ukarofi

12641 Posts
Tinubu ya naɗa Taiwo Oyedele Ministan Kuɗi

Tinubu ya naɗa Taiwo Oyedele Ministan Kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Taiwo Oyedele a matsayin ƙaramin Ministan Kuɗi, inda ya maye gurbin Doris Uzoka-Anite. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar wannan Talatar. Sanarwar ta ce Uzoka-Anite za ta koma Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare ta ƙasa a matsayin ƙaramar Minista, wanda shi ne sauyin muƙami na uku a da aka yi mata a wannan gwamnati. Sanarwar ta ƙara da cewa Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio sunan Oyedele domin tantancewa.…
Read More
Gwamnatina ba za ta lamunci rashawa ba – Ahmed Aliyu

Gwamnatina ba za ta lamunci rashawa ba – Ahmed Aliyu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmed Aliyu ya "gargaɗi" manyan ma'aikatan gwamnatin jihar game da rashawa, tare da bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba. Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na gwamnan jihar Abubakar Bawa ya fitar, ta ce gwamnan ya yi wannan bayani ne sa'ilin taron buɗe-baki da manyan sakatarori da shugabannin ma'aikatu da kuma daraktocin gwamnatin jihar a ranar Litinin. Aliyu ya ce "a matsayinku na shugabanni a ma'aikatunku, wajibi ne ku rungumi ɗabi'ar kaffa-kaffa da adalci a kan duk wata hulɗa." Sanarwar ta kuma ja hankalin…
Read More
Mutane fiye da 300,000 aka raba da muhallansu a jihar Neja

Mutane fiye da 300,000 aka raba da muhallansu a jihar Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin jihar Neja ta ce yawan mutanen jihar da suka tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren 'yan bindiga a sassan jihar ya zarce 300,000. Gwamnatin ta ce wannan matsala ta fi zarce abin da mutane ke zato, domin kuwa ta kai yadda tantance haƙiƙanin adadin mutanen da aka sace da waɗanda aka kashe da kuma waɗanda aka tilastawa yin hijira daga ƙauyukansu ba ƙaramin aiki bane. A wata hira da BBC, kwamishinan yaɗa labaran jihar Neja, Obeh Nuhu Nana ya ce duk da cewa matsalar na da girma sosai, gwamnan jihar Umaru Muhammed Bago na…
Read More
Zazzaɓin Lassa ya hallaka mutane 35 a Taraba

Zazzaɓin Lassa ya hallaka mutane 35 a Taraba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mahukunta a birnin Jalingo na Jihar Taraba sun tabbatar da mutuwar mutane 35 sakamakon kamuwa da cutar zazzaɓin Lassa. Shugaban Sashen Kula da Lafiya na Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Jalingo, Dokta Suleiman Abubakar Kirim, ya bayyana cewa an kwantar da marasa lafiya 226 da ake zargin sun kamu da cutar. Bayan gwaje-gwaje, an tabbatar da cewa mutum 95 daga cikinsu sun kamu da cutar, inda 35 suka rasu, yayin da 20 sun warke har an sallame su. Ya kuma bayyana cewa ma’aikata uku na asibitin sun kamu da cutar da suka haɗa…
Read More
Nijeriya za ta karɓi maganin rigakafin cutar ƙanjamau a watan Maris – NACA

Nijeriya za ta karɓi maganin rigakafin cutar ƙanjamau a watan Maris – NACA

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka mai Karya Garkuwar Jiki (NACA) ta sanar da cewa Nijeriya za ta karɓi maganin rigakafin cutar HIV mai suna Lenacapavir a watan Maris 2026. A cikin wata gajeriyar sanarwa da Shugabar Hulɗa da Jama’a ta hukumar, Toyin Aderibigbe, ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa hukumar ta samu amincewar doka daga hukumar NAFDAC domin shigo da maganin cikin ƙasa. Lenacapavir magani ne da ake yi ta allura sau biyu kacal a shekara, wanda hakan ya sa ya fi sauƙi idan aka kwatanta da magungunan rigakafin da ake sha kullum.…
Read More
Kano: Kotu ta yanke hukuncin kisa kan matasan da suka kashe sabon ango a unguwar Sheka

