ukarofi

12641 Posts
INEC ta yi kira ga jam’iyyu su daidaita rikicin cikin gida da ya dabaibaye su kafin babban zaɓe

INEC ta yi kira ga jam’iyyu su daidaita rikicin cikin gida da ya dabaibaye su kafin babban zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓen Nijeriya, INEC ta yi tsokaci game da matakan shari'a da ɓangarorin cikin gida na jam'iyyun siyasar ƙasar ke ɗauka a tsakaninsu, da kuma rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyun. Shugaban Hukumar Zaɓen, Farfesa Joash Amupitan wanda ya bayyana damuwar ya ce yanayin ba alheri ba ne ga jam'iyyun, kuma hakan na yin barazana ga saita tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya. Farfesa Amupitan ya koka da cewa, maimakon jam'iyyun su zama wani tsanin kawo sauyi a ƙasa, amma sun koma suna hamayyar shugabanci da ringingimu, al'amarin da ya koma kamar wani wasan kwaikwayo.…
Read More
Masu buƙata ta musamman a Kano sun buƙaci a rika naɗa su kan muƙaman da suka shafe su

Masu buƙata ta musamman a Kano sun buƙaci a rika naɗa su kan muƙaman da suka shafe su

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wasu daga cikin shugabannin masu buƙata ta musamman (Persons With Disabilities – PWDs) a Jihar Kano sun buƙaci gwamnatin jihar da ta riƙa naɗa mutane daga cikin su a muƙaman gwamnati da suka shafi harkokin nakasa, domin tabbatar da adalci da wakilci a harkokin shugabanci. Kiran na ƙunshe ne cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da jagorancin ƙungiyar PWDs suka aike wa gwamnatin jihar Kano, inda suka bayyana cewa mutanen da ke rayuwa da nakasa su ne suka fi fahimtar ƙalubalen da ɓangaren ke fuskanta a rayuwa. A cikin wasikar, wacce Ali Miko Muhammad Dangwauro, wanda ke…
Read More
Zanga-zangar kisan Khamenei: Amurka ta soke alƙawuran biza a Nijeriya

Zanga-zangar kisan Khamenei: Amurka ta soke alƙawuran biza a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ofishin Jakadancin Amurka da ke Nijeriya ya soke dukkan alƙawuran neman biza da aka tsara gudanarwa ranar Laraba, 4 ga Maris, 2026, sakamakon yiwuwar ɓarkewar zanga-zanga a Abuja dangane da rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Amurka da Iran. A wata sanarwa da ofishin ya fitar, ya gargaɗi ’yan ƙasar Amurka da ke Babban Birnin Tarayya Abuja da su zauna a gidajensu, yana mai cewa akwai “babbar yiwuwar zanga-zanga” a birnin saboda rikicin da ke gudana da Iran. Sanarwar ta fito ne bayan hare-haren sama na hazin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran,…
Read More
Rikicin Iran: Nijeriya ta dakatar da jigilar Kiristoci masu zuwa ibada Isra’ila

Rikicin Iran: Nijeriya ta dakatar da jigilar Kiristoci masu zuwa ibada Isra’ila

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta dakatar da dukkanin wata zirga-zirgar Kiristoci masu zuwa ibada zuwa Isra’ila sakamakon rikicin da ya ɓarke a yankin Gabas ta Tsakiya. Hukumar Aikin Hajjin Kiristoci (NCPC) ce, ta sanar da wannan mataki a ranar Talata. Babban Sakataren Hukumar, Bishop Stephen Adegbite, ya bayyana hakan a wata sanarwa da sashen yaɗa labarai na hukumar ya fitar a Abuja. Ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin kare ’yan Nijeriya daga faɗa wa hatsari. A cewarsa, abubuwan da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da ayyana dokar ta-ɓaci a…
Read More
Kawo ƙarshen mace-macen mata masu juna biyu a Nijeriya

Kawo ƙarshen mace-macen mata masu juna biyu a Nijeriya

Matsalar mace-macen mata da yara a lokacin ciki ko haihuwa dai ta jima ta na ci wa ƙasashe masu tasowa tuwo a ƙwarya. Alal misali, ƙasashen da suka ci gaba mata 7 zuwa 15 ne ke mutuwa a cikin mata masu juna 100,000 daga lalurar ciki ko haihuwa; amma a ƙasashe masu tasowa har wajen mata 500 ne kan rasu sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwa. Wani sabon rahoton da hukumomin Majalisar ɗinkin Duniya suka fitar na cewa a duk minti biyu mace na mutuwa a duniya yayin da take ɗauke da juna biyu ko haihuwa. Hakan na ƙara nuna rashin…
Read More
Majalisar Dokokin Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin Gwamna

