06
Mar
Daga USMAN KAROFI Matatar man fetur ta Dangote ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da wadatar makamashi a ƙasar, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar tangarɗa a kasuwar mai ta duniya. Kamfanin ya bayyana cewa rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya ya janyo rufe wasu matatun mai tare da rage yawan tace man fetur a sassa daban-daban na duniya, lamarin da ya haddasa ƙarancin man fetur a kasuwannin duniya. Kamfanin ya ƙara da cewa wasu ƙasashe sun fara ɗaukar matakai domin kare kasuwanninsu, inda ƙasar Sin ta…