Kano: Kotu ta yanke hukuncin kisa kan matasan da suka kashe sabon ango a unguwar Sheka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta samu nasarar tabbatar da laifin Amir Zakariyya da Aliyu Hussaini kan tuhume-tuhumen hada baki, fashi da makami da kuma kisan kai a gaban babbar kotun jihar Kano. Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ce ta yanke hukuncin a ranar Talata a Kotu mai lamba 7 da ke Sakatariyar Audu Bako  a Kano. Kotun ta tabbatar da cewa da misalin karfe 2:47 na safiyar ranar 11 ga watan Yuni, 2025, waɗanda aka yankewa hukuncin sun hada baki tare da kutsa kai cikin gidan marigayin, Yazid Haruna, a unguwar Sheka da…
Read More
Kotu ta ɗaure boka watanni 11 a Anambra

Kotu ta ɗaure boka watanni 11 a Anambra

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata Babbar Kotu da ke Awka a Jihar Anambra ta yanke wa wani boka mai suna Chigozie Nwangwu hukuncin ɗaurin watanni 11, bayan samun sa da laifukan da ake tuhumarsa da su. Bokan, wanda aka fi sani da laƙabin “Akwa-Okuko Tiwalu Aku”, ya shahara a kafafen sada zumunta inda yake tallata kansa tare da yi wa mabiyansa ayyukan tsibbu. A watan Fabrairun shekarar da ta gabata ne wata ƙungiyar tsaro ta yankin Agunechemba ta gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Jude Obiora. An gurfanar da bokan tare da wasu mutum biyu; Onyebuchi Okocha…
Read More
Gwamnatin Kano ta bayar da tallafi ga waɗanda gobara ta shafa a garin Zago

Gwamnatin Kano ta bayar da tallafi ga waɗanda gobara ta shafa a garin Zago

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta ƙarƙashin ma’aikatar jin ƙai da rage talauci ta kai tallafi ga al’ummar da gobara ta shafa a garin Zago da ke ƙaramar hukumar Ɗanbatta. Tallafin na kuɗaɗe da aka raba jiya a garin na Zago da ke ƙaramar hukumar Ɗanbatta ya kai jimillar Naira miliyan N6,576,537.33 an raba shi ga iyalai 28 da gobarar ta shafa a watan Fabrairu na shekarar 2025 da ta gabata. Ta cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan al’umma a ma’aikatar jin ƙai da rage talauci Ibrahim Abdullahi ya rabawa manema labarai ta ce, a…
Read More
A shirye mu ke domin cigaba da bibiyar shari’ar Walida – Gwamna Namadi

A shirye mu ke domin cigaba da bibiyar shari’ar Walida – Gwamna Namadi

Daga USMAN KAROFI Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bin shari’ar sace Walida Abdulhadi har zuwa ƙarshen ta, domin tabbatar da adalci da kuma haɗa ta da iyalanta nan ba da jimawa ba. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar ga manema labarai. Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya gana da iyayen Walida tare da lauyansu a fadar gwamnati da ke Dutse. Gwamna Namadi ya shaida musu halin da Walida ke ciki a yanzu, yana mai jaddada…
Read More
Sauye-sauyen tattalin arziki na Tinubu sun fara haifar da ɗa mai ido – Idris

Sauye-sauyen tattalin arziki na Tinubu sun fara haifar da ɗa mai ido – Idris

Daga USMAN KAROFI Ministan yaɗa labarai da wayar da kai na ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun fara nuna sakamako a fili. Idris ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Jumoke Oduwole, wadda ta kai masa ziyarar girmamawa a ma’aikatar sa. Idris ya ce a karon farko cikin shekaru 13, ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na Najeriya ya haura dala biliyan 50. Ya kuma ƙara da cewa an cire Najeriya daga jerin ƙasashen da ke cikin “grey list” na Financial Action Task…
Read More