Majalisar Dokokin Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin Gwamna

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, kwamared Aminu Abdulsalam, bisa zarge-zargen aikata manyan laifuka a kan aiki, wulaƙanta aiki da kuma karya dokokin aikin gwamnati. Matakin ya biyo bayan wani ƙorafi da ɓangaren zartarwa ya gabatar wa majalisar, inda aka buƙaci ta ɗauki mataki a kan Abdulsalam kan wasu zarge-zargen da suka shafi yadda ya gudanar da aikinsa a lokacin da yake kwamishinan ƙananan hukumomi tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024. Da yake karanta ƙorafin, Shugaban nasu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya ce sanarwar ta yi daidai da tanadin…
Read More
Dikko Raɗɗa ya yaba da haɗin kan Katsinawa a ƙarƙashin jam’iyar APC

Dikko Raɗɗa ya yaba da haɗin kan Katsinawa a ƙarƙashin jam’iyar APC

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Katsina ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake gabatar da jawabi bayan kammala babban taron jam'iyar inda aka zaɓi sabbin shugabannin a matakin jihar ta hanyar sasanci. Ya kuma taya shugabannin jam'iyar murna ƙarƙashin jagorancin Dr Bishir Gambo Saulawa. Raɗɗa ya bayyana nasarar da aka samu ta hanyar maslaha da yarjejeniya shaida ce ta irin kyakkyawan dimokuraɗiyyar cikin gida ta APC a jihar Katsina. Ya jawo hankalin sabbin shugabannin jam'iyar cewa wannan nauyi ba muƙami ba ne kawai ko girmamawa; kira ne na sadaukar da kai domin ƙarin ɗaukar nauyi da hidima…
Read More
An jinjinawa ga gwamnan Katsina kan yadda ya gudanar da zaɓen shugabannin APC

An jinjinawa ga gwamnan Katsina kan yadda ya gudanar da zaɓen shugabannin APC

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai bai wa Gwamnan Katsina shawara kan harkokin jam'iyyu, Alhaji Shafi'u Duwan yayi wannan jinjinar ga gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa kan yadda ya gudanar da zaɓuɓɓukan sabbin shugabannin jam'iyyar APC na jihar Katsina tun daga matakin unguwanni har zuwa na jiha. Duwan ya ce zaɓen an yi shi cikin natsuwa, ilmi da hangen nesa wanda hakan ya ƙara saka jihar Katsina a tarihi a matsayin gagara gasa, kuma abin misali da koyi. "Duk waɗannan nasarorin sun samu ne a bisa kyakkyawan jagorancin mai girma Gwamnan Katsina, mai hangen nesa da adalci,"Inji Duwan. Alhaji Shafi'u…
Read More
Ƙungiya ta yabi Tinubu kan shirin wayar da kai kan sauyin yanayi

Ƙungiya ta yabi Tinubu kan shirin wayar da kai kan sauyin yanayi

Daga ABUBAKAR A BOLARI, Gombe Wata ƙungiya mai zaman kanta da ke Gombe, Jewel Environmental Initiative (JEI), ta yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙaddamar da shirin yawon wayar da kai kan sauyin yanayi na Renewed Hope Climate Change Awareness Tour (REHCCAT), tana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin mataki na tinkarar barazanar sauyin yanayi da ke ƙara tsananta a Najeriya. Ƙungiyar ta ce shirin zai taimaka wajen ƙara wayar da kan jama’a, ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire tare da inganta hanyoyin kare muhalli, musamman a cikin al’ummomin da sauyin yanayi ya fi shafa. A cikin wata sanarwa da babban daraktan ƙungiyar,…
Read More
Ya kashe ɗan uwansa saboda ya yi mafarkin ya harbe shi

Ya kashe ɗan uwansa saboda ya yi mafarkin ya harbe shi

Daga USMAN KAROFI Wani mutum mai shekaru 43 ya shiga hannun ‘yan sanda bayan zargin kashe babban ɗan’uwansa, Mustapha Amidu, a Jihar Oyo. Ana zargin mutumin ya aikata laifin ne bayan ya ce marigayin ya “harbe shi” a mafarki. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ayanlade Olayinka, ya fitar a birnin Ibadan. Olayinka ya bayyana cewa an kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Ago-Amodu ta hannun Badmus Yunisa, mazaunin unguwar Alegunlode a yankin Sepeteri. A cewarsa, wanda ake zargin ya je inda marigayin yake zaune, ya…
Read More