28
Feb
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar EFCC ta sanar da kama mutum 20 da ake zargi da aikata laifukan zaɓe yayin zaɓen ƙananan hukumomin babban birnin tarayya, Abuja da aka gudanar a ranar 21 ga Fabrairu, 2026. Ta ce an kama su ne a wurare daban daban saboda zarge zargen sayen ƙuri’u da sayar da ƙuri’u da kuma hana jami’ai aiki, inda aka gano kuɗi har Naira miliyan 17,218,700. A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya fitar, an ce an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin da Naira miliyan 13,500,000 a cikin mota…
