ƙasar nan domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a yayin bikin Eid-el-Fitr. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Callistus Unyimadu ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne domin samar da sufuri mai sauƙi, tsaro da inganci sakamakon karuwar matafiya da ake sa ran samu a lokacin bukukuwan Sallah. Hukumar ta bayyana cewa za a ƙara yawan tafiye-tafiye a muhimman hanyoyi kamar Legas–Ibadan da Abuja–Kaduna domin biyan buƙatar jama’a. A kan…
Read More
Gwamna Soludo ya sauke dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a Jihar Anambra

Gwamna Soludo ya sauke dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a Jihar Anambra

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya sauke dukkan muƙarraban siyasa da ke aiki a gwamnatinsa, inda ya umarce su da su miƙa ragamar aiki ga sakatarorin dindindin ko kuma manyan ma’aikatan gwamnati mafi girma a ma’aikatunsu da hukumominsu. Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan rantsar da shi karo na biyu a matsayin gwamnan jihar. A cikin wata sanarwa da Sakatare Dindindin na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Nwabufo Nwankwo ya fitar, an umarci dukkan wadanda abin ya shafa da su kammala mika ragamar aiki kafin ƙarshen ranar Laraba, 18 ga watan Maris,…
Read More
Gidauniyar Al-Ihsan ta raba tallafin abinci da kayan Sallah ga marayu da marasa ƙarfi

Gidauniyar Al-Ihsan ta raba tallafin abinci da kayan Sallah ga marayu da marasa ƙarfi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gidauniyar Al-Ihsan ƙarƙashin jagorancin Dr. Hauwa’u Yakubu Bako ta gudanar da rabon tallafin kayan abinci da kayan Sallah ga marayu da marasa ƙarfi a wani ɓangare na ayyukan jinƙai da take yi lokaci-lokaci domin rage raɗaɗin rayuwa ga al’umma. An gudanar da rabon tallafin ne a wani taro da ya gudanar a makarantar Yombe da ke Kurmin Mashi Kaduna, inda ya samu halartar masu ruwa da tsaki da kuma waɗanda suka amfana, inda aka raba kayayyaki da suka haɗa da shinkafa, wake, gero da kuma kayan sawa na Sallah domin bai wa waɗanda suka…
Read More
Muhimmancin kare sirrin asusun banki a zamani mai cike da ’yan damfara

Muhimmancin kare sirrin asusun banki a zamani mai cike da ’yan damfara

Gargaɗin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi wa ’yan Nijeriya kan kare lambobin sirri, kalmomin shiga da sauran bayanan banki ba kawai saƙon faɗakarwa ba ne na yau da kullum, illa wata muhimmiyar kira ce ga jama’a su ɗauki mataki cikin gaggawa domin kare dukiyoyinsu. A wani lokaci da damfarar kuɗi ke ƙara yawaita tare da ɗaukar sabbin salo na zamani, sakaci da bayanan banki na iya jefa mutum cikin babbar asara cikin ƙanƙanin lokaci. A yau, kusan duk mu’amaloli — daga biyan kuɗin abinci zuwa sayayya da kasuwanci — ana yin su ta hanyar fasahar zamani, wanda hakan…
Read More