01
Mar
Daga DAUDA USMAN An shawarci al’ummar Musulmi a Nijeriya da ma sauran sassan duniya da su ƙara himma wajen aiwatar da ayyukan alheri a cikin wannan watan azumin Ramadan mai tsarki. Wannan kira ya fito ne daga wani fitaccen ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Mustapha Mairoba, wanda aka sani a matsayin jigo a kasuwar ƙofar Wambai da ke cikin birnin Kano, kuma na hannun daman marigayi Sheikh Malam Ibrahim Shehu Dahiru Usman Bauchi a Kano. Haka kuma shi ne shugaban ƙungiyar Dattawan Kasuwar ƙofar Wambai da kewayenta. Ya bayar da wannan shawara ne yayin wani taron walimar buɗa baki da…